Mun ɗaura ɗamarar kare rayukan al'umma a yayin bukukuwan ƙarshen shekara - FRSC

Jami'an hukumar kiyaye afkuwar hadura ta Najeriya FRSC

Asalin hoton, Twitter/FRSC Twitter

Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da ake tunkarar ƙarshen shekara da shigowar sabuwar shekara, hukumar kiyaye haɗura ta Najeriya, wato FRSC ta ce ta ƙara ɗaura ɗamara, domin gudanar da ayyukan kula da zirga-zirgar ababen hawa a wannan lokaci da jama'a ke hada-hadar tafiye-tafiye.

Shugaban hukumar na kasa, Shehu Muhammed, ya shaida wa BBC cewa, sun yi wannan shiri ne domin shawo kan aukuwar hadura da sauran gaggan matsalolin da ake fuskanta a manyan hanyoyin kasar.

Ya ce," A watanni uku na karshen shekara da kuma watan farko na kowacce shekara ana samun karuwar zirga-zirgar Ababan hawa da kuma tafiye-tafiye, ba don komai bas ai saboda bukukuwan kirsimeti dana sabuwar shekara."

"To a irin wannan lokaci hukumarmu kan kara yawan abubuwan da ta ke yi, kamar misali mu kan kawo dukkan ma'aikatanmu da kuma masu farin kaya da ake kira "Special Marshal", sai mu zuba su a kan hanya gaba daya don ya kasance an samu ganinmu a hanya musamman manyan hanyoyi."In ji shi.

Shehu Muhammed, ya ce,"Za a ga ana samun cunkoson ababan hanya a irin wannan lokaci to ba wani ke janyo shi ba illa aikin hanyoyi da ake yi kusan a ko ina a shiyoyin kasar nan, masu aikin hanyar kan toshe hanyoyi sai ka ga an koma ana bin hanya guda maimakon hanya biyu, to duk irin wannan shi ke kawo cunkoson Ababan hawa musamman a lokacin bukukuwan karshen shekara."

Ya ce,"Irin wannan aikin hanya da ake yi musamman a manyan hanyoyi na sanya aikinmu ya zamo mai wahala saboda hanyoyi sun ragu, amma motoci sun karu, saboda haka zaka ga idan muna sa mutum 10 a kan hanyar a lokacin da ba na karshen shekara ba, to idan lokacin ya zo sai mun sanya mutum 30."

Shugaban hukumar kiyaye afkuwar haduran ta Najeriya y ace," Abin da muke yi shi ne idan ya rage saura kamar makonni biyu a fara bukukuwan karshen shekarar mu kan sanar da kamfanonin da ke aikin hanyoyin akan su bude hanyoyin da suka kammala ko da kuwa ba su gama gabaki day aba, saboda mutane da motoci sus amu saukin wucewa ta hanyoyin."

Ya ce," Kuma yanzu haka ma kamfanonin sun bamu tabbaci akan za su yi abin da muka bukata don saukakawa mutane, saboda suma kamfanonin su kan tafi hutu a irin wannan lokacin."

Shehu Muhammed, ya ce, "Dangane da batun sanya alamomi a kan hanya kuwa, dama mu kan samu gudunmuwa daga kamfanoni musamman wadanda ke aikin hanya, su kan tuntubemu su ce mana to muna aiki a kan hanyar kaza, don haka a ina ya kamata mu sanya alamar ana aikin hanya, ko kuma sauran alamomin saboda masu tuki, sai mu basu shawara mu ce ga yadda za a yi, to yanzu haka ma kusan akwai alamomin hanyar da aka sanya a hanyoyi da dama."

Ya ce," Baya ga alamomin hanya, muna kan yi amfani da wasu abubuwa ma masu haske saboda masu tukin dare don su gane ga alamar ana aiki a gaban hanyar da suke bi, sannan ga ma'aikatanmu ma da ake aiki cikin dare a irin wadannan hanyoyi don su taimakawa masu bin hanyar."