Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hukumar NDLEA ta kama dubban kwalaben 'A-Kurkura'
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta ce ta kai samfurin A-kurkura, wani hade-haden ruwan saiwowi da wasu abubuwa da ke tashe musamman a arewacin Najeriya zuwa dakin gwaje-gwaje don tantance irin illar da yake yi wa masu ta'ammali da shi.
Hukumar ta NDLEA ta bayyana hakan ne bayan wani gagarumin kame na dubban kwalaben ruwan na A-kurkura da ƙarin wasu miyagun ƙwayoyi a Jihar Kaduna, wadanda ta ce an yi niyyar safararsu zuwa wasu jihohin arewacin Najeriya.
Hukumar ta ce ta kama nau’i daban-daban na miyagun kayan maye sama da miliyan biyu a jihohin Kaduna da Kogi da Sokoto da kuma birnin Tarayya Abuja.
Cikin kayan mayen har da maganin nan na A-kurkura wanda kan jefa mutumin da ya yi amfani da shi a karon farko cikin wani mawuyacin hali, wanda za a ga mutum kamar zai mutu, yana amai yana shure-shure.
Mutane da dama na amfani da shi a matsayin wani hadi da su kan ce yana sa su ji garau ko caji.
A tattaunawarsa da BBC kwamandan hukumar ta NDLEA na Jihar Kaduna Umar Isa Adoro ya ce kwalabe 67,353 suka kama.
Kuma wannan shi ne adadi mafi yawa da aka kama a jihar ta Kaduna tare da dubban miyagun kwayoyi.
Ya ce daga cikin kwalaben kayayyakin da suka kama, akwai sama da 7,000 na A-kurkura.
Shugaban ya yi karin bayani da cewa, ''A-kurkura wato jike-jike ne hade-hade ne suke yi suka harhada kuma ake ta saidawa yanzu saboda yanzu kwayoyi da kuma abin nan hukumar Najeriya ta tashi tsaye wajen yaki, to muna ganin shi suke so ya maye hanyoyi na amfani da miyagun kwayoyi.''
''Duk mutum idan ya sha ''First timer'' (wanda ya fara sha a karon farko), suna ce yana magani dari ba daya, suna cewa duk kusan magunguna na duniya yana maganinsu, amma in mutum ya sha za ka ka ya fadi kasa, yana ta amai ana ta fama da shi kuma kawai kuskurawa din da ya yi ya zubar kenan,'' in ji Kwamandan.
A baya-bayan nan dai, an yi ta yada hotunan bidiyon wadanda suka yi amfani da A-kurkura suna murkususu a kasa.
Haka kuma Kwamanda Umar ya ce sun kama dubban kwayoyin da ke haddasa maye da kuma illa ga jikin bil-Adama.
NDLEA ta ce ruwan hade-haden na A-kurkura an yi yunkurin kai shi wasu jihohin arewacin Najeriya ne, sai dubun masu safarar ta cika a Kaduna.
Hukumar NDLEA ta kama fiye da mutum 50 wadanda ake zargi da hannu wajen safarar A-kurkuran, wadanda ta ce za ta gurfanar da su a kotu, sai dai hukumar ba ta yi karin haske ba game da lokacin da za ta yi hakan.