'An kashe 'yan Nigeria' da dama a Libya

Jama'a sun taru a wurin da aka kai harin cikin dimuwa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Jama'a sun taru a wurin da aka kai harin cikin dimuwa

Hukumomi sun ce an kashe akalla mutum 40 a wani hari da aka kai ta sama wanda ya fada kan wata cibiyar tsare 'yan ci-rani a kasar Libya.

Rahotanni sun ce karin wasu 80 sun ji raunuka a harin bam din wanda ya tarwatse, a wata cibiya da ke wata unguwa a gabashin birnin Tripoli.

Bayanai sun ce mafi yawan wadanda aka kashe 'yan ci-ranin Afirka da ke hank'oron tsallakawa zuwa Turai, kuma akwai 'yan Najeriya da dama a cikinsu, wadanda ke cike da mafarkin rayuwa mayalwaciya.

Kawo yanzu hukumomin Najeriya ba su ce komai game da batun ba, amma a baya sun sha kwashe 'yan kasar da rikici ya rutsa da su a Libya.

Tarzoma da rarrabuwar kai sun daidaita Libya tun bayan hambaraswa da kashe Shugaba Muammar Gaddafi mai dogon zamani a 2011.

Osama Ali, mai magana ne da yawun hukumomin ba da agaji ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa wani hari ne daga Tajoura kai tsaye ya fada wa wata rumfa da ake tsare 'yan ci-rani 120.

Ya ce mai yiwuwa ne mamatan su fi 40 domin kuwa kididdigar mutanen da aka kashe din ta farko-farko ce.

Jami'an agaji sun isa wurin da lamarin ya faru a yankin Tajoura na birnin Tripoli

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Jami'an agaji sun isa wurin da lamarin ya faru a yankin Tajoura na birnin Tripoli

Cibiyoyin tsare 'yan ci-ranin dai sun shiga tsaka mai wuya.

Gwamnatin National Accord mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya wadda Fira minista Fayez ai Serra ke jagoranta ta zargi dakarun Libyan National Army da kai wannan hari na wayewar garin ranar Laraba.

Mayakan karkashin jagorancin Khalifa Haftar na fada ne da dakarun gwamnatin da kasashen duniya ke marawa baya a yankin da harin ya auku.

A ranar Litinin ne ta sanar da cewa za ta fara kai hare-hare ta sama cikin birnin Tripoli bayan hanyoyin da aka saba da su sun faskara.

Sai dai mai magana da yawun mayakan ya musanta cewa dakarunsu ne suka far wa cibiyar tsare mutanen.