Saudiyya ta gabatar da buƙatar karɓar baƙuncin Kofin Duniya 2034

Asalin hoton, Getty Images
Saudiyya wadda ita kaɗai ce ke neman ɗaukar baƙuncin Kofin Duniya na 2034, ta gabatar da buƙatar neman ɗaukar gasar a hukumance.
A watan Oktoba ƙasar da yankin Gulf ta nuna muradin ɗaukar gasar a zahiri, bayan Australia ta janye daga neman baƙuncin gabanin cikar wa'adin da Fifa ta sanya.
Majalisar Fifa ce za ta tabbaatar da amincewa kan wannan buƙata a wannan shekarar.
Shugaban hukumar kwallon ƙafa ta SaudiyyaYasser Al Misehal ya ce za a amince da buƙatar ta Saudiyya saboda yadda take samun ci gaba cikin gaggawa.
Al Misehal ya ƙara da cewa: "Yana da muhimmanci mu gayawa daniya labarinmu.
"Mun samu wani irin ci gaba mai girma daga bangaren wasan mata da na maza, buƙatar tamu wata takardar gayyata ce ga duniya ta zo ta ga yadda tafiyarmu ke cike da albarka."
Duk da cewa ita kaɗai ce ta nemi ɗaukar nauyin gasar, dokokin Fifa na buƙatar sai an shigar da buƙatar neman hakan a hukumance.
An yi wa bukatar taken "Mu bunƙasa tare", wanda hukumar kwallon ƙafa ta Saudiyya ta ce zai haɗa tsakanin "masarauta, da mutanenta da kuma duniyar kwallon kafa".
Saudiyya ta zuwa jari da ya kai fan biliyan biyar a ɓangaren wasanni tun 2021, Ka zalika Yarima ya bayyana cewa wannan na ɗaya daga cikin hanyoyin fadade hanyoyin samun kuɗin ƙasar.
Gasar za ta zama ita ce ta farko da ƙasashe 48 za su halarta a ƙasa guda.
Moroko da Portugal da Sifaniya su ne za su ɗauki nauyin gasar ta 2030 a wani mataki na haɗin gwiwa, yayin da za a fara wasanni ukun farko za a yi su a Uruguay da Argentina da Paraguay.
Gasar 2026 da za a yi, za ta zama ta farko da ƙasashe 48, amma za a gudanar da ita ne a ƙasashen Amurka da Mexico da kuma Canada.











