Me ya sa aka 'kasa' magance rashin tsaro a hanyar Kaduna zuwa Abuja?

Bayanan bidiyo, Me ya sa aka 'kasa' magance rashin tsaro a hanyar Kaduna zuwa Abuja?

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Matsalar garkuwa da mutane da ta ta'azzara a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja tana ci gaba da jan hankulan jama'a.

A karshen makon jiya an kashe wani dan siyasa sanna aka sace mutanen da ba a san adadinsu ba.

Hakan na faruwa ne yayin da hukumomi suke cewa suna bakin kokarinsu wajen kawo karshen matsalar.

Shin yaya za a magance matsalar rashin tsaron da ke addabar hanyar?

Abokiyar aikinmu Badriyya Tijjani Kalarawi ta yi mana nazari kan hakan: