Bayanai kan rikicin nukiliyar Iran cikin kalmomi 300

File photo of Bushehr nuclear power plant in southern Iran (26 October 2010)

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Iran ta dage akan cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne

Da alama yarjejeniyar da kasashen duniya suka cimma da Iran kan shirinta na nukiliya na gab da tarwatsewa. Ga wasu bayanai kan takaddamar da zarge-zarge.

Menene alfanun wannan yarjejeniya?

Zarge-zargen da ake cewa Iran na fakewa da shirinta na nukiliya wajen bunkasa makamin nukiliya ya tilastawa Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai kakaba mata takunkumai masu tsauri da niyyar karya lagonta na samun nasara a shirin na ta.

Iran ta dage a kan cewa shirinta na zaman lafiya ne, sai dai a 2015 ta cimma yarjejeniya da kasashe shida - wato Amurka da Birtaniya da China da Rasha da Jamus.

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce ba zai janye daga yarjejeniyar nukiliyar kasar ba

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce ba zai janye daga yarjejeniyar nukiliyar kasar ba

Kasar ta amince ta takaita harkokinta na uranium, wanda ake amfani da shi wajen samar da makaman nukiliya; da sake kerata, wanda ake kuma iya mayar da shi makami; kuma kwararu a duniya ke sa ido a kai.

A madadin haka aka dage takunkuman da aka kakaba ma ta, wanda haka ya bai wa kasar damar dawowa da harkokinta da fitar da man fetur - wanda shi ne babban hanyar da ke samarwa kasar kudin shiga.

line

Menene ke ingiza sabon rikici?

Gwamnatin Donald Trump ta fice daga yarjejeniya a watan Mayun 2018 da kuma mayar da takunkumai a kan kasar. A watan Nuwamba, takunkuman suka soma aiki kan fannin fitar da man Iran da kudade.

Iran ta shiga barazana na tattalin arziki da hauhawan farashi.

Iran ta mayar da martani ta hanyar janyewa daga wani bangare na yarjejeniyar.

Anti-US mural in Tehran

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Rashin jituwa tsakanin Iran da Amurka ya karu a zamanin Trump

Kasar ta kuma dakatar da harkokin cinikin ketare da man fetur.

Ta kuma bai wa kasashe biyar da suka ci gaba da mutunta yarjejeniyar kwanaki 60 su kare harkokinta na cinikin fetur daga barazanar takunkumin Amurka.

Akasin haka zai tilas ma ta ci gaba da harkokinta na uranium da karfafa cibiyoyin nukiliya.

line

Me Amurka ke so?

Mista Trump ya ce yana son ya sake yi wa yarjejeniyar kwaskwarima da fadada ta ta yadda za ta dakile shirinta na makamin mai linzami da kuma rawar da take takawa a rikicin gabas ta tsakiya

Iran ta jajirce cewa ba za ta yarda a sake yarjejeniyar ba.

Wasu karin labarai kan Iran