Yadda direbobi da ke shan barasa ke jefa rayuwar fasinjoji cikin hadari a Najeriya

Matafiya a Najeriya sun bayyana damuwarsu a kan yadda ake sayar da barasa a tashoshin mota.
Bincike ya nuna ana sayar da karamin kunshin giyar cikin leda daban-daban ko kuma a cikin ‘yar karamar kwalba a tashoshin mota musamman a jihar Legas da ke kudancin kasar.
Matafiyan sun ce an samun wasu direbobin da kan sayi barasa su sha kafin su tuka mota abin da ke jafa rayuwarsu cikin hadari.
A wasu lokuta a kan samu hadarin mota wanda ke da nasaba da barasar da direba kan sha kan ya fara tuka mota.
Wani fasinja da ba a bayyana sunansa ba ya shaida wa BBC cewa, idan har ya ga direban da ya shiga mota ya sha barasar da ta nemi ta fitar da hankalinsa to ko ya shiga motar sai ya fita don neman tsira da rayuwarsa.
Ita ma wata mata ta bayyana cewa,”Ta ce gaskiya ya kamata a samu mutanen da za su rinka bin tasha-tasha don ganin cewa ba a sayar da barasa a tasha, don bai kamata a ce ana sayar da barasa a tashar mota ba.”
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shi ma wani fasinjan ya ce yana ganin shan barasa a lokacin da mutum zai tuka mota sam ba abu ne mai kyau ba, don yawanci abin da ke biyo baya hadari ne, wanda kuma ba direba kawai zai shafa ba har fasinjan motar.
A farkon shekarar 2022 ne hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya ta hana sayar da barasa kunshi cikin kanana fakiti da kwalabe a tashoshin mota.
Ita ma gwamnatin jihar Legas, a kwanakin baya ta haramta sayar da barasa a wuraren shakatawa da tashoshin mota.
Ita dai wannan barasa ana sayar da ita ne a cikin kananan fakiti da kwalabe hakan ne yasa ta ke samun karbuwa daga wajen masu ta’ammali da ita.
Yawancin direbobi da sauran mutane na adana barasar a cikin motocinsu saboda tafiye-tafiye.
Wasu alkaluma daga hukumar kididdiga ta Najeriya ta fitar a 2021, na cewa an samu mutum akalla 6,205 da suka mutu sakamakon hadarin mota.
Ita ma hukumar kiyaye afkuwar hadura ta Najeriyar ta ce kashi 90 cikin 100 na hadurran da ke faruwa a kan titunan Najeriya na faruwa ne a sanadiyyar shaye -shayen barasa da sauran abubuwan da ke sanya maye.











