Rikicin Gabas ta Tsakiya: Iran ta harbo jirgin yakin Amurka

A US Navy MQ-4C Triton unmanned aircraft system prepares to land at Naval Air Station Patuxent River, Md., Sept. 18, 2014, after completing a cross-country flight from California. The Triton will conduct flight testing at Patuxent River in preparation for an operational deployment in 2017. (US Navy photo by Kelly Schindler

Asalin hoton, US Navy/Kelly Schindler

Bayanan hoto, Wani jami'in Amurka ya bayyana sunan jirgin da US Navy MQ-4C Triton

Dakarun Iran sun harbo wani jirgin yakin Amurka mara matuki wanda ke shawagin tattara bayanan sirri a sararin samaniyar mashigar ruwan ta Hormuz.

Dakarun musamman na Iran (Islamic Revolution Guards Corps IRGC) sun ce jirgin ya saba ka'ida bayan da ya shiga yankin sararin samaniyarta.

Amma dakarun Amurka sun ce jirgin na shawagi ne a sararin samaniyar gabar ruwan kasashen duniya ne.

Babban kwamandan dakarun Manjo Janar Hossein Salami ya ce harbo jirgin "sako ne karara ga Amurka" cewa Iran "ba kanwar lasa ba ce."

Wannan abin ya faru ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin Iran da Amurka take kara yin tsami.

A ranar Litinin, ma'aitakan taron Amurka ta ce za ta kara tura karin dakaru 1,000 ga yankin don mayar da martani ga "take-taken" Iran.

Amurka ta kuma zargi Iran da kai hari ga wasu jiragen ruwa na mai biyu ranar Alhamis da ta gabata a kusa da mashigar ruwa ta Hormuz da ke gabar tekun Oman.

Sai dai Iran ta musanta zargin.

Wannan ne karo na biyu a wata guda da ake kai hari kan jiragen ruwan mai a yankin, inda kaso daya bisa biyar na danyen man fetur din duniya yake wucewa ta nan.