Iran ta yi barazanar komawa shirinta na nukiliya

Cibiyar nukiliyar Iran

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Iran tana cewa shirinta ba na kera makamai ba ne, yayin da Amurka da wasu kasashen Yamma ke musanta hakan

Ministan harkokin kasashen wajen Iran, Mohammad Javad Zarif, ya ce kasarsa a shirye take ta sake komawa harkar nukiliya gadan-gadan idan Shugaba Trump na Amurka ya soke yarjejeniyar nukiliyar kasar da aka cimma a shekara ta 2015.

A karkashin yarjejeniyar, Iran ta amince ta sassauta shirinta da nukiliya domin samun sassaucin takunkuman karayar tattalin arziki.

Sai dai shugaba Trump na ganin cewa akwai rashin adalci a yarjejeniyar, inda ya bayar da wa'adin zuwa ranar 12 ga watan Mayu don sake bitar yarjejeniyar.

Mista Zarif ya ce Washington na gindaya hujjojinta ne kan abin da ya shafe ta ko ribar da za ta samu.

Iran ta jaddada cewa shirinta na nukiliya ba na yaki ba ne.