Nasir el-Rufai ya yi wa sanatocin Kaduna tofin Allah-tsine
A wasu kalamai da wasu ke wa kallon na ingiza jama'a ne su dauki doka a hannunsu, gwamnan jihar Kaduna a arewacin Najeriya, ya nemi jama'a da su farwa sanatocin da suka fito daga jihar.
Nasir Ahmad el-Rufai ya ce "wadannan dattijan [sanatocin Kaduna] banza ne... domin su makiyan jihar Kaduna ne, ba sa son ci gaban jihar."
Sannan ya yi kira ga magoya bayansa da su askewa sanatocin gashin kansu da gemunsu domin a cewarsa "ba sa kaunar jihar."
Gwamnan ya zargi Sanatocin da suka hada Shehu Sani, Suleiman Hunkuyi da Danjuma Laah, da hada baki domin hana majalisar dattawan Najeriya amincewa da bukatarsa ta cin bashi daga Bankin Duniya.
Kawo yanzu sanatocin ba su ce uffan ba game da kalaman gwamnan.
Gwamnan ya yi amfani da wasu kalmomi da suka saba wa ka'idojin aikin BBC, dalilin da ya sa ba a wallafa ba.
Jama'a da dama na ci gaba da yada kalaman gwamnan, wadanda ya yi a wurin taron gangamin siyasa, a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama ke Allah-wadai da shi.
Gwamna Nasir el-Rufai na magana ne a wurin bikin bayar da tutar takara ga wadanda za su tsaya wa jam'iyyar APC takara a zabukan kananan hukumomin jihar.
Ya ce "wadannan... in suka shigo Kaduna, ku yi musu aski, daya ku aske masa gashin kansa, daya ku aske masa gemu"
A ranar Asabar 12 ga watan Mayu ne za a yi zabukan.
Jihar Kaduna na fama da tashe-tashen hankula musamman na barayi a yankin Birnin Gwari da kuma na makiyaya da manoma a kudancin jihar.
Hakazalika jihar Kaduna ta dade tana fama da rikicin siyasa tsakanin bangaren gwamnan da Sanata Shehu Sani da Suleiman Hunkuyi a daya bangaren na jam'iyyarsu ta APC.
Rikicin siyasar tsakanin bangarorin biyu ya kai ga rasa rayuka da jikkata mutane da dama.

Asalin hoton, Kaduna Government/Facebook

Asalin hoton, Kaduna Government/Facebook












