An daure wanda ya yada harin masallacin New Zealand ta Facebook

Asalin hoton, AFP
An daure wani mutum tsawon wata 21 a gidan yari cikin kasar New Zealand saboda yada wani bidiyo na harin kare dangin da aka kai masallacin Christchurch ta intanet.
Philip Arps mai shekara 44 ya amsa tuhumar da aka yi masa kan rarraba bidiyo.
Mutum 51 aka kashe a harbe-harben wanda kuma maharin ya watsa wani bangarensa kai tsaye a shafin sada zumunta.
Washe gari ne, Philip Arps ya yada bidiyon ga mutum talatin, kuma ya yi kokarin yin wani kwafin wanda ya yi wa kwaskwarima.
Kotu ta saurari cewa mutumin na da matsanancin ra'ayin kin jinin musulunci kuma bai nuna alamun gyara halinsa ba.
Alkali ya ce ayyukansa na raba bidiyon kashe-kashen a lokacin da 'yan'uwa da dangin mamatan ke dakon su san ko an kashe makusantansu, mugun abu ne kuma babu tausayi a ciki







