Abin da ya sa ziyarar Biden a Gabas ta Tsakiya ta jawo ce-ce-ku-ce

Activist

Asalin hoton, MANDEL NGAN

Kwana guda bayan sanarwar da fadar White House ta fitar cewa Shugaba Joe Biden zai kai ziyara kasar Saudiyya, wasu masu gwagwarmaya sun taru a gaban ofishin jakadancin Saudiyya da ke Washington a kan titin ''Khashoggi'' rike da kwalaye.

Sun ce ya zama tilas a rika tuna wa jami'an diflomasiyya da ke ofishin a kulli yaumin cewa gwamnatin Saudiyya na da hannu a kisan dan jaridar kasar Jamal Khashoggi.

'Yan gwagwarmayar sun yi Alla-wadai da matakin Shugaba Biden na ganawa da mutumin da Amurka ta ce da hannunsa a kisan dan jaridar - Yerima Mohammed bin Salman, da aka fi sani da MBS.

"Idan gaskiya za a fada da kuma fito da ita a fili, shin za ka iya tambayar cewa ina gawar Jamal? Bai kai a yi masa jana'iza da ta kamata ba ne?", tambayar da Hatice Cengiz, budurwar Khashoggi, ta yi ke nan.

Me ya sa ziyarar ta jawo ce-ce-ku-ce ?

Dangantaka tsakanin Amurka da Saudiyya ta shekara-da-shekaru ta fi ta'allaka ne kan harkokin kasuwanci da kuma wasu bukatu na kashin kansu.

Sai dai Shugaba Biden ya sha nanata muhimmancin kare hakkin dan adam a cikin dangantakar kasashen, a yanzu , yayin da yake karkata ga hakikanin harkokin siyasar da ke zayyana ta, yana fuskantar kasadar rasa kwarin gwuiwa kan tsarinsa game da manufofinsa kan kasashen ketare.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kisan gillar da aka yi wa Khashoggi ya raba kan bangarori da dama a Washington. Khashoggi, wanda dan jarida ne kuma mai sukar Yarima mai jiran gado, an kashe shi tare da yin gunduwa-gunduwa da gawarsa a karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Isatanbul.

A matsayinsa na dan takarar shugaban kasa, Mr Biden ya yi alwashin daukar mataki kan masarautar Saudiyya saboda ayyukanta na keta haƙƙin ɗan adam.

Ya yi amfani da kalaman wajen bambanta kansa da irin rungumar da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya yi wa Saudiyya. Mr Trump ya taba ikirarin cewa ya ceci Yarima bin Salman daga dambarwar mutuwar Khashoggi.

Me ya kawo sauyawar al'amura?

Lokacin da ya hau karagar mulki, Mr Biden ya dakatar da sayar da makamai ga Saudiyya sannan ya kuma ki yin magana da Yarima bin Salman. Amma akwai shakku a gwamnatin cewa ko hakan zai dore kan mutumin da nan ba da jimawa zai zama mai mulkin Saudiyya. Al'amura sun ci gaba da wakana a tsawon shekarar da ta gabata, inda yaki tsakanin Rasha da Ukraine ya sanya shugaban na Amurka fitowa fili domin sanya baki.

Tashin farashin man fetur shi ne ya jawo sauyawar al'amura. Amurka ta bukaci Saudiyya da ta samar da karin man fetur domin taimakawa wajen sauko da farashin. Riyadh dai ba ta amince da bukatar ba a farko.

Sai dai kwanaki kafin sanar da ziyarar Shugaba Biden, kamfanin Opec Plus, da ke samar wa Saudiyya mai ko da yake ita ke da iko da kamfanin, ya amince da bukatar kara yawan mai da yake samarwa.

Masu sharhi sun ce akwai kuma wata yarjejeniya da Saudiyya ta kara yawan man da kasar ke fitarwa da zarar yarjejeniyar da ke aiki a yanzu ta kare a watan Satumba. Amma da wuya a tattauna kan batun a ziyarar.

Abin da ziyarar Mr Biden za ta fi mayar da hankali a kai shi ne ganin an ci gaba da samar da makamashi a kasuwannin duniya musamman ma a wannan mayuwacin hali da ake ciki, a cewar Ben Cahill, wani masani kan harkar makamashi a Cibiyar Dabaru da Nazarin Ƙasashen Duniya (CSIS).

"Ina ganin akwai ma'ana a maganar fadar White House cewa suna bukatar samun damar amma kiran waya da kuma tattaunawa mai ma'ana da jami'ai da dama da kuma kasashe masu samar da man fetur inda za su fara da Saudiyya," in ji shi.

Me yake fatan cimmawa?

Idan har ziyarar ba za ta yi tasiri na nan take ba ga tashar samar da gas din Amurka, wane sakamako za ta haifar?

Mr Biden bai nuna wani muhimmanci da ganawar sa za ta yi da MBS ba, inda ya nanata cewa zai halarci taron kasashen Larabawa ne a Jeddah, taro kuma da shi Yarima bin Salman zai kasance a wajen.

Biden

Asalin hoton, JACK GUEZ

Ya kare matakinsa na cewa wani bangare na tafiyarsa na kan bukatar Isra'ila. Ya jaddada ziyarar tasa ta hanyar nanata muhimmancin hada kai da Isra'ila a yankin.

Ana kuma ganin cewa wani babban bangare na ziyarar tasa ita ce ta ganin an daidaita huldar dangantaka tsakanin Isra'ila da Saudiyya, musamman ma ta fuskar tsaron kasashen larabawan da Isra'ila.

Batun shi ne ta hada tare da karfafa tsarin tsaro ta sama domin dakile barazanar hare-haren makamai masu linzami daga Iran da kawayenta.

Shirin ya samu karbuwa idan aka yi la'akari da kokarin da Amurka ta yi na farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran, shirin nukiliyar Iran farfadowa cikin sauri, da kuma karuwar hare-haren makamai masu linzami na 'yan tawayen Houthi daga Yemen.

Paul Pillar na Cibiyar Quincy Institute for Responsible Statecraft ya kira tsarin da "ƙawancen soji da Iran".

''Dukkanin tsarin ya dogara ne, daga mahangar Isra'ila, amma kuma daga mahangar Larabawan Fasha, kan gaba da Iran," in ji shi.

Sai dai, ba sa saran cimma matsaya a tattaunawar. Saudiyya dai na hada kai a boye da Isra'ila, amma ta ja baya daga ba tare da wani yunkuri na warware rikicin Falasdinu ba.

Akwai wasu ƙananan matakai ko da yake: Saudiyya ta faɗaɗa zirga-zirgar jiragen sama na Isra'ila a cikin sararin samaniyarta. Ana kuma sa ran zata amince da zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye ga musulmi mahajjata daga Isra'ila, da kuma ba da tabbacin yin jigilan jiragen ruwa na Isra'ila a tsibiran biyu na cikin Tekun Bahar Maliya daga Masar.

Yaya batun tabarbarewar siyasa ?

A Amurka, hankali zai koma kan tattaunawar Mr Biden da Yerima mai jiran gadon sarautar Saudiyya. Shugaban yana da shakku a al'ummar ta kare hakkin bil'adama, amma kuma shawarar da ya yanke za ta iya rage tagomashin da yake da ita a siyasa a cikin jam'iyyarsa ta Democratic.

Dukkan su suna jayayya cewa hanya daya tilo da zai iya mayar da tafiyar zuwa ga nasara ita ce ta bijiro da al'amuran 'yancin ɗan adam.

Suna kira gare shi da ya matsa lamba don a saki fursunonin siyasa da kuma dage takunkumin tafiye-tafiye da sauran takunkuman da aka yi wa masu fafutuka.

Suna kuma son ya fito fili ya maimaita bukatar ganin an hukunta wadanda suka kashe Khashoggi.

Kuma a wata wasika ta hadin gwuiwar shugabannin kwamitocin majalisar guda shida, sun yi kira ga shugaban kasar da ya dakatar da taimakon fadan da kawancen Saudiyya ke jagoranta a Yemen.

A kan wannan yakin, Masarautar ta daidaita matsayinta, inda ta amince da tsagaita bude wuta da Majalisar Dinkin Duniya ta cimma a bana, tare da kara tattaunawa da 'yan tawayen Houthi na Yemen.

Mista Biden ya yaba wa wannan yunƙuri, inda kuma ya ce yana fatan ganin an samu zaman lafiya.

Me Saudiyya ke so?

Hasali ma, MBS, wanda ke dora alhakin kisan Khashoggi kan jami’an tsaronsa, ya biya wa Amurka bukatu da dama , kuma yana son ta ba shi ta hanyar sake farfado da dangantaka, farawa da yarjejeniyar tsaro mai karfi tsakanin kasashen biyu.

Har ila yau Saudiyya na son a fayyace manufar mista Biden, in ji Jonathan Panikoff, wani tsohon jami'in leken asiri na kasa, da a yanzu ke aiki da kungiyar Atlantic Council."

Ba wai shugaban ya zo kan mulki ne ba domin ya canza dangantakar su da Saudiyya. Ya kasance tsawon watanni 18 da suka gabata ba a san inda dangantakar za ta je ba," in ji shi.

Rashin fayyace manufar Amurkan na da shakku a cikin mutane da yawa… kawai sakon shi ne : eh za mu zama abokan juna gare ku ko a'a, ba za mu zama abokan juna ba.

Saudiyya na kallon ziyarar a matsayin "sake wa da kuma tabbatar da hakan ta yadda hakan zai nuna cewa ba za a yi watsi da masarautar ba," in ji Ali Shehabi, marubuci kuma mai sharhi wanda ke da tarihin paputukar bayyana manufofin Yerima bin Salman a Washington.

Yana yin abin da Trump ya yi ne?

Mista Biden ya yi kokarin kawar da ra'ayin cewa duk da ikirarin da ya yi na kare dimokradiyya da kare hakkin dan Adam, manufofinsa na Gabas ta Tsakiya ba su da bambanci da na magabacinsa.

Trump and MBS

Asalin hoton, ANADOLU AGENCY

Mun canza tsarin da muka gada," ya rubuta a cikin wani shafi na Washington Post a baya bayan -nan.

Sai dai kuma ya bayyana cewa yakin da ake yi a nahiyar Turai ya taimaka masa wajen sake fasalin manufofinsa kan tsare-tsare na yankin, musamman na Saudiyya.

Masarautar ta karfafa dangantakarta da Rasha da China a lokacin da Biden baya nan, kuma ta jure matsin lambar Amurka na ganin ta dauki muhimman matakai na maida shugaban Rasha Vladimir Putin saniyar ware, wanda yarima mai jiran gado ke da kyakkyawar alaka da shi.

"Dole ne mu mayar wa Rasha martani kan mamayarta, mu sanya kan mu a cikin mafi kyawun wuri don tserewa China, da kuma yin aiki don samar da kwanciyar hankali a wani yanki na duniya," Mista Biden ya rubuta.

"Don yin wadannan abubuwa, dole ne mu yi hulda kai tsaye da kasashen da za su iya yin tasiri ga sakamakon. Saudiyya na daya daga cikinsu."

Wannan ciniki ne na dogon lokaci da ba zai iya haifar da wani ci gaba ba game da mutuwar Jamal Khashoggi. Hadari ga Mista Biden shi ne idan tafiyar sa zuwa Saudiyya za ta haifar da da' mai ido.