Manhajar hukumar FRSC da za ta nuna muku motocinku da aka sace
Hukumar kiyaye haɗurra ta Najeriya, FRSC ta ce ta fito da wata sabuwar manhaja da masu ababan hawa za su iya amfani da ita wajen sanin al'amuran da suka shafi tuƙi.
Shugaban hukumar, Shehu Muhammad ya shaida wa BBC cewa "lokacin da muka zo mun yi tunanin me za mu yi domin rage yawan haɗurra. Wannan ne ya sa muka fito da wata manhaja wadda za ta zama tamkar jagora ga direbobi."
"Direba zai iya sabunta lasisinsa na mota da sauran su ba tare da ya zo ofishinmu ba. Sannan manhajar na nuna wa direba duk wani abun da zai iya janyo hatsari a kan titi. Misali, idan akwai kwana za ta faɗa maka. Haka ma idan akwai rami a gaban direba to za ta sanar. Haka kuma ita wannan manhaja za ta iya nuna motar da aka sace." In ji Shehu Mohammed.

Asalin hoton, BBC/SCREENSHOT



