Yaushe za a fara bai wa ƙananan hukumomin Najeriya kuɗaɗensu?

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Juma'a ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci gwamnonin ƙasar su yi biyayya ga umarnin kotun ƙoli da ya bai wa ƙananan hukumomi ƴancin tafiyar da kuɗaɗensu.

Shugaban ya yi gargaɗi gwamnonin ne da ba su biyayya ga umarnin su sani cewa za su tilasta masa zartar da wata doka da za ta ba shi ikon aikewa ƙananan hukumomin kuɗaɗensu kai tsaye daga asusun kwamitin rabon arzikin tarayya.

Tinubu ya yi gargaɗin ne a wajen taron majalisar zartarwar jam'iyyar APC karo na 15 a Abuja.

Gargaɗin Tinubu?

Shugaba Tinu wanda ya yi gargaɗin da kakkausan harshe ga gwamnonin ya ce dole ne gwamnatinsa ta tabbatar da bin umarni kotunan ƙasa.

"Kotun ƙoli ta bayar da umarni gare ku, inda ta ce ku bai wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye. Idan kuka ƙi har sai na yi amfani da dokar shugaban ƙasa, domin wuƙa da doya duk suna hannuna, to zan yanke ta.

"Ina matuƙar mutumta ku ne kawai, a matsayin gwamnonina. Amma idan ba ku fara aiwatar da wannan umarni daki-daki ba, za ku ga abin da zai faru,'' in ji Tinubu. .

A ranar 11 ga watan Yulin 2024 kotun ƙoli ta bayar da hukuncin da ya tabbatar da wanda buƙatar gwamnatin tarayya ta bai wa ƙananan hukumomin Najeriya ƴancin tafiyar da kuɗaɗensu.

Dukkan alƙalan kotun bakwai sun amince da hukuncin cewa riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi da gwamnatocin jihohi ke yi ya saɓawa tanadin kundin mulkin ƙasa.

Me ya hana gwamnoni bin umarnin kotu?

Fiye da shekara ɗaya bayan hukuncin na kotun ƙoli, ta bayyana a fili cewa gwamnonin jihohi na hana shugabannin ƙananan hukumomi ƴancin karɓa da kuma tafiyar da kuɗaɗensu.

Kawo yanzu dai babu wani gwamna a Najeriya da ya fito fili ya shadai wa duniya dalilin da ya sa ba sa son bai wa ƙananan hukumomi kuɗaɗen nasu.

Sai dai ƴan gwagwarmaya da masu fafutukar yaƙi da rashawa da cin hanci a Najeriya na ganin cewa gwamnonin ba sa son bin umarnin kotun ne saboda yadda hakan zai shafi ayyukansu.

''Ina ganin kamar su gwamnonin ba su son wannan tsari saboda suna ganin cewa kuɗaɗen ƙananan hukumomin nan ba ƙaramin romo ba ne a gare su, saboda haka za su ci gaba da yin amfani da su,'' kamar yadda Auwal Musa Rafsanjani, shugaban ƙungiyar CISLAC ya shaida wa BBC a kwanakin baya.

To amma wani ɗan gwagwarmaya mai fafutukar ƴancin ɗan'adam, Faruk Musa Muhammad ya ce dalilin da ya sa gwamnoni ke shakkar bai wa ƙananan hukumomi kudaden nasu shi ne tsoron kishiyanta.

"Ba wani abu ba ne yake tsorata gwamnonin nan illa idan ƙananan hukumomi suka samu zarafin tafiyar da harkokinsu to lallai za su zama kishiyoyin gwamnoni sannan kuma gwamnoni ba za su iya juya su ba wanda kuma wannan babbar matsala ce ga mulkinsu," in ji Faruk.

Dan gwagwarmayar ya kuma ƙara da cewa "sannan idan aka bai wa kananan hukumomi kuɗadensu ta ina gwamna zai samu kuɗin gina gadoji da sauran manyan ayyuka da ake yi a manyan birane da kudaɗen ƙananan hukumomi?

Abin da ya kamata Tinubu ya yi

Masu fafutukar ganin ƙananan hukumomi sun samu ƴancinsu na walwala wanda rashinsa ne wasu ke alaƙantawa da baƙin talaucin da jama'a ke fama da shi a ƙauyukan Najeriya.

"Ni ina ganin barazanar da shugaba Tinubu ya yi ta idan gwamnonin nan ba su bin umarnin kotu ba sun bai wa ƙananan hukumomin nan kuɗadensu to zai fara bai wa ƙananan hukumomin kuɗadensu kai tsaye kamar yadda ake bai wa gwamnoni," in ji faruk Musa Muhammad.

Ya kuma ƙara da cewa "lallai Tinubu ya cancanci a yaba masa dangane da barazanar da ya yi wa gwamnoni. To amma muna fatan barazanar ba ta fatar baki ba ce."

Yaushe za a fara biyan ƙananan hukumomin?

kawo yanzu dai babu wata tabbatacciyar rana da su gwamnoni suka ajiye domin fara biyan kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

Sannan shi ma shugaba Tinubu da ya yi barazanar ayyana dokar shugaban ƙasa domin fara biyan ƙananan hukumomin kuɗaɗen nasu ka itsaye bai faɗi lokacin da zai yi hakan ba.

Amma dai alamu na nuna cewa batun ya taso kuma al'amarin bai yi wa shugaban dadi ba kuma a kowane lokaci za a iya samun yanayin da za a aiwatar hakan.

Sai dai kuma wasu masu fashin baƙi na ganin cewa siyasa ka iya sauya ra'ayin shugaban ƙasa, inda su kansu gwamnonin ka iya yi wa shugaban ƙasar barazanar yi masa tawaye a zaɓen 2027.

Shin asusun hadaka da jihohi ne matsalar kananan hukumomi?

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, a wata tattaunawa da BBC a 2021ya musanta cewa asusun hadaka ne ya haifar da wannan matsala.

Ya ce a lokacin da yake shugabantar jiharsa, yana bayanin yadda za a kasafta kudaden da gwamnatin tarayya ta bayar.

"Idan an aiko da kuɗin akwai takarda da ke dauke da bayanan yadda za a bai wa ko wacce jiha kudadenta, kuma idan aiki za a yi da kudaden wata karamar hukuma sai an tambayi izininta sannan a nemi ta bayar da wani abu domin aiwatar da aikin.

"Babu tilastawa cewa sai an yi amfani da wadannan kudade karfi da yaji," in ji Shekarau.

Ya kuma ce bai kamata a dauki kudaden kananan hukumomi ba a zuba aiki a hedikwatar jiha wadda kawai wasu kalilan ne ke amfana.

"Wani mazaunin kauyen har ya gama rayuwarsa ba zai je inda aka zuba kudaden ba."

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum na ganin ba ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kai ne kawai zai iya kawo karshen matsalarsu a Najeriya saboda su ne suka fi kusa da jama'a kuma su suka fi sanin matsalolinsu ta yadda za su magance su.

Sai dai wasu na ganin su ma suna da nasu laifukan wadanda ke da alaka da zargin cin hanci da rashawa, ko da yake sun sha musantawa.