Takunkumin Amurka ya jefa Iran cikin matsin tattalin arziki

Asalin hoton, EPA
Shugaban Iran, Hassan Rouhani ya yi gargadin cewa rayuwa za ta yi wahala nan gaba a lokacin da tattalin arzikin kasar ke shiga matsi saboda sabbin takunkuman da Amurka ta kakaba mata.
Mr Rouhani ya ce Iran na iya fuskantar matsalolin tattalin arziki fiye da na shekarun 1980 a lokacin da kasashen duniya suka kakaba mata takunkumai lokacin yakinta da Iraqi.
Ya yi kira ga bangarorin siyasa a Iran da su hada kai su yi aiki tare.
Amurka ta sake kakaba takunkumanta ne bayan da Shugaba Trump ya janye Amurkar daga yarjejeniyar nukiliyar Iran inda itama Iran din ta yi barazanar cewa za ta ci gaba da gwajin nukiliyarta idan sauran kasashen suka ci gaba da hulda da Amurkar.
Tun bayan nan ne kuma harkar man da Iran ke fitarwa kasashen waje ya tsaya cik.
Mista Rouhani ya ce'' a lokacin yakin da muka yi a baya, ba mu samu matsala da bankuna ko kuma ta fuskar sayar da man fetur ba, an kakaba mana takunkumi ne kawai ta bangaren sayen makamai.''
Wane irin matsi Iran ke fuskanta?
Shugaba Rouhani na fuskantar matsi na cikin gida musamman daga kungiyoyi daban-daban tun bayan da Amurka ta janye daga yarjejeniyar nukiliyar da gwamnatin Mista Rouhani ta sa wa hannu.
Karkashin yarjejeniyar, Iran ta amince da takaita manya-manyan gwaje-gwajen nukiliyarta da kuma amincewa da hukumomin da ke kula da harkokin nukiliya su sa ido kan ayyukanta.
Takunkuman da Amurkar ta kakaba mata musamman kan wuta da kuma sufurin ruwa da bangaren hada-hadar kudade sun kawo cikas ga fitar da man fetur din kasar wanda hakan ya jawo matsala ga jarin kasar a kasashen ketare.
Takunkumin ya jawo hana kamfanonin mai na Amurka su rinka cinikayya da Iran kai tsaye da kuma duk wata kasa ko kamfani da ke cinikayya da Iran.

Asalin hoton, Reuters
Hukumar bayar da lamuni ta duniya ta yi hasashen cewa tattalin arzikin Iran zai ragu da kusan kashi 6 cikin 100 a bana.
A watan da ya gabata ne dai Amurka ta ayyana wata rundunar tsaro da ke Iran wato ''Islamic Revolutionary Guard Corps'' a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.
Iran dai ta yi ikirarin ramuwar gayya ga Amurka inda take da niyyar toshe wata mashigar teku ta ''Strait of Hormuz '' inda hanya ce da man fetur din da kasashe da dama na duniya ke amfani da shi ke wuce wa.











