Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ngozi Okonjo-Iweala ta zama darakta a kamfanin Twitter
Kamfanin sada zumunta na Twitter ya nada tsohuwar Ministar Kudin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin daya daga cikin daraktocinsa.
Kamfanin wanda yake da hedkwata a jihar California ta kasar Amurka ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis.
Misis Okonjo-Iweala ita ce mace ta farko da ta fara zama ministar kudin kasar da kuma ministar harkokin waje a tsakanin shekarun 2003 zuwa 2006.
Har ila yau ta kara sake zama ministar kudin kasar kuma mai kula da harkokin tattalin arziki a zamanin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan.
Shugaban kamfanin Omid Kordestani ya ce yana yi wa Misis Okonjo-Iweala da Mista Robert Zoellick, wanda shi ma kamfanin ya dauke shi aiki a matsayin darakta, maraba kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.
Ita ma Okonjo-Iweala ta bayyana farin cikinta da sabon matsayin, kamar yadda ta bayyana a shafinta na Twitter.
Tsohuwar ministar ta taba yin aiki da bankin duniya, inda ta shafe fiye da shekara 20 a hedkwatarsa da ke birnin New York na Amurka.
Karanta wadansu karin labarai