Saudiya za ta kera makamin nukiliya saboda Iran

Asalin hoton, Getty Images
Saudiyya ta yi gargadin cewa ita ma za ta kera makamin nukiliya idan har abokiyar hamayyarta Iran ta mallaki makamin.
Yarima mai jiran gado Mohammad bin Salman ya shaidawa kafar yada labarai ta CBS cewa kasarsa ba ta son mallakar makaman nukiliya.
"Amma babu tantama, idan har Iran ta mallaki makamin nukiliya, za mu kera namu ba da dade wa ba," a cewarsa.
Sannan a cikin tattaunawar da aka yi da shi, Yariman ya kira Ayatollah Ali Khamenei a matsayin Hitler.
Saudiya da Iran sun dade suna hamayya da juna a yankin gabas ta tsakiya.
Kuma sabanin kasashen biyu ya samo asali ne daga banbancin akidar addinin Musulunci.
Saudiya na bin tafarkin akidar Sunni, yayin da kuma Iran ke bin akidar Shi'a.
Haka kuma bangarorin biyu sun dade suna hannun riga da juna a yake-yaken da ake yi a gabas ta tsakiya musamman rikicin Syria da Yemen.
Barazanar Saudiyar a yanzu na nuna fargabar yiyuwar shiga yakin makaman nukiliya a yankin na gabas ta tsakiya.

Asalin hoton, Getty Images
Iran dai ta yi alkawalin takaita ayyukanta na mallakar makamin nukiliya karkashin yarjejeniyar 2015 da ta amince tsakaninta da manyan kasashen duniya zamanin mulkin Shugaban Amurka Barack Obama.
Sai dai kuma shugaba mai ci Donald Trump ya yi barazanar janye wa daga yarjejeniyar.
Tun a 2015 da aka kulla yarjejeniyar, Saudiya ta kalubalanci matakin.
Saudiya ta fito ta yi gargadin cewa, bawa Iran damar ci gaba da shirinta na nukiliya, dama ce ga wasu kasashe a yankin su fara kera nasu makaman na kare dangi.











