Nan muka kawo karshen shirin da fatan za ku tara nan gaba.
Nine Nasidi Adamu Yahaya tare da Mohammed Abdu Mamman Skeeper mu muke ce muku sai anjima.
Wannan shafi na kawo muku labarai da rahotanni da bayanai har ma da martani kan matakin da hukumar zaben Najeriya ta dauka na dage zaben.
Nasidi Adamu Yahya and Mohammed Abdu
Nan muka kawo karshen shirin da fatan za ku tara nan gaba.
Nine Nasidi Adamu Yahaya tare da Mohammed Abdu Mamman Skeeper mu muke ce muku sai anjima.
Kananan 'yan kasuwa sun ci gaba da gudanar da kasuwancinsu a Makurdi, bayan da hukumar zabe ta Nigeria ta dage zaben da ta shirya gudanarwa.

Gwaman jihar Imo Rochas Okorocha ya yi bayani kan daga wannan zabe
Jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta yi zargin cewa jam'iyyar APC mai mulki da fadar shugaban kasar ne suka kitsa dage zaben Najeriya domin bai wa shugaban kasar damar magudin zabe, tana mai cewa 'yan Najeriya ba za su amince da duk wani yunkurin magudi ba.

Asalin hoton, Getty Images
Dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kama hanyarsa ta komawa Abuja inda zai yi taro da masu ruwa da tsaki na jam'iyyarsa da kuma sauran jama'a kan dage zaben da INEC ta yi.

Hukumar zaben Najeriya ta shirya tsaf domin yi wa masu sanya ido na kasashen waje kan zaben kasar jawabi kan dalilanta na dage zabukan 2019.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Tun bayan da hukumar zaben Najeriya ta sanar da dage manyan zabukan kasar, masu mu'amala da shafukan sada zumunta musamman Twitter a kasar suka soma aike wa da sakonni da ke nuna shaukinsu na son komawa kasar Canada.
Sakonnin sun kunshi na ban dariya da ban haushi da gatsine.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Karshen labarin da aka sa a X, 3
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya garzaya Abuja daga Katsina. Sanarwar da ya fitar ta ce shugaban ya yanke shawarar komawa Abuja ne saboda ya tabbatar cewa taron da hukumar zabe za ta gudanar da masu ruwa da tsaki ya yi nasara.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Kungiyar tuntuba ta ‘yan arewa mai nsuna Arewa Consultative Forum (ACF) ta bayyana takaicinta na dage babban zabe da Hukumar Zaben Najeriya ta yi.
Kungiyar ta ce dagewar ya kamata a ce an yi ta tun a baya domin a rage wa ‘yan kasa da sauran wadanda abin ya shafa wahalhalu.
“Shirye-shiryen da INEC ta ce ta yi ya kara wa ‘yan Najeriya kwarin gwiwa game da samun cikakken zabe na adalci. ACF da ‘yan Najeriya ba su da wani zabi face su ci gaba da fatan INEC ta cika alkwarainta na zabe mai adalci.’
A bayanan da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban ya shawarci ‘yan Najeriya da su kauce wa tashin hankali.
Ya kuma ce zai dawo Abuja domin ci gaba da ayyukan gwamanti.
Na yanke shawarar dawowa Abuja domin halartar ganawa da INEC ta shirya gudanarwa da masu-ruwa-da-tsaki da karfe 2 na rana.
“Ina shawartar ‘yan Najeriuya da su guje wa taashin hgankali kuma su bzama ‘yan kasa na garidomin kada su kawo wa dimokradiyyar Najeriya nakasu.”

Asalin hoton, Getty Images
Shirin safe da muka gabatar kai tsaye a radiyon BBC.
Sakamakon dage zaben da aka yi mun tsara kawo muku shirin awa daya da rana da kuma shirin maraice.
'Yan jarida da dama ne suka yi shirin daukar labarin yadda tsohon mataimakin shugaban Nigeria, Atiku Abiubakar zai yi zabe a Jada jihar Adamawa, Nigeria.
Sai kuma hukumar zabe ta ce ta dage zaben.

'Yan kasuwar kayan miya inda akafi sani da ramin Kura a cikin garin Sokoto,sun fito sun ci gaba da sana'ar su, bayan dage zabe.