Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rasu yana da shekara 82
Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rasu ranar Lahadi yana da shekara 82 da haihuwa.
Wata sanarwa da Garba Shehu mai magana da yawunsa ya fitar ta ce Buhari ya rasu a wani asibiti da ke birnin Landan.
Fadar shugaban Najeriya ta ce ya rasu da misalin ƙarfe 4:30 "sakamakon doguwar jinya".
"Shugaban ƙasa ya umarci Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya tafi Landan domin ya rako gawar Buhari zuwa gida Najeriya," a cewar wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa.
A makon da ya gabata ne aka kwantar da tsohon shugaban a asibiti bayan ya je duba lafiyarsa kamar yadda ya saba, amma daga baya sai ya kamu da rashin lafiya.
Sai dai Garba Shehu bai bayyana rashin lafiyar da Buhari ke fama da ita ba a lokacin, ko kuma sunan asibitin da yake jinyar.
Buhari ya mulki Najeriya a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa daga 2015 zuwa 2023, inda ya miƙa wa Bola Tinubu ragama bayan jam'iyyarsu ta APC ta sake lashe zaɓen shugaban ƙasa.
Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin sassauto da tutocin Najeriya "a matsayin girmamawa ga marigayin", in ji sanarwar.
An haifi Muhammadu Buhari a ranar 17 ga watan Disambar shekarar 1942 a garin Daura da ke jihar Katsina, kuma shi ne ɗa na 23 a wajen mahaifinsa Malam Harɗo Adamu wanda ya rasu lokacin Buhari yana ɗan shekara huɗu.
Buhari ya yi takarar shugaban ƙasa har karo huɗu kuma a na huɗun ne ya yi nasarar hawa mulki, inda ya yi shekara huɗu sau biyu. Shi ne shugaban Najeriya na huɗu tun bayan komawa mulkin dimokuraɗiyya a 1999.
Ya haifi ƴaƴa 10 da matansa biyu, Safinatu Yusuf wadda suka rabu a baya da kuma Aisha Halilu wadda aka fi sani da Aisha Buhari - wadda ita ce take yi masa takaba.
Muhammadu Buhari ya halarci makarantar allo sannan ya yi kiwon shanu, kafin ya shiga makarantar firamare a garin Daura da Mai'Adua, inda ya kammala a 1953.
Daga nan kuma marigayin ya tafi zuwa makarantar sakandare ta Katsina Provisional Secondary School daga 1956 zuwa 1961.