Pogba ya matsar da kwalbar barasa daga gabansa

Asalin hoton, Getty Images
Dan kwallon tawagar Faransa, Paul Pogba ya matsar da kwalbar barasa ta Heineken daga gabansa a lokacin da zai gana da 'yan jarida a gasar Euro 2020 ranar Talata.
Hakan ya biyo bayan kwana daya tsakani da Cristiano Ronaldo ya janye kwalaben da ke dauke da Coca Cola daga gabansa kana san Hungary da Portugal.
Pogba wanda Musulmi ne ya matsar da barasar daga gabansa a lokacin da zai zauna don amsa tambayoyin 'yan jarida, bayan da aka bayyana shi fitattcen dan wasa a karawa da Jamus.
Tawagar kwallon kafa ta Faransa ta yi nasarar doke ta Jamus a wasan farko na rukuni na shida da suka fafata ranar Talata.
Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya tuntubi Heineken, daya daga cikin kamfanonin da ke daukar gasar cin kofin nahiyar Turai da ake yi.
Ranar Litinin Ronaldo ya matsar da kwalabe biyu da ke dauke da Coca Cola ya kuma dauki roba mai dauke da ruwan sha ya ce ''Agua'' da harshen Portugal






