Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rayuwar Buhari a gida daga fitowa zuwa faɗuwar rana
Ƴan Najeriya na ci gaba da alinin rasuwar tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu ranar Lahadi 13 ga watan Yulin 2025, yana da shekara 82 a duniya.
Kafin rasuwar tasa ya yi jinya lamarin da ya sa aka garzaya da shi birnin Landan domin duba lafiyarsa a wani asibiti, inda a can ne kuma ya cika.
Tuni dai gwamnatin jihar Katsina ta bayar da hutun ranar Litinin domin nuna alhini ga rasuwar tsohon shugaban ƙasar, wanda ɗan asalin jihar ne.
Yayin da ke ci gaba da alhinin, mun yi nazari kan yadda yake gudanar da harkokin rayuwarsa na yau da kullum.
Kamar kowanne ɗan'adam, shi ma yana da tsarin yadda yake gudanar da rayuwarsa a kullu-yaumin, daga fitowar rana zuwa faɗuwarta.
Tsohon ministan jiragen sama na Najeriya a zamanin mulkin Buharin - wanda kuma ke da alaƙa ta kut da kut da shi, da kuma iyalinsa - ya bayyana wa BBC yadda tsohon shugaban ƙasar ke gudanar da harkkin rayuwarsa daga asuba zuwa kwanciya barci.
'Mutum ne mai haƙuri da kula da dangi'
Hadi Sirika ya bayyana marigayin da mai ɗimbin imani , wanda a cewarsa ke mutunta rayuwar ɗan'adam da ta dabbobi da sauran hannun Allah.
Ya ce ƙara da cewa mutum ne mai tausayi da gaskiya da riƙon amana tare da kyautatawa.
''Marigayin mutum me da ba ya son wulaƙanta ɗan'adam da duka hallitun Ubangiji, musamman dabbobin da yake kiwonsu'', in ji shi.
Mutum ne mai haƙuri da kula da dangi, ''baya son ganin an wulaƙanta duk wani abu mai rai'', in ji hadi Sirika.
'Yana tashi daga barci kafin sallar asuba'
Makusancin Buharin ya ce tsohon shugaban ƙasar kan tashi daga barci, tun kafin ketowar asuba, sannan ya kammala shirin zuwa masalllaci domin yin sallar jam'i.
''Bayan kammala sallar asuba yakan zauna ya yi azkar daidai gwargwado kafin ya koma gidansa, kuma ba ya komawa barci''.
Idan lokacin da yaransa ke zuwa makaranta ne zai tabbatar da yaransa sun tashi domin su tafi makaranta a kan lokaci, a cewar Hadi Sirika.
''Bayan hakan yakan zagaya gidansa kaf, domin yadda kowa ya tashi a gidan'', in ji Hadi Sirika.
'Kullum sai ya saurari BBC Hausa'
Hadi Sirika ya ce bayan kammala duk waɗancan hidimomi, tsohon shugaban ƙasar kan zauna domin sauraron radiyo, mutum ne son sauraren radiyo, musamman BBC Hausa.
''Bana tsamanin akwai shirin BBC Hausa da yake wuce shi, zai kunna ya saurari duka shirin BBC'', in ji tsohon Ministan.
Hadi Sirika ya ce a irin sauraron BBC Hausa da yake yi ne, wata rana ya ji musayar kalamai da tsohon ministan ya yi da wani.
''Nan take ya kirawoni ya ce me ya sa kuke musayar kamalamai da wane, rashin fahimtar juna ne ya sa abin naku ya kai haka'', in ji shi.
'Mutum ne mai barkwanci ga iyalansa'
Makusancin Buharin ya ce tsohon shugaban ƙasar mutum ne da ya gina kyakkyawar alaƙa da iyalansa.
''Duk da cewa ba zan iya cewa komai game da rayuwar matarsa ta farko ba, amma dai ga ƴaƴansa mutum ne mai kyakkyawar alaƙa da su''.
''Rayuwar da yake yi da ƴaƴansa rayuwa ce ta barkwanci da wasa da dariya da tsausaya da kuma ƙaunar juna''.
''Idan ka ga yadda yake rayuwar barkwanci da ƴayansa sai ka ɗauka jikokinsa ne ba ƴaƴa ba'', in ji Hadi Sirika.
Yakan zauna da iyalansa su ci abinci tare su yi raha su yi barkwanci, a cewar Sirika.
'Yana yawan nasiha da riƙon amana'
Tsohon Ministan ya ce a mafi yawan lokuta idan sun zanuanda marigayin kana yawaita yi musu nasiha da riƙon amana.
''Idan aiki aka ba ka to ka riƙe amana, domin ai shugaban ƙasa na shi ne kadai ke mulkin ƙasar ba''.
''Yana yawan yi magana game da yadda tsarin mulki yake, (kowane mai muƙami yana da da rawar da zai taka)''. in ji shi.
Wane abinci Buhari ya fi so?
Makusancin Buharin ya ce abinci da tsohon shugaban ƙasar ya so shi ne tuwon alkama miyar kuka da kuma ganye kamar salat.
Ya kuma ce marigayin ma'acn son shan shayi ne, da bai fiya cin abinci da yawa ba.
''Yana da saurin jin yunwa, amma kuma ba ya cin abinci da yawa, da ya ci kaɗan sai ya ƙoshi'', in ji shi.
Yana son dabbobi da shuke-shuke
Hadi Sirika ya ce Buhari mutum ne mai son tsirrai da dabbobi.
Ya kuma ce mutum ne mai son zuwa gonarsa, musamman ya ga dabbobinsa da yake kiwonsu.
''Shi duk inda ya zauna sai ya shuka itatuwa, ya yi lambu, ya zauna tare da su'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa marigayin mutum ne mai son motsa jiki da yawa.