Iran ta yi gagarumin kuskure da ta harbo jirginmu - Trump

Rundunar sojin Amurka ta bayyana jirgin maras matuki da RQ-4A Global Hawk irin wannan

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Rundunar sojin Amurka ta bayyana jirgin maras matuki da RQ-4A Global Hawk irin wannan

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Iran ta yi "gagarumin kuskure" da ta harbo jirgin yakin Amurka a mashigar Tekun Hormuz.

Sai dai ya shaida wa manema labarai cewa harin ka iya zama kuskure ne da wani ya yi, yana mai cewa: "Ina ganin ba da gangan ba ne."

Dakarun musamman na Iran (Islamic Revolution Guards Corps IRGC) sun ce jirgin ya saba ka'ida bayan da ya shiga yankin sararin samaniyarta.

Amma dakarun Amurka sun ce jirgin na shawagi a sararin samaniyar gabar ruwan kasashen duniya ne.

Wannan abin ya faru ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin Iran da Amurka take kara yin tsami.

A ranar Litinin, ma'aitakar tsaron Amurka ta ce za ta kara tura karin dakaru 1,000 ga yankin don mayar da martani ga "take-taken" Iran.

Amurka ta kuma zargi Iran da kai hari ga wasu jiragen ruwa na mai biyu ranar Alhamis din da ta gabata a kusa da mashigar ruwa ta Hormuz da ke gabar tekun Oman.

Sai dai Iran ta musanta zargin.

Wannan ne karo na biyu a wata guda da ake kai hari kan jiragen ruwan mai a yankin, inda kaso daya bisa biyar na danyen man fetur din duniya yake wucewa ta nan.