Me ya kai Obasanjo da Buhari kotu a Paris?

Lokacin karatu: Minti 4

Tsoffin shugabannin Najeriya biyu, Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari sun bayyana a gaban wata kotun cinikayya ta ƙasa da ƙasa da ke birnin Paris na a ƙasar Faransa domin bada bahasi dangane da kwangilar aikin gina cibiyar samar da wutar lantarki ta Mambilla da ke jihar Taraba.

Wani kamfani mai suna Sunrise Power ne dai ya kai gwamnatin Najeriya ƙara kan saɓa ƙa'idojin kwangilar, inda yake neman gwamnatin ta biya shi dalar Amurka biliyan biyu da miliyan 300 a matsayin diyya na asarar da aka janyo masa.

Wata majiya ta tabbatar wa da BBC kasancewar Obasanjo da Buhari a birnin Paris ɗin inda kowannensu zai bayar da shaida kan abin da ya sani dangane da wannan kwangila da aka bayar da ita a 2003, lokacin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo.

Abin da ya faru

A 2003 ne gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ta bai wa kamfanin na Sunrise kwangilar gina da kula da tashar wutar lantarki ta Mambilla da za ta samar da megawatt 3,050.

To sai dai a wata tattaunawa da tsohon shugaban, Olusegun Obasanjo ya yi da jaridar The Cable a 2023 kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito, ya ƙalubalanci ministan wutar lantarki na zamaninsa, Olu Agunloye wanda shi ne ya bayar da kwantaragin ga Sunrise.

"A lokacin da nake shugaban ƙasa, babu ministan da yake da damar amince wa da abin da ya zarce naira miliyan 25 ba tare da sahhalewar shugaban ƙasa ba. Ba zai yiwu Agunloye ya bayar da kwangilar dala biliyan shida ba tare da izinina ba kuma ni dai ban ba shi izini ba."

A watan Okotoban 2017 ne kuma kamfanin na Sunrise ya shigar da ƙarar neman diyyar saɓa ƙa'idar kwantaragin, inda yake neman gwamnatin Najeriya ta biya shi diyyar dala biliyan biyu da miliyan 354.

Rahotanni sun nuna cewa a 2020 tsohon ministan lantarki na Najeriya zamanin shugaba Buhari, Sale Mamman ya cimma sulhu da kamfanin a wajen kotu inda aka amince za a bai wa kamfanin dala miliyan 200 a cikin makonni biyu.

To amma kamfanin ya ɗaukaka ƙaran neman diyyar dala miliyan 400 a kotun cinikayya ta ƙasa da ƙasa da ke Paris bisa zargin karya ƙa'idojin yarjejeniyar kwantaragin.

Kamfanin ya ce ya kai ƙarar ne saboda gwamnati ta karya alƙawarin biyar diyyar dala miliyan 200 a cikin makonni biyu.

Ba mu tilasta kowa zuwa Paris ba - Gwamnatin Tinubu

Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, Bayo Onanuga, a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar dangane da batun, ya ce sam gwamnatinsu ba ta tilasta wa tsoffin shugabannin ƙasar biyu zuwa Paris ba domin bayar da bahasi.

Rahotanni dai sun ta fitowa daga kafafan watsa labaran Najeriya cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ce ta tilasta wa tsoffin shugabannin zuwa Paris.

Sanarwar ta ƙara da cewa "duk da cewar batun shari'ar abu ne da bai kamata a bayyana shi a kafafen watsa labarai ba, amma muna ba ku tabbacin cewa gwamnatin shugaba Tinubu ba ta tilasta wa kowa ba kan ya bayar da sheda ko ya ƙi bayar da shedar a gaban kotun ba."

Dukkan mutanen da suka bayyana a kotun sun yi hakan ne bisa raɗin kansu da kuma kishin ƙasa." In ji Bayo Onanuga.

Taƙaitaccen tarihin wutar Mambilla

A shekarar 1982 ne aka bijiro da maganar aikin wutar lantarkin ta Mambila. Daga lokacin gwamnatoci dabdan-daban sunyi ta sauya tsarin aikin wutar.

Misali tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo yayin kaddamar da fara aikin tashar wutar a ranar 12 ga watan Afrilun shekarar 2007 a garin Gembu da ke kan tsaunin Mambila, ya bayyana cewa tashar za ta samar da megawat 2600 na wuta kuma ya sa an gina ofisoshi da gidaje inda ma'aikata da za su yi aikin za su zauna tare da ajiye kayan aiki.

Bayan Shugaba Obasanjo ya sauka daga kan karagar mulki, an sake fadada fasalin aikin a zamanin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan a shekarar 2012 inda aka kara shi zuwa megawat 3050.

Sai dai kuma a watan Yulin shekarar 2021 gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta rage yawan megawatt din zuwa 1,520.

Tsohon ministan wuta Injiya Saleh Mamman ya ce an dauki matakin ne domin ganin ya gudana.

Abin da BBC ta gano

Binciken da BBC ta gudanar yayin ziyarar datsohon wakilinta Salihu Adamu Usman ya kai makwararar ruwa na 'Tambi Waterfalls' a tsaunin Mambila wanda shi ne jigo daga cikin wurare 3 da za a kafa cibiyar wutar lantarkin Mambila domin ganin yadda wurin yake ya gano cewa ba a fara aikin ba.

Babu hanyar mota da za ta kai mutum zuwa kan tsaunin da za a yi aikin kuma babura ne kadai ke iya zuwa sai kuma kafa.

Ana shafe sa'o'i 5 ana tafiya kan babur sai kuma sa'a daya ta tafiyar kafa.

Bayan isa filin da za a yi aikin wutar, BBC ta tarar babu aikin da aka yi a wurin.

A tsawon wadannan shekarun dai an yi ta maganganu daban-daban kan inda aka kwana wajen aiwatar da aikin da ake sa ran zai samar wa Najeriya isasshiyar wutar lantarki.

Ko da a shekarar 2020 ma a wata hira da BBC, tsohon ministan wutar lantarki Injiya Saleh Mamman ya ce akwai tatsuniya kan batun wutar ta Mambila.

Idan har aikin ya kammala tashar za ta kasance mafi girma a Najeriya kuma daya daga cikin manyan tashoshin wuta a nahiyar Afirka.

Najeriya na samar da megawat na wuta tsakanin 5,000 zuwa 5400 a lokaci da dukkan tashoshin samar da wuta na kasar ke cikakken aiki.