MDD ta soki manufar Amurka

Asalin hoton, EPA
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta damu matuka, kan yadda bisa sabbin dokokin Amurka na shige da fice za a hana mutanen da suka fito daga nahiyar Amurka ta tsakiya damar neman mafaka a Amurkar, idan har sun fara ratsawa ta wata kasa kafin isarsu Amurkar.
A wata sanarwa da ta fitar a hedikwatarta da ke Geneva, hukumar ta ce da dama daga wadanda ke isa Amurka ta iyakarta ta kudu, suna tsere wa tashin hankali ne da gallazawa, saboda haka mutanen na cikin bukatar kariya ta duniya.
Hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta ce sabuwar manufar ta Amurka tana da tsanani, kuma za ta jefa iyalai masu rauni cikin hadari.
Matakin hana mafaka ga wadanda suka isa Amurka ta iyakarta ta kudu, muddin dai sun fara ratsawa ta wata kasar kafin su shiga Amurkar, majaliar dinkin duniyar ta yi amanna, hakan abu ne da ya saba wa dokokin duniya, wadanda Amurka da dadewa ta rattaba hannu a kansu.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar 'yan gudun hijirar ta duniya ta ce da yawa daga cikin wadanda ke isa Amurka, suna tsere wa cin zali ne da gallazawa, kuma ba wata kasa da za ta ba su mafaka a kan hanyarsu ta neman tsira.
Hukumar ta ce ta lura cewa tsarin bayar da mafaka na Amurka a takure yake, kuma ta ce a shirye take ta taimaka wajen magance hakan, amma kuma ta kara da cewa tsarin ya takaita 'yanci da walwala na masu cin gajiyar shirin, wanda kuma hakan ba shi da alfanu wajen ci gaba.

Asalin hoton, Getty Images
Ana sa ran sabuwar dokar ta Amurka za ta fara aiki a take, wadda kuma tana daya daga cikin dokokin da hukumar 'yan gudun hijira ta duniya ke fargaba a kai, amma kuma daman tana tsammaninta.
Kalaman Shugaba Trump sun nuna karara cewa gwamnatin Amurka ba ta da niyyar karbar 'yan gudun hijira da 'yan ci-rani.










