BBC ta bankaɗo yadda TB Joshua ya riƙa yi wa mabiya fyaɗe a cocinsa

TB Joshua

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, TB Joshua ne ya kafa shahararriyar cocin Synagogue Church of all Nations
    • Marubuci, Charlie Northcott and Helen Spooner
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Africa Eye

BBC ta bankaɗo hujjojin da ke tabbatar da yadda ɗaya daga cikin shugabannin coci mafiya girma ya azabtar da kuma cin zarafin mabiyansa.

Gomman mambobin cocin Synagogue Church of all Nations - biyar daga cikinsu 'yan Birtaniya - sun zargi fasto ɗan Najeriya, TB Joshua, da cin zarafinsu ta hanyar fyaɗe, da tilasta musu zubar da ciki.

Zarge-zargen da aka yi sun ce an shafe kusan shekara 20 ana aikata su a wani gida da ke Legas.

Cocin Synagogue Church of All Nations ba ta mayar da martani ba game da zargin amma ta taɓa musanta waɗanda aka yi a baya, cewa ba su da tushe.

Abin da BBC ta gano a binciken da ta yi tsawon shekara biyu sun ƙunshi:

  • Gomman shaidun gani da ido da suka bayyana yadda Joshua ya azabtar da mutane, wani zubin ma har da yara, ta hanyar ɗaure su da kuma yi musu bulala
  • Mata da yawa da suka ce Joshua ya yi lalata da su, inda da yawansu suka yi iƙirarin cewa an shafe tsawon shekaru ana yi musu fyaɗe a gidan
  • Zarge-zarge iri-iri game da tilasta zubar da ciki a cikin cocin baya ga zargin fyaɗen, inda wata mace ta ce an zubar mata da ciki har sau biyar
  • Labarai iri-iri game da ke bayyana yadda Fasto Joshua ya dinga ƙirƙirar "warkar da mutane da karamominsa", wanda aka dinga yaɗawa ta kafofin yaɗa labarai ga miliyoyin masu kallo a faɗin duniya

Ɗaya daga cikin matan, 'yar Birtaniya da ake kira rae, tana da shekara 21 lokacin da ta jingine karatunta na digiri a Jami'ar Brighton a shekarar 2002, kuma aka yi mata rahista a cocin. Ta shafe shekara 12 a matsayin waɗanda ake kira "hadiman" Joshua a gidan nasa da ke Legas mai kama da zubin masara da aka gina da kankare.

"Dukkanmu mun zaci a aljanna muke, ashe a wuta muke, kuma a wuta ne munanan abubuwan ke faruwa," kamar yadda ta faɗa wa BBC.

Bayanan bidiyo, Bidiyo: Zargin lalatar da wasu mabiya ke yi wa TB Joshua

Rae ta ce Joshua ya yi lalata da ita kuma ya tilasta mata zaman kaɗaici na shekara biyu. Lalatar har ta yi yawan da ta yi yunƙurin kashe kanta ba sau ɗaya ba a gidan, in ji ta.

Cocin Synagogue Church of All Nations [Scoan] na da mabiya a faɗin duniya, inda suke gudanar da gidan talabijin na Emmanuel TV da shafukan sada zumunta masu miliyoyin mabiya.

Kusan baki ɗayan shekara 1990 zuwa 2000, dubban mutane sun sha yin balaguro daga Turai, da Amurka, da Kudancin Asiya, da Afirka zuwa Legas don su ga Joshua yana "yana ba da magani da karamarsa".

Mutum aƙalla 150 ne suka zauna tare da shi a gidan na Legas a matsayin hadimansa, wasu ma sun shafe sama da shekara 10.

Rae ta zauna tsawon shekara 12 a gidan Joshua
Bayanan hoto, Rae ta zauna tsawon shekara 12 a gidan Joshua
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Hadimai" fiye da 25 ne suka yi magana da BBC - daga Birtaniya, da Najeriya, da Amurka, da Afirka ta Kudu, da Namibia, da Jamus - suna masu bayyana labaran abubuwan da suka fuskanta a cocin.

Da yawan mutanen na cikin shekarun ƙuruciyarsu lokacin da suka shiga cocin.

Joshua ne ya ɗauki nauyin wasu daga cikin masu zuwa wajensa daga Birtaniya ta hanyar haɗin gwiwa da wasu coci-cocin.

Rae da wasu sun ce kamar ƙungiyar asiri haka cocin take.

Jessica Kaimu daga Namibia ta ce ta sha fama tsawon shekara biyar. Ta ce tana shekara 17 lokacin da Joshua ya fara yi mata fyaɗe kuma fyaɗen da ya dinga yi mata daga baya ya sa dole ta zubar da ciki har sau biyar lokacin da take cocin.

"Ta bayan fage ake yin al'amuran...irin magungunan da likitoci suka dinga ba mu...za su iya kashe mu," in ji ta.

Wasu suka ce an cire musu kaya kuma aka zane su da wayoyin lantarki da bulalar dukan doki, kuma aka dinga hana su barci.

Bayan rasuwarsa a watan Yunin 2021, an yabi TB Joshua a matsayin ɗaya daga cikin fasto mafiya tasiri a tarihin Afirka baki ɗaya. Akwai ɗumbin 'yan siyasa, da shahararrun mutane, da 'yan ƙwallon ƙasashen duniya a cikin mabiyan cocinsa ta ɗariƙar evengilism.

Sai dai ya jawo cecekuce a lokacin rayuwarsa lokacin da ginin gidansa ya rikito a 2014, inda ya kashe mutum 116.

Binciken na BBC tare da haɗin gwiwar kafar yaɗa labarai ta Open Democracy, shi ne karon farko da tsofaffin mambobin cocin suka fito fili suka yi magana. Sun ce sun daɗe suna yunƙurin fallasawa amma kuma aka hana su.

Wasu daga cikin mutanen a Najeriya sun ce an kai musu hari, an harbi wasu ma, bayan sun yi magana game da cin zarafin da kuma wallafa bidiyo a dandalin YouTube kan hakan.

Tawagar BBC da ta yi yunƙurin ɗaukar bidiyon gidan cocin na Legas a watan Maris na 2022 ta fuskanci harbi daga wani mai gadin wurin, kuma aka tsare su tsawon lokaci.

BBC ta tuntuɓi Scoan game da zarge-zargen da aka yi a binciken. Ba ta bayar da amsa ba, amma ta taɓa musanta wani zargin da aka yi wa TB Joshua.

"Yin zarge-zarge marasa tushe a kan TB Joshua ba sabon abu ba ne...ba a taɓa tabbatar da gaskiyar ko ɗaya daga cikinsu ba," in ji cocin.

Wasu 'yan Birtaniya huɗu da suka yi magana da BBC sun ce sun kai ƙara zuwa hukumomin ƙasar bayan sun fice daga cocin. Sun ce ba a ɗauki wani mataki ba.

Anneka ta ce har yanzu akwai wasu mutanen da ba su faɗi nasu cin zarafin da aka yi musu ba
Bayanan hoto, Anneka ta ce har yanzu akwai wasu mutanen da ba su faɗi nasu cin zarafin da aka yi musu ba

Bugu da ƙari, wani ɗan Birtaniya da matarsa sun rubuto saƙon imel ɗauke da nasu labarin - har da bidiyon da suka naɗa lokacin da wasu suka tsare su da bindiga suna cewa 'yan sanda ne kuma mambobin cocin Scoan - zuwa ofishin jakadancin Birtaniya a Najeriya a watan Maris na 2010.

Mutumin ya ce an yi ta lalata da matarsa kuma Joshua ya yi mata fyaɗe. Ya gargaɗi ofishin cewa har a lokacin akwai 'yan Birtaniya da ke cikin gidan kuma suke fuskantar lalata.

Ya ce ba a ɗauki wani mataki ba.

Ofishin Harkokin Wajen Birtaniya bai ba da amsa ba kan zarge-zargen, amma ya faɗa wa BBC cewa yana ɗaukar kowane rahoton aikata laifi, ciki har da na lalata da kuma zalintar 'yan Birtaniya a ƙasashen waje, da muhimmanci.

Har yanzu Scoan na aiki a ƙarƙashin jagorancin bazawarar Joshua mai suna Evelyn. A watan Yulin 2023, ta jagoranci balaguron buɗe-ido zuwa Sifaniya.

Anneka, wadda ta bar Derby a Birtaniya kuma ta koma Scoan tana shekara 17 da haihuwa, ta faɗa wa BBC har yanzu akwai mutanen da ba su bayyana halin da suka shiga ba a hannun Joshua.

"Na tabbata akwai buƙatar a bincika Synagogue Church of All Nations da kyau don gano dalilin da ya sa wannan mutumin ya shafe lokaci yana aikata abin da ya yi," a cewarta.

Akwai gudummawar Maggie Andresen, da Yemisi Adegoke, da Ines Ward a wannan rahoton