Ruga: Gwamnonin kudu ba su yarda da matsayar Buhari ba

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
Tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da shirinta na tsugunar da makiyaya ta hanyar gina masu "ruga," 'yan kasar na ciki da wajenta suka fara bayyana mabambantan ra'ayoyi.
Gwamnatin jihohi ma ba a bar su a baya ba, inda tuni gwamnonin yankin kudu maso gabashin Najeriya suka kekashe kasa cewa ba za su shiga wannan shiri ba.
Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi shi ne shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya, kuma mai magana da yawunsa Emmanuel Uzor ya shaida wa BBC cewa su kam ba da su ba a wannan shiri.
"Sun riga sun yanke hukunci cewa babu wani yanki na kudu maso gabas da za a bayar domin yin rugar Fulani, tunda abu ne na kashin-kai duk wanda yake ganin zai yi sai ya yi, amma ba sai Fulani sun zo nan ba."
Ba gwamnonin kudu ne kawai ke da irin wannan ra'ayi ba, jihar Benue ma ta ce ba za ta bayar da wani yanki na jihar ba domin gina Rugar.
A ranar 25 ga watan Yuni Gwamnan jihar Samuel Ortom ya ce gina Ruga a Benue "tamkar cin fuska ne ga al'ummar jihar saboda haka ba ma goyon bayan al'amarin."
Gwamna Ortom ya yi wannan bayani ne jim kadan bayan karbar ma'aikatan gwamnatin tarayya daga ma'aikatar Aikin Gona inda suka je da motocin tantan domin share filayen da za a gina Rugar.

'Ba kyamar Fulani muke yi ba'

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban kungiyar manoma ta All Farmers Asscociation of Nigeria (AFAN) reshen jihar Abia Cif Dunlop Okoro ya shaida wa BBC cewa "wannan shirin ba zai yi aiki a Najeriya ba.
Ya kara da cewa shirin ka iya zama mai kyau a wani wurin amma ba abu ne mai yiwuwa ba "musamman a Najeriya inda muke saurin zargin juna".
"Yanzu mutane suna dari-dari da makiyaya sakamakon yawan samun rikici tsakaninsu da manoma. Saboda haka duk lokacin da ka yi maganar ruga babu wanda zai karbe ta.
"Ba ma kyamarsu domin kuwa 'yan Arewa da suke zaune a kudu a yanzu sun fi wadanda suke zaune yawa kafin yakin basasar Biyafara. Haka su ma al'ummar Igbo da ke zaune a Arewa sun fi yawa a yanzu."

'Mun fi jin dadin yawo'

Asalin hoton, Getty Images
Wasu daga cikin wadanda abin ya shafa wato al'ummar Fulani sun ce su fa sun fi son a bar su su ci gaba da yawo da shanunsu maimakon tsugunar da su da gwamnati ke shirin yi.
Ardo Sa'idu Baso shi ne sarkin Fulanin kudu maso gabas a Najeriya, ya ce ai in so samu ne a ce wata uku ko hudu shanunka su canza wurin zama.
Ya ce: "Mu a bar mu haka muna yawace-yawace da shanunmu ya fi mana a kan a tsugunar da mu a wuri daya. Inda shanu suka yi bazara ba nan suke shekara ba.
"Ya kamata a ce wata uku ko hudu shanu su canza wurin zama, mu mun fi jin dadin hakan."

'Shirin ba na Fulani ba ne kadai'

Asalin hoton, Getty Images
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya fitar, gwamnatin ta ce "ba wai Fulani makiyaya ne kawai za su ci gajiyar Rugar ba, duk wani mai sana'ar dabbobi zai amfana."
"Ruga na nufin wani wuri da za a tsugunar da makiyaya da masu kiwon dabbobi," in ji Garba Shehu.
Rugar za ta kasance tana da makarantu da asibitoci da tituna da kasuwanni da dai sauran abubuwan da za su taimaka wajen inganta rayuwar dabbobinsu.
Sanarwar ta kara da cewa "gwamnati ba ta da niyyar kwace wa mutane filayensu ko kuma ta tursasa su yin abin da ba sa so".

#SayNoToRuga da #SayNoToRugaSettlement
Tun a makon da ya gabata ne mutane da dama suka yi ta amfani da maudu'in #SayNoToRuga da #SayNoToRugaSettlement a dandalin Twitter domin yin Allah-wadai da shirin.
Wasu jiga-jigai a jam'iyyar adawa ta PDP irinsu Reno Omokri da Femi Fani Kayode, na cikin 'yan gaba-gaba wajen yin kiraye-kirayen yin watsi da shirin.
Wannan cewa yake, shugaban kasa ka dauki rugarka ka kafa ta a dajin Sambisa:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Shi kuma wannan cewa yake ai ruga ba ta cikin kundin tsarin mulkin kasa:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2











