'Gwamnatin Donald Trump ta bankaura ce'

Donald Trump

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sir Kim Darroch yana ganin da wuya gwamnatin Trump, ta saito, ta daina shirme da bankaura

Jakadan Birtaniya a Amurka ya caccaki gwamnatin Shugaba Trump inda ya bayyana ta da cewa, ta bankaura ce, mai rauni kuma wadda ba ta dace ba.

A wata wasika ta sirri wadda ta bayyana Jakada Sir Kim Darroch, ya ce fadar gwamnatin kasar karkashin Trump ta sukurkuce tare da rarrabuwa.

Sai dai kuma duk da wannan suka Mista Darroch ya yi gargadin da kada a yi watsi da shugaban na Amurka, duk da yadda yake.

Ma'aikatar harkokin waje ta Birtaniya ta ce satar bayyana takardar da ke dauke da wadannan maganganu da aka yi ga jaridar Mail ranar Lahadi, an yi hakan ne da mummunar niyya, amma kuma ba ta musanta kalaman ba.

Sir Kim Darroch

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Jakadan ya ce kan gwamnatin Trump a rarrabe yake

A cikin takardar Sir Kim ya ce: ''Ba ma ganin wannan gwamnatin za ta daidaita; sukurkutacciya ce; ba ta da kan kado; ba ta yin abu cikin tsari.''

Jakadan yana ganin ba lalle ba ne gwamnatin ta Trump ta taba zama wadda ta dace.

Duk da cewa Sir Kim ya ce Trump ya ji matukar dadi da mamaki a ziyarar da ya kai Birtaniya a watan Yuni, amma ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da kasancewa mai nuna bambanci da fifita Amurka a komai.

Sabanin da ke tsakanin Amurka da Birtaniya a kan batun sauyin yanayi da 'yancin 'yan jarida da hukuncin kisa zai iya kara ffitowa fili, yayin da kasashen ke neman kyautata dangantakarsu bayan ficewar Birtaniya daga kungiyar kasashen Turai, kamar yadda takardar ta sirrri ta bayyana.

A bayanan na sirri jakadan ya ce, idan kana son shawo kan shugaban ya fahimce ka, sai ka yi bayaninka cikin sauki, ko ma ya zama ka yi shi kai tsaye kawai ko keke da keke.

A wani sako da Sir Kim ya aika a watan da ya wuce, ya bayyana manufar Amurka a kan Iran, a matsayin wadda babu tsari kuma mai rudani.