Lagos ce ta fi yawan wadanda suka karbi katin zabe

katin zabe

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta fitar da adadin yawan mutanen da suka yi rijistar katin zabe da kuma wadanda suka karbi katin zuwa yanzu.

INEc ta ce mutum miliyan tamanin da hudu da dubu hudu da tamanin da hudu ne 84,004,084 suka yi rijista a fadin kasar, yayin da mutum miliyan saba'in da biyu da dubu dari bakwai da saba'in da biyar da dari biyar da biyu 72,775,502 ne suka karbi katin.

A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Twitter, INEC ta ce mutum miliyan goma sha daya da dari biyu da ashirin da takwas da dari biyar da tamanin da biyu 11,228,582 ba su karbi nasu katin ba.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

A jerin yawan masu rijistar na jihohin da INEC din ta fitar dai, jihar Legas ce ta fi kowace jiha yawan wadanda suka yi rijista da mutum miliyan 6,570291 amma mutum miliyan 5,531,381 ne suka karbi katinsu zuwa yanzu.

Jihar Kano ce ta biyu bayan Legas wajen yawan masu rijista inda take da mutum miliyan 5,457,747, sannan mutum 4,696,747 ne suka karbi katinsu zuwa yanzu.

Ga dai taswirar yawan wadanda suka yi rijista da wadanda suka karbi katin a kasa, kamar yadda hukumar zaben ta wallafa.

yawan masu zabe

Asalin hoton, InEC