Waiwaye: Ficewar El-Rufai daga APC da ƙai ƙarar Akpabio zuwa MDD

Lokacin karatu: Minti 5

Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.

Abin da ya sa na fita daga APC na koma SDP - El-Rufa'i

Nasiru El-Rufai

Asalin hoton, Nasir El-Rufa'i/FB

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya tabbatar da ficewarsa daga jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar, tare da komawa jam'iyyar SDP.

Hakan ya kawo ƙarshen raɗe-raɗin da ake yi na inda tsohon gwamnan zai nufa bayan alamun da suka nuna cewa ya raba gari da jam'iyyar APC.

A ranar Litinin ne El-Rufa'i ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce: "A yau 10 ga watan Maris, 2025, na miƙa takardar fita daga jam'iyyar APC a mazaɓata da ke Kaduna, wadda za ta fara aiki nan take. Kafin wannan lokaci na kammala tuntuɓar magabatana, da abokan tafiya da magoya baya a faɗin ƙasar nan game da inda za mu dosa, yanzu na yanke shawarar komawa jam'iyyar Social Democratic Party, kuma zan kasance a cikinta wajen tafiyar da al'amurana na siyasa a nan gaba."

A kwanakin baya, lokacin tattaunawarsa da kafar talabijin ta Arise, El-Rufa'i ya koka kan cewa "jam'iyyar APC ta sauka daga kan manufifin da aka ƙirƙire ta a kai."

EFCC ta ce ta samu nasarar da ba ta taɓa samu ba a tarihi

Shugaban EFCC

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK

Hukumar EFCC ta ce a shekarar 2024 ta samu nasarar da ba ta taɓa samu ba tun daga lokacin da aka ƙirƙire ta.

Ta ce a shekarar ta ƙwato kuɗaɗe da suka haɗa da naira biliyan 364.6 da dala miliyan 214.5 da fan 54,318.64 da yuro 31,265 da kuɗin ƙasar Canda, dala 2,990 sai kuma kuɗin ƙasar Australia, dala 740, kamar yadda ta bayyana.

Wasu kuɗaɗen da hukumar ta ƙwato sun haɗa da CFA7,821,375 da dirham ɗin UAE 170 da riyal 5,115 da W73,000, yen 105, da GH¢ 225 da rand 50.

Hukumar ta ƙara da cewa a shekarar ce ta ƙwato rukunin gidaje 750, wanda shi ne mafi girma a tarihin hukumar.

Haka kuma ta ƙwato kuɗaɗen kirifto irin su Bitcoin guda 13.37 wanda darajarsu ta kai dala 572,992.86 da Ethereum 5.97886094 masu ƙimar dala 13,353.06 da USDT 1,002.547631 da sauransu.

Hukumar ta kuma ƙwato kamfani da otel da zinare da fulotai.

Ina nan daram a jam'iyyar APC mai mulki - Buhari

Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce har yanzu shi ɗan APC ne, kuma ya fi so ana alaƙanta shi da ita.

Buhari ya bayyana haka ne a wata sanarwa da tsohon kakakinsa, Garba Shehu ya fitar, inda ya ce ba ya so ya bar kowa a cikin ruɗani game da inda yake, domin a cewarsa ba zai taɓa juya wa jam'iyyar da ta ba shi damar tsayawa takara har ya yi shugabancin ƙasa na wa'adi biyu ba.

"Ni ɗan APC ne, kuma na fi so ana alƙanta da jam'iyyar, sannan zan yi duk mai yiwuwa wajen tallata jam'iyyar.

Buhari ya ƙara da cewa babu abin da zai ce game da jam'iyyar APC sai dai godiya bisa goyon bayan da ya samu daga jam'iyyar, a lokacin da yake mulki da bayan ya kammala wa'adinsa, wanda a cewarsa alfarma ce babba da ba zai taɓa mantawa ba.

Gwamnatocin baya ba su yi wa yaran da za a haifa tanadi ba - Tinubu

Bola Tinubu

Asalin hoton, Nigerian Presidency

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ke yi, tana yi ne da nufin gyara makomar yara masu tasowa.

Yayin da yake jawabi ga ƙungiyar ƴan majalisa ta uku - wadda ya kasance cikin a Jamhuriya ta uku - da suka kai masa ziyara a fadarsa, Shugaba Tinubu ya ce a baya ƙasar na kashe kuɗaɗen yaran ƙasar da ba a kai ga haihuwarsa ba.

"Shekara 50 da suka gabata, Najeriya na kashe kuɗaɗen yaran da ba a kai ga haihuwarsu ba, tare da mayar da hankali kan man fetur wajen samun kuɗin shiga. Ba a yi wani tsari na tallafa wa yaran da za a haifa a gaba ba," kamar yadda ya ce.

Shugaban ya kuma bayyana tarin matsalolin da ya fuskanta a farkon mulkinsa, musamman fannin tattalin arzikin da rayuwar jama'a.

"Mun fuskanci tarin ƙalubale a lokacin da na karɓi mulki. Inda ba mu ɗauki matakai ba da yanzu ƙasar ta talauce, kuma ai haƙƙinmu ne mu kare tattalin arzikinmu daga rugujewa'', in ji Shugaba Tinubu.

Sanata Natasha ta kai ƙarar Akpabio zuwa MDD

Sanata Natasha

Asalin hoton, Natasha Akpoti/X

Sanata Natasha Akpoti-Uguaghan ta yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta hukunta majalisar dattawan Najeriya game da dakatarwar da aka yi mata na tsawon wata shida.

Majalisar dattawan ta dakatar da sanata Natasha ne kan zargin yunkurin cin zarafin da ta yi wa shugaban majalisar, Godswill Akpabio.

Da take magana a taron mata na ƴanmajalisar ƙasashen duniya na Majalisar Ɗinkin Duniya da aka yi a birnin New York, Akpoti-Uduaghan ta ce tana fuskantar "tsangwama a siyasa da kuma barazana" saboda ta nemi a yi bincike na gaskiya kan zarge-zargen cin zarafi ta hanyar lalata da ta yi wa Akpabio.

Ta ƙara da cewa ta yi kiran ne don "kada duniya ta zura ido a yi shiru yayin da dimokraɗiyya da haƙƙoƙin mata ke cikin tasku a Najeriya".

Hare-hare sun kashe 'yan Najeriya 1,010 a watan Fabrairu - Rahoto

Ƴansadan Najeriya

Asalin hoton, Nigeria Police

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mutum 1,010 ne aka kashe a faɗin Najeriya sakamakon hare-haren 'yanbindiga da na jami'an tsaro cikin watan Fabrairun da ya gabata, a cewar rahoton kamfanin Beacon Security and Intelligence.

Alƙaluman na watan Fabrairu sun nuna cewa an samu raguwar sace mutane zuwa 955 daga 1,101 a watan Janairu, amma kuma kashe-kashe ya ƙaru - bayan samun 991 a watan Janairu.

Sabon rahoton na watan Fabrairu ya ce daga 1 zuwa 28 ga watan, an kai hare-hare ko kuma tashin hankali 716 jimilla, waɗanda suka jawo sacewa ko kuma garkuwa da mutum 955.

Kazalika, hare-haren sun ragu da kashi 2.19 idan aka kwatanta da watan Janairu, inda aka samu 732.

Mutum 592 (kashi 58.6 cikin 100) na mutanen da suka mutu fararen hula ne, inda 'yanbindiga suka kai hari 478 (kashi 66.76), jami'an tsaro suka kai 177 (24.72), in ji rahoton.

Jihohin Katsina, da Kaduna, da Neja, da Zamfara, da Sokoto, da Borno, da Kebbi ne suka fi fuskantar ƙaruwar hare-hare a watan, kamar yadda rahoton ya bayyana.

Ƴanbindiga sun sace wanda ya lashe gasar karatun al-Qur'ani ta Najeriya

Ƴan bindiga

Asalin hoton, Getty Images

Ƴanbindiga sun sace mutumin da ya zama zakaran gasar karatun al'qur'ani ta bana tare da danginsa a kan hanyar Faskari zuwa ƴankara a jihar Katsina.

Shugaban ƙaramar hukumar Faskari, Hon Musa Ado Faskari ya shaida wa BBC faruwar lamarin, inda ya ce ƴanbindigar sun sace Abdulsalam Rabi'u Faskari tare da mahaifinsa da ƴan'uwansa a lokacin da suke kan hanyar komawa gida bayan sun halarci fadar gwamnatin Katsina inda gwamna ya karrama gwarzon.

Hon. Musa Faskari ya ce gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda ne ya gayyaci , Abdulsalam Rabi'u Faskari tare da iyalansa ciki har da mahaifinsa a ƴan'uwansa, domin karrama shi bisa nasarar da ya samu ta zama gwarzon gasar karatun al-qur'ani da aka kammala a jihar Kebbi.

''A kan hanyarsu ta komawa gida ne, sun baro Funtua a kan hanyar Faskari zuwa ƴankara , ƴanbindiga suka tare su tare da yin garkuwa su duka, sai mutum guda da ya samu nasarar kuɓuta'', in ji shugaban ƙaramar hukumar.