Barca za ta ba Arsenal Malcom, United na dab da sayen Fernandes

Bruno Fernandes

Asalin hoton, Getty Images

Barcelona ta nemi Arsenal ta sayi dan wasan Brazil Malcom, amma ta fi mayar da hankalinta ga dan kwallon Ivory Coast Wilfred Zaha daga Crystal Palace, in ji Mirror.

Gunners na da fam miliyan 70 domin taya Zaha a karo na biyu amma Palace na son a biyata miliyan 80, a cewar Sky Sports.

Wakilin Romelu Lukaku ya gana da Inter Milan a lokacin da Inter ke cigaba da tattaunawa da Manchester United kan farashin dan kwallon na Belgium mai shekara 26, in ji Sky Sport Italia.

Manchester United na son daukar dan wasan tsakiya na Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 24 daga Sporting Lisbon, a cewar Sky Sports. Wasu rahotannin sun ce ana dab da kammala cinikin.

Leicester City na dab da kashe kudin da ba ta taba kashe irinsu ba wurin sayen dan kwallo a yunkurinta na sayen dan wasan Belgium Youri Tielemans, mai shekara 22, daga Monaco kan fam miliyan 40, kuma suna son sayen Ayoze Perez, daga Newcastle kan fam miliyan 30, in ji Telegraph.

Real Madrid a shirye take ta bayar da Gareth Bale mai shekara 29 domin karbo Paul Pogba daga Manchester United mai shekara 26, in ji jaridar Mail.

Gareth Bale da Pogba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An dade ana hasashe kan makomar Bale da Pogba a Real Madrid da Manchester United

Sai Manchester United ta biya fam miliyan 90 idan har tana son sayen Harry Maguire mai shekara 26 daga Leicester City - inda dan wasan na Ingila zai kasance dan wasan baya mafi tsada a tarihi, a cewar Telegraph.

Manchester United ta nuna sha'awar dan wasan Spain Dani Olmo da ke taka leda a Dinamo Zagreb mai shekara 21, in ji Daily Mail.

Crystal Palace ba ta son sayar wa Arsenal dan wasan Ivory Coast Wilfried Zaha, mai shekara 26, in ji Daily Mirror.

Akwai yiyuwar Alexandre Lacazette, mai shekara 28 zai bar Arsenal kafin rufe kasuwar musayar 'yan wasa, a cewar Express.

Atletico Madrid na son dauko Lacazette domin maye gurbin Antoine Griezmann, mai shekara 28 idan ya koma Barcelona, in ji Daily Mirror.

Barcelona na jiran tayin dan wasanta na baya Samuel Umtiti, mai shekara 25, wanda Manchester United ke son saya, in ji Sport, via Mirror.

Dan wasan Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 22, yana son ci gaba da taka leda a Barcelona duk da manyan kungiyoyi sun nuna suna sha'awarsa kamar Liverpool da Bayern Munich, a cewar jaridar L'Equipe.

Aston Villa tana son sayo dan wasan Kasimpasa dan kasar Masar Mahmoud Trezeguet, mai shekara 24, in ji jaridar Sun.