Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amfani 6 da albasa ke yi a jikin ɗan'adam
- Marubuci, Abubakar Maccido
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reporter
- Aiko rahoto daga, Kano
- Lokacin karatu: Minti 2
Albasa kayan lambu ne da ake amfani da ita wajen girki domin inganta ɗanɗano da ƙamshi. Takan zo da launin ja ko kuma fari.
Ana iya cin ta ɗanye, ko a soya ko a gasa ko kuma a jefa ta cikin abinci, musamman a cikin miya.
"Sanadarin sulphur da ke cikin albasa na yaƙi da ƙwayoyin cuta da kuma kumburi a sassan jiki," in ji ƙwararriya kan harkar abinci, A'isha Bala Ahmad, kamar yadda ta shaida wa BBC.
Ta kuma ce akwai alamun da ke nuna cewa mutanen da ke yawan cin albasa ba su cika kamuwa da cutar daji, wato kansa ba, saboda tana da sinadarai masu tsaftace jiki.
Amfani shida da albasa ke da shi ga lafiya
- Haɓɓaka garkuwar jiki: Sinadarin Vitamin C da ke cikin albasa na taimaka wa jiki wajen yaƙi da cutuka.
- Bunƙasa lafiya zuciya: Albasa na ƙunshe da sinadarin flavonoids, kamar 'quercetin' wanda ke taimakawa wajen rage kitse da hawan jini.
- Yana iya daidaita sukarin cikin jini: Wasu sinadaran da ke cikin albasa, kamar allyl propyl disulfide za su iya taimakawa wajen rage tashin adadin sukarin da ke cikin jinin bil'adama.
- Kashe ƙwayoyin cuta: Sinadarin Sulphur da ke cikin albasa zai iya kashe cutuka da kuma rage kunburin sassan jiki.
- Taimawa wajen tace narkar da abinci: Albasana ƙunshe da abubuwan da ba su cika narkewa ba, wanda hakan zai taimaka wajen saurin niƙe abinci da kuma samar da ƙananan halittu masu amfani da cikin tumbi.
- Za ta iya kare mutum daga kansa: Alamu sun nuna cewa mutanen da ke yawan cin albasa ba su cika shiga haɗarin kamuwa da cutar kansa ba.
Sinadaran da ke cikin albasa ( a cikin kowane giram 100 na albasa)
- Calories: 40 kcal
- Protein: 1.1 g
- Carbohydrate: 9.3 g
- Dietary Fibre: 1.7 g
- Fat: 0.1 g
- Vitamin C: 7.4 mg (12% of daily value)
- Vitamin B6: 0.12 mg
- Folate: 19 µg
- Potassium: 146 mg
- Calcium: 23 mg
- Magnesium: 10 mg
- Phosphorus: 29 mg
Shawara ta musamman: Ƙwararriya kan harkar abinci Aisha Bala Ahmad ta ce ga masu son cin albasa ɗanya, su sani cewa za su iya jin zafi a ƙirjinsu ko kuma fitar da iska sosai bayan sun ci.
Domin kauce wa hakan, mutum zai iya dafa ta sama-sama domin kada saukaka wa cikinsa.