Yadda TB Joshua ya yi rufa-rufa da ɓoye gawawwaki bayan rugujewar cocinsa

TB Joshua looks at the rubble of the collapsed church guesthouse of the Synagogue Church of All Nations in Lagos, Nigeria - 20 September 2014

Asalin hoton, AFP

    • Marubuci, Charlie Northcott & Tamasin Ford
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa Eye

BBC ta bankaɗo sabbin hujjoji da ke nuna cewa mai katafaren cocin nan na Najeriya, TB Joshua ya ɓoye gawawwaki, kuma ya razana dangin mutanen da lamarin ya ritsa da su, don yin rufa-rufa kan batun rugujewar ginin wanda ya hallaka aƙalla mutum 114 a shekarar 2014.

Rugujewar ginin na ɗaya daga cikin bala'i mafi muni da ya taɓa auka wa wani wurin ibada a Afirka.

Binciken BBC shi ne karon farko da wasu makusantan cocin TB Joshua Synagogue Church of All Nations (Scoan) a Lagos suka gabatar da shaidu na abin da ya janyo faruwar lamarin kusan shekara goma da ta wuce, da kuma yadda aka yi zargin limamin cocin ya kitsa duk rufa-rufar da aka yi.

Lamarin na zuwa ne bayan BBC ta bankaɗo ɗumbin cin zarafi da azabtarwar da mai cocin - ɗaya daga cikin cibiyoyin wa'azin addinin Kirista mafi girma a duniya, ya aikata.

Kwana biyu bayan rugujewar ginin a ranar 12 ga watan Satumban 2014, TB Joshua ya fito ya bayyana a bainar jama'a cewa lamarin yana da alaƙa da wani jirgin sama da ya keta ta saman ginin, wanda ake amfani da shi wajen tsugunnar da masu ibada da ke kai ziyara.

Sai dai binciken wani ƙwararren mai binciken sanadin mutuwa a Lagos ya yi daidai da bayanin ma'aikatan agaji, da suka ce gazawar ginin ce ta yi sanadin rugujewarsa, kuma sun ce an gina gidan ne ba tare da cikakken izini ba.

Sai dai shaidu sun faɗa wa BBC cewa an gargaɗi TB Joshua game da manyan matsaloli a ginin tun ma kafin faruwar bala'in. Sun ce bayanin giftawar jirgin sama "ƙarya ne".

"Ya sani ginin yana tangaɗi," cewar Emmanuel, wanda ya shafe tsawon sama da shekara goma a matsayin almajiran TB Joshua - wani rukunin riƙaƙƙun mabiya da suka zauna a cocinsa da ke Lagos.

Kamar sauran almajiran malamin waɗanda BBC ta zanta da su, ya zaɓi kawai ya yi amfani da suna ɗaya kawai.

Ya bayyana lokacin da limamin cocin yake karɓar wani rahoto, sa'o'i kafin faruwar lamarin, wanda ke cewa ginin yana "tangaɗi" kuma yana "jijjiga".

Ɗumbin shaidu sun ce ba a gargaɗi masu ziyara ba. Maimakon haka an shigar da fiye da mutum 200 cikin ɗakin cin abinci na ginin wanda ke ƙasan gidan don su yi kalaci - a nan aka zazzaunar da su, lokacin da dukkan hawa shida na ginin kuma ya faɗa musu.

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Da yawansu nan take suka riga mu gidan gaskiya, amma gini ya binne wasu fiye da 100 da ransu.

"Ina iya jin mutane suna ta ihu: 'A taimake ni, a cece ni, a cece ni,'" in ji Emmanuel, wanda ya isa wurin mintuna ƙalilan bayan rugujewar.

"Muryoyinsu suka riƙa dusashewa kuma kana iya fuskantar cewa mutanen suna gab da mutuwa."

Wasu sun bayyana munanan raunukan da wasu suka ji, inda suka rasa idanuwa da ƙafafuwa ko hannuwa - bayan sun ɓaɓɓalle sanadin ginshiƙan da suka faɗo kansu.

"A bayyane take ƙarara cewa ginin, ba a yi shi da niyyar zai yi tsawo kamar yadda TB Joshua ya mayar da shi ba," a cewar Rae, daga Birtaniya, wadda ta shafe tsawon shekara 12 a matsayin ɗalibar malamin cocin.

Ta ce tana nan lokacin da TB Joshua ya ba da umarni ga ma'aikatansa su gina ƙarin benaye a ginin: "Ba a yi harsashin ginin don ya ɗauki benaye masu hawa da yawa haka ba.

"Kawai ya yi ta ingiza su yana cewa: 'Ina son ya ƙara tsayi. Jazaman ne ya ƙra yin sama. Dole a ƙara ɗaga shi.'"

Mutane na ciki-cikin cocin waɗanda suka zanta da BBC sun kuma ce da mai yiwuwa an kuɓutar da rayuka, da a ce TB Joshua ya maida martani ga rushewar ginin cikin hanzari. Maimakon haka, suka ce sai ya toshe hanyar da ma'aikatan agaji za su bi su shiga wurin tsawon sa'a 24 - zargin da rahotannin labarai suka gaskata a lokacin.

A lokacin, akwai muhimmiyar dama ta ceto mutane da taimaka wa waɗanda suka ji raunuka, shaidun BBC sun ce wasu ma'aikatan cocin sun yi yunƙurin kuɓutar da rayuka amma cikin ganganci da rashin ƙwarewa. Ba tare da amfani da injina ko ƙwarewar ma'aikatan lafiya ba, inda suka riƙa amfani da kayayyaki daga sashen gyare-gyare na cocin.

A wani lamari, an zargi wani ma'aikacin cocin da amfani da zarto wajen yanke ƙafar wani mutum da ya gini ya tokare shi a ƙasan wata dirka.

"Yana ta ihu!" a cewar Emmanuel, wanda jikinsa ke ɓari a lokacin wannan hira. Ba shi da tabbaci a kan ko mutumin ya tsira.

"Na ga ɗumbin abubuwan da suka ɗimauta ni… an talitse fuskokin mutane," in ji Michael, wani almajirin malamin wanda ke da sauran ƙuruciya a lokacin da bala'in ya faru.

Ba a taɓa wallafa bayanan shaidu na game da miyagun abubuwan da suka faru bayan rugujewar ginin ba kafin wannan lokaci, yayin da makusantan cocin na ciki-ciki suka rantse a kan za su rufa asiri, kuma aka gina ƙatuwar ganuwa don kare wurin daga idon mutane.

Majiyoyi guda uku, ciki har da Michael, sun ce TB Joshua ya ba da umarni ga ma'aikatansa su kawar da tsibin gawawwakin daga ginin da ya rushe da daddare, don ɓoye su daga 'yan jarida da kuma hukumomi.

A National Emergency Management Authority spokesperson speaks at the scene of the collapsed church guesthouse of the Synagogue Church of All Nations in Lagos, Nigeria - 17 September 2014.

Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPEI

Bayanan hoto, An ba da rahotannin cewa an tarewa ma'aikatan agaji hanyar shiga wurin rugujewar ginin tsawon sa'a 24

Biyu daga ciki sun ce an nemi su ɗauki bidiyon al'amarin da ke faruwa, kuma su kai faifan da suka naɗa ofishin TB Joshua.

"Mun riƙa naɗar bidiyon su lokacin da suke zuba su a cikin jakunkunan sanya gawa… mutane tsibi-tsibi," Michael ya ce.

Chloe, ita ma wata tsohuwar ɗalibar limamin coci TB Joshua daga Birtaniya, ita ma ta shaida abubuwan da suka faru bayan rusau ɗin. Ta ce ta shiga cikin motar bas kuma nan da nan ta lura da wani irin ɗoyi mai tayar da hankali.

Direban ya faɗa mata cewa motar na "cike da gawawwaki… kuma za mu tafi da su ne cikin dare saboda kada 'yan jarida su gani".

Ɗumbin majiyoyi sun yi imanin cewa yawan waɗanda suka mutu ya fi mutum 116 da cocin ta bayar, inda suka buga hujja da abokai da kuma ma'aikatan cocin da suke ciki a lokacin rugujewar, waɗanda suka ce ba a sanya cikin lissafin hukuma na mamatan ba.

Da farko hukumomin Najeriya sun ɗauki tsattsauran mataki a kan bala'in da ya faru. Mai binciken sanadin mutuwa na Lagos ya ba da shawarar cewa a tuhumi TB Joshua da laifin aikata sakaci.

Duk da ɗumbin sammacin da aka gabatar, malamin cocin bai taɓa zuwa kotu ba.

Wasu tsoffin ɗalibansa sun ce ya yi ta zazzaga ruwan kuɗi ga mutanen da ke da tasiri a shari'a. Wannan ya ƙunshi dubban dalolin Amurka da kuɗaɗen Afirka ta Kudu rand da kuma nairorin Najeriya ga iyalan waɗanda suka mutu a rushewar ginin, daga ciki 85 'yan Afirka ta Kudu.

Sihle, wata tsohuwar ɗalibar TB Joshua, ta faɗa wa BBC cewa an ba ta wannan aiki a Afirka ta Kudu domin ta "je ta ba da kuɗi, jakunkunan kuɗi" ga waɗanda suka rasa danginsu.

"Za mu faɗa musu cewa kada su kuskura su yi magana da 'yan jarida, kuma kada su sake su ba da rahoto ko wani abu mai kama da haka. Alal haƙiƙa dai, muna rufe musu baki," ta ce.

A framed photo of Llwandle Mkhulisi's sister Pumzile
Bayanan hoto, Ɗan Afirka ta Kudu Llwandle Mkhulisi ya nanata cewa an ba shi abin da ya kira "kuɗin jinin" 'yar'uwarsa Pumzile, wadda ta rasu a rushewar ginin

Dangi uku a Afirka ta Kudu sun tabbatarwa da BBC cewa wakilan cocin sun yi ƙoƙarin ba su kuɗi kuma su hana su yin magana da 'yan jarida.

Llwandle Mkhulisi, daga Johannesburg, wanda ya rasa 'yar'uwarsa Pumzile a bala'in, ya bayyana lamarin da "kuɗin jini" kuma ya ƙi karɓa.

Bayan karɓar kyautar farko ta rand 50,000 daga cocin, Sonny Madzhiye daga yankin Benoni a kusa birnin Johannesburg ta ce ta ƙi karɓar bandiran kuɗin da aka kawo mata daga bisani saboda mutuwar matashiyar 'yarta Sibongile.

Ta ce ta fara fahimtar cewa ana ba ta kuɗaɗen ne don kada ta ɗauki ƙarin wani mataki. TB Joshua ya riƙa razana ta da kiraye-kirayen waya bayan ta ƙi karɓar kuɗi kuma ya yi mata barazana: "Ya turo min waɗannan saƙonni. Suna cewa: 'Idan ka mayar da hankali a kan abin da ka rasa, kana iya rasa komai.'

"Yanzu yana yi min barazana, cewa illahirin iyalaina za su tafi, kamar yadda 'yata ta salwanta."

Ta nuna waɗannan saƙonni da kuma muryar da ta naɗa ta wani kiran waya daga TB Joshua ga BBC.

Misis Madzhiye daga bisani ta yi yunƙuri, ta maka cocin Scoan ƙara a gaban kotun Najeriya, inda take neman diyya kan rasuwar ɗiyarta. Yanzu haka, ana ci gaba da shari'ar.

Sihle ta ce an kuma bai wa 'yan jarida toshiyar baki bayan faruwar bala'in, don yin tasiri a rahotanninsu.

"Mukan samu 'yan jarida da ke zuwa cocin a kan wani abu ko wancan, sai dai sukan tafi riƙe da ambulan… zai ba su daloli," in ji ta.

Chloe, wadda ta yi aiki a sashen labarai na cocin TB Joshua, ta tabbatar da haka ga ɗumbin 'yan jarida a lokacin. Wannan ma, wasu 'yan jarida biyu da suka zanta da BBC da kuma ƙungiyar Open Democracy - abokiyar ƙawance a wannan bincike, sun tabbatar da haka.

A wani saƙon murya da ɗan jaridan Najeriya Nicholas Ibekwe ya naɗa a watan Satumban 2014, ana iya jin TB Joshua ƙarara yana cewa: "To yanzu me za ku rubuta a kai?" bayan gabatar wa da 'yan jarida ambulan cike da kuɗi. Ibekwe dai ya ƙi karɓa.

Sonny Madzhiye
Bayanan hoto, Sonny Madzhiye ta ce har yanzu tana jiran a yi mata adalci dangane da mutuwar 'yarta

Emmanuel da Michael, waɗanda kowannensu ya shafe sama da shekara 20 a cocin, sun ce TB Joshua ya ba su umarni, su sanya ambulan ɗin kuɗi a motocin 'yan siyasa da kuma jami'an kotu na Najeriya a lokacin binciken sanadin mutuwa a Lagos.

"Ya lulluɓe komai," a cewar Emmanuel. "Ya sayi gaba ɗaya al'amura a gwamnati."

TB Joshua ya rasu cikin watan Yunin 2021, yana da shekara 57, amma har yanzu matarsa Evelyn tana ci gaba da gudanar da ita.

Da BBC ta tuntuɓi shugabannin cocin na yanzu a kan bala'in da kuma zarge-zargen fyaɗe da azabtarwa da TB Joshua ya riƙa aikatawa a cikin gidansa da ke Lagos, sun amsa da cewa: "Zarge-zarge marasa tushe a kan Babban Liman TB Joshua ba sabon abu ba ne.

"Babu ko ɗaya daga cikin irin waɗannan zarge-zarge da aka taɓa tabbatarwa."