Za mu shafe Iran daga duniya idan yaki za mu yi - Trump

Ya ce idan suka shiga yaki Amurka za ta gama da Iran
Bayanan hoto, Shugaba Donald Trump ya nemi zama da Iran

Shugaba Donald Trump, ya ce shi ba ya fatan gabza yaki da kasar Iran amma kuma ya gargade ta da cewa idan fa har rikici ya barke to fa Amurka za ta gama da ita ne.

Da yake magana da gidan talbijin na NBC a ranar Juma'a, Mista Trump ya kara da cewa a shirye Amurka take domin tattaunawa da kasar Iran.

Sai dai ya nanata cewa babu yadda za a yi Amurkar ta bari kasar Iran ta samar da makaman nukiliya.

Donald Trump ya sake yin karin haske kan sauya tunanin da ya yi na fasa kai wa Iran din hari domin mayar da martani kan harbo jirgin Amurka maras matuki da Iran din ta yi a makon nan, inda ya ce an sanar da shi cewa mutum 150 ka iya mutuwa sakamakon harin.

"Ban so a yi hakan ba. Ba na zaton hakan ya dace," In ji mista Trump.

Kasar Iran dai ta ce jirgin maras matuki ya kutsa sararin samaniyarta ne da safiyar ranar Alhamis.

Sai dai Amurkar ta musanta hakan, inda ta ce an harbo jirgin nata a sararin samaniyar kasa da kasa.

Amurka ta ce Iran ta yi babban kuskure
Bayanan hoto, Tarkacen jirgin da Iran ta harbo ya zama abin tunkaho ga Iran din

Ana ci gaba da samun rashin jituwa tsakanin Amurka da Iran, inda Amurkar ta zargi Iran din da kai wa wasu jiragen ruwa masu dauke da danyen mai hari, a yankin gabas ta tsakiya.

Kasar Iran ta sanar da cewa, nan ba da jimawa ba za ta ci gaba da makamin nukiliya fiye da abin da dokokin kasa da kasa suka iyakance mata.

A bara ne dai Amurka, bisa radin kanta ta fice daga yarjejeniyar dakatar da Iran daga mallakar makamin nukiliya da kasashen duniya suka rattaba wa hannu.

Yanzu haka Amurka ta nemi Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zauna ranar Litinin domin tattaunawa kan Iran.