Ana zargin bam ya tashi a mashaya a Jihar Kogi

Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba

Asalin hoton, Other

Rahotanni daga garin Kabba da ke Karamar Hukumar Kabbah-Bunu a Jihar Kogi ta arewa maso tsakiyar Najeriya na cewa wani abu da ake zargi bam ne ya fashe a wata mashaya.

Sai dai bayanan farko-farko kan lamarin da ya faru da misalin karfe tara da minti 15 na dare ranar Lahadi, na nuna cewa ba mutumin da ya rasa ransa a fashewar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP William Ovye-Aya wanda ya tabbatar wa da BBC fashewar, ya ce ba su kai ga tantance ainahin abin da ya fashe ba.

Ya ce lamarin wanda ya faru a wata mashaya ta Omofemi a unguwar Okepadi, da ke garin na Kabba, ya yi sanadiyyar lalacewar gini da kujeru da kuma tebura a wurin.

'Yan-sandan Najeriya

Asalin hoton, Other

Kakakin ya kara da cewa, tuni kwamishinan 'yan-sandan jihar Mista Edward Egbuka ya bayar da umarnin tura kwararru a kan bam, su je wurin domin su gano abin da ya fashe da kuma irin illar da aka samu.

Wannan ba shi ne karon farko ba da ake samun fashewa a wuraren shan barasa a garin na Kaba, inda ko a ranar 11 ga watan Mayu na 2022, wani bam ya tashi a yayin da ake bushasha a wani gidan giya a garin.

Fashewar wadda ta auku da misalin karfe goma saura kwata na dare a wancan lokacin, rahotanni sun ce ta yi sanadiyar mutuwar mutum akalla uku, tare da jikkata wasu da yawa.

Ana samun irin wannan fashewa a wuraren shan barasa da dama a arewacin Najeriya, inda a baya-bayan ta auku a jihohin Yobe da Kaduna.