Ko yaki zai iya barkewa tsakanin Amurka da Iran?

Lokacin da masu zanga-zanga a Iran suka kone tutar Amurka a watan Mayun 2019

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Rikicin tsakanin kasashen biyu ya dade yana ruruwa
    • Marubuci, Jonathan Marcus
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan tsaro da diflomasiyya

Wakilin BBC kan tsaro da diflomasiyya a kasashen duniya, Jonathan Marcus ya yi duba dangane da yiwuwar ko kuma akasin Amurka da Iran yin gaba da gaba a fagen yaki, al'amarin da duniya ta zura wa ido tana jiran afkuwarsa. Usman Minjibir ya fassara bahasin da wakilin na BBC ya yi kan wannan kiki-kaka kamar haka:

Iran ta harbo jirgi maras matuki na sojin ruwan Amurka wanda yake leke asiri. Shugaba Donald Trump ya ce ya bayar da umarnin kai hare-haren ramuwar gayya amma ya sauya aniyayarsa minti 10 kafin fara kai hare-haren. Yadda abubuwan suka faru na nuna akwai yiwuwar kasashen biyu ka iya fada wa rikici.

Bari mu yi tsammanin cewa Shugaba Trump bai fasa kai hare-haren ramuwar gayya ba. Da mene ne zai faru? Watakila hare-haren da Amurkar za ta kai irin wanda Iran din ta kai ne na kakkabo jirgi maras matuki ko kuma a hari wurin da ake gina makaman nukiliya. Da hakan zai zama tamkar gargadi ga kasar ta Iran.

Rahotanni sun ce Mista Trump ya aike wa da Iran din wani sako da daren Alhamis ta hannun kasar Oman, inda ya nemi su zauna a teburin sasantawa.

Mene ne zai faru idan da Amurka ta kai hari Iran?

Abu na gaba shi ne yadda kasar Iran za ta mayar da martani.

Wani rahoto ya nuna cewa Iran din ta bayyana cewa ba ta da niyyar tattaunawa da Amurkar.

Ta kuma gargadi Amurkar cewa "Kai wa Iran hari zai yi tasiri a kan gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya", In ji wani jami'n gwamnatin Iran da ya tattauna da kamfanin dillancin labarai na Reauters.

Iran

Asalin hoton, IRIBNEWS

Bayanan hoto, Tarkacen jirgi marar matukin da Iran ta baro ke nan kamar yadda gidan talbijin na kasar ya nuna

Ya ya yaki zai kasance tsakanin Amurka da Iran?

Akwai abubuwan dubawa da yawa kuma hakan ne zai sa a ce yaki tsakanin kasashen biyu ba mai yiwuwa ba ne.

Duk da kasancewar gwamnatin Shugaba Donald Trump ba ta kaunar gwamnatin Iran karkashin Hassan Rouhani ba, amma Amurkar ba za ta iya kutsawa cikin Iran ba domin ta kifar da gwamnati mai ci ba. Iran ba Iraqi ba ce. Kasar Iran tana da sarkakiya fiye da Iraqi ta fuskar karfin soji da siyasa. Hakan na bakanta wa wasu jami'an gwamnatin Amurka a fadar WHite House wadanda ke son ganin an tumbuke gwamnati mai ci. Da alama za su kunyata. Saboda haka shiga Iran a yake ta ta kasa ba abu ne mai yiwuwa ba.

To sai dai idan fa har Iran ta sake kai wani harin bayan kakkabo jirgin Amurkar maras matuki, to fa za ta iya gamuwa da fushin Amurkawa. Za a iya kai wa sansanin sojojinta na ruwa hari da na sama ta hanyar amfani da makamai masu linzami. Babban abin da Amurkar za ta hara shi ne dakarun juyin juya halin Iran wadanda sashensu mai aiki a ruwa ya taka babbar rawa wajen kakkabo jirgin Amurka marasa matuki.

Babu ko tantama Amurka za ta iya kai hare-hare kan makaman sojin Iran. To sai dai Iran din ita ma na da hanyoyin kai hare-haren ramuwar gayya kamar amfani da nakiyoyi da kai wa kananan jiragen ruwa hare-hare da kuma amfani da jiragen yaki na karkashin ruwa wajen hana hada-hada a gabar ruwa na yankin Larabawa. Kana za ta iya kai wa jiragen ruwa masu dauke da danyen mai hare-hare, al'amarin da zai iya tilasta Amurka daukar matakan kariyar kai.

Tsakanin Amurka da Iran, wa ya fi karfi?

Amurka ta sha gaban Iran ta fuskar leken asiri da kuma sanin yanayin da kasa ke ciki. To sai dai kakkabo jirgi maras matuki na Amurkar mai tsadar gaske da Iran ta yi, ya nuna Amurkar na da gibi a harkar leken asirin. Bugu da kari, Iran za ta iya rugurguza jiragen ruwa na yaki masu tsada mallakar Amurka wanda hakan ka iya sa mista Trump sauya tinaninsa kan yakar Iran din.

Idan kuma har kasashen biyu suka fada yakin, to Amurka za ta so ta ga ta karya lagon sojojin Iran, ta hanyar fara lalata tsarin tsaron Iran na sama da dai sauransu.

To sai dai idan Iran ta ji matsa za ta iya neman fadada yakin zuwa sauran wurare, inda za ta iya umartar magoya bayanta da ke Iraq da Syria da ma sauran wurare da su kai wa Amurka hari.

Idan gumu ta yi gumu ma, Iran din za ta iya amfani da kungiyar Hezbollah bisa hadin gwiwar sojojin Iran din da ke Syria wajen kai hare-haren roka kan Isra'ila. Iran kuwa za ta yi hakan ne domin ta nuna wa Mista Trump irin hadarin da yankin Larabawa zai fada ciki idan ya ci gaba da kai mata hari.

Amurka za ta so ta koya wa Iran hankali ta hanyar illata karfin sojinta musamman ma dakarun juyin juya hali. Ita kuma Iran abin da take son yi shi ne tana son janyo Mista Trump ya yi yaki da ita wanda hakan zai janyo wa Amurka kashe makudan kudade, al'amarin da daga bisani ka iya shafar kokarin sake neman zabe karo na biyu da Donald Trump yake yi

Iran dai na ganin idan jam'iyyar Democrat ta su Hillary Clinton ta ci zabe, watakila Amurka ta koma kan yarjejeniyar takaita gina nukiliya da aka kulla a 2015 tsakanin Amurkar da Iran da sauran kasashen duniya masu fada a ji.

A 2018 ne dai Donald Trump ya sanar da ficewa daga yarjejeniyar da aka kulla a lokacin mulkin shugaba Barrack Obama.

Rouhani ke nan yake jawabi a wani taro

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Gwamnatin Iran karkashin Hassan Rouhani na fama da kangin tattalin arziki

Yakar Iran ba zai magance komai ba. Ba zai warware batun samar da makamin nukiliyar kasar ba. Haka kuma ba zai janyo tawaya ga irin karfin fada a jin da Iran take da shi a yankin Larabawa ba, wani abu da Amurkar take matukar kaunar gani ya faru.

Kasar Iran ta sanar da cewa, nan ba da jimawa ba za ta ci gaba da makamin nukiliya fiye da abin da dokokin kasa da kasa suka iyakance mata.

Yanzu haka Amurka ta nemi Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zauna ranar Litinin domin tattaunawa kan Iran.