Shin Facebook da Tuwita na fuskantar barazanar kawowa ƙarshe?

Logon Facebook da Tiwita

Asalin hoton, Getty Images

Idan dai ba kashe intanet ɗinka ka yi ba, to mai yiwuwa ka san sarƙaƙiyar da ta baibaye manyan kamfanonin fasaha na duniya a makonni da suka wuce.

A watan da ya gabata ya bayyana ƙarara cewa manyan kamfanonin da suka haɗa da Apple da Netflix da Amazon da Microsoft da Meta (mamallakin Facebook) da Alphabet (mamallakin Google) - sun tafka asarar fiye da dala tiriliyan uku a cikin wata 12 da suka wuce a kasuwar hannayen jarin Amurka.

A watan Nuwamba, sai da ta kai da yawan kamfanonin nan kamar su Amazon suka sanar da rage ma'aikata a faɗin duniyada ya kai rufe ayyuka 136,000 zuwa ranar 21 ga watan Nuwamna, kamar yadda shafin intanet na Layoffs.fyi website, mai bibiyar korar ma'aikata a kamfanoni ya bayyana.

Da yawa daga cikin ma'aikatan da aka kora ɗin na Facebook ne daga kamfanin Meta, inda aka kori mutum 11,000, Tuwita kuma ya kori mutum 3,700 zuwa yanzu.

Wannan lamari ya bujiro da tambayoyi a kan abin da ka iya faruwa nan gaba da fitattun shafukan sada zumuntar: shin muna tunanin cewa waɗannan kamfanoni ba za su kai labari ba?

Yaya girman matsalar da Facebook da Twitter ke ciki?

Kamar yadda yawan ma'aikatan da aka sallama a can sama ke nunawa, waɗannan shafuka na nuna yadda su ma matsalar tattalin arziki ke shafarsu kamar sauran fannoni.

Mai kamfanin Facebook Mark Zuckerberg

Asalin hoton, Getty Images

Wannan na nufin takaita kudaden da ake zubawa a fannin kasuwancin – da karuwar kudaden tallace-tallace ga masu hulda da shafukan sada zumunta.

"Duk mutumin da ke kokarin samun kudade a yanzu ta wannan hanyar dole ya fuskanci kalubale sosau," a cewar Farfesa Jonathan Knee, wani kwararre a fannin labarai da fasaha a kwalajin kasuwanci na Columbia da ke New York.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Farfesa Knee ya ce shafukan sada zumunta kusa "sun kasance masu harkokin kasuwanci a wannan lokaci".

"Idan ka dogara kan irin wadannan hanyoyin samun kudi shiga, fadawa cikin matsin tattalin arziki zai zame maka kalubale, a cewarsa.

Sabon rahoton da kamfanin Meta ya fitar a karshen watan Oktoba, ya ambato yadda ake samun koma baya a fannin kudaden shiga tallace-tallace saboda matsalar da kamfanin ke cika.

Sai dai hakan ya sake fito da karuwar goggayar kasuwaci tsakaninsa da shafin hamayya na TikTok.

Twitter, da ta rage tagomashi a kasuwa tun bayan saye ta da attajiri Elon Musk ya yi, na fuskantar kalubale da Karin matsaloli da ke da alaƙa da shugabancin Musk da wasu matakansa ma su cike da ce-ce-ku-ce.

Kwanan nan Musk ya dawo da shafin tsohon Shugaba Donald Trump na Amurka bayan gudanar da wata kuri'a ta jn ra'ayi.

A ranar 8 ga watan Janairu aka haramta shafin Trump a tuwita sakamakon sakonni da ya wallafa kan wani rikici da aka yi a birnin Washington.

Wanda ya siyi kamfanin Tiwita Elon Musk

Asalin hoton, Getty Images

Amma alamomin gargadin na nan kafin zuwan Musk: wasu bayanan sirri da Reuters suka samu a watan Oktoba sun nuna cewa mutanen da ke hawa Tuwita sosai akalla sau shida zuwa bakwai a sati da aike sakon tuwita sau uku zuwa hudu a mako – sun ragu sosai tun bayan soma annobar korona.

Reuters ya rawaito wani bincike na cewa kashi 10 cikin 100 na masu amfani da shafin tuwita ke wallafa sakonni da ke jan hankali da kusan kashi 90 cikin 100 da sama musu kudaden shiga.

Sannan zuwa Musk, ya sake bijiro da sabon matsala: a wani bincike da aka wallafa a ranar 3 ga watan Nuwamba, mako guda bayan saye shafin, masu Nazari daga jami'ar Massachusetts sun kiyasta cewa tuwita ya rasa masu amfani da shafin miliyan guda.

Sauye-sauye

Wannan wani abu ne da masana ke ganin zai kawo karshen wasu sauye-sauye a kamfanonin sada zumunta? "Ko wane shafi na da nashi tsarin ci gaba ko nakasu.

Ana daukar tsawon lokaci kafin wasu sauyin su tabbata,"a cewar Dakta Natalie Pang, kwararriya a fannin sadarwa a Jami'ar Singapore.

Dr Pang na da yakinin cewa Facebook da Twitter sun samu habbaka sosai a kasuwarsu lokacin dokar kulle sakamakon annobar korona, inda miliyoyin mutane a fadin duniya suka fuskanci yanayi na takaita zirga-zirgarsu.

Mace na danna wayar komai da ruwanka

Asalin hoton, Getty Images

"A lokacin annobar an samu cigaba a fanin fasahar zamani lura da yadda duniya ke habbaka a fanin kimiyar zamani."

A yanzu, ta ce lokaci ya yi na sake daidaita wasu lamuran.

Wani kwararre da ke ganin a yanzu shafukan Facebook da Tuwita na kasa saboda wasu dalilai shi ne Dakta Lianrui Jia, kwararre a fannin fasahar sadarwa ta zamani a Jami'ar Sheffied da ke Landan.

"Babu mamaki mun yi sake wajen kiyatsa salon karbuwar wadannan fasahohi a kasuwa," a cewar Dakta Jia.

"Masu amfani da wadannan shafuka a yanzu sun soma duba wasu matsaloli da ke tattare da wadanna shafuka."

Manyan kamfanononin biyu na da bambanci-bambanci, sai dai: Facebook na da mutane biliyan uku da ke amfani da shafin a watanni huɗun karshen shekara ta 2022, a cewar Meta, hakan ya sa shafin ya kasance na uku mafi shahara a duniya.

Amma a cikin Fabarairu, Meta ya sanar da cewa shafin ya rasa mabiya a karfin farko na shekaru 18 da ya shafe, abin da yae fa kasuwarsa cikin garari.

Allon TikTok a birnin Cannes na Faransa

Asalin hoton, Getty Images

Tun 2019, Tuwita ya bijiro da tsari da ke mayar da hankali kan tallace-tallace, maimakon adadi masu amfani da shafin.

Alkaluman da ya fitar a watan Oktoba, na nuna cewa akwai mutane miliyan 238 da ke amfani da shafin.

Kodayake, akwai damuwar cewa mutane da ke amfani da wannan shafi na kaucewa samun bayanai na labarai da lamuran yau da kullum, suna ba da fifiko ga fanin abubuwan da suka shafi batsa da kuma kudin intanet na kiripto.

Wannan na iya takaita jan hankali masu talla, da ke kauracewa duk wani abu da zai haifar da ce-ce-ku-ce.

Renaud Foucard, wani Babban Malami tattalin arziki a Jami’ar Lancaster, ta Burtaniya, na cewa takaita amfani da wadannan shafi da wasu gwamnatoci ke yi na zama babban kalubale ga manyan kamfanonin fasaha saboda gogayyar da ke ikin fannin.

Rashin sani

Akwai shafukan da ke ɓacewa ko sannu a hankali su daina tasiri.

Daya daga cikin irin wadannan shafuka shi ne Myspace.com: kamfanin sada zumunta na farko da ya taba tara mutane miliyan 300 a shekara ta 2007.

Amma kuma ya disashe daga baya saboda Facebook, inda a wannan lokaci ya rungumi wasu abubuwan intanet da harkokin wallafa wakoki, inda yanzu masu amfani da shafin a duniya suka kai miliyan shida a faɗin duniya.

A irin wannan shekaru a baya, Orkut da Google ke marawa baya ya samu tagomashi inda ya kasance shafin da aka fi amfani da shi a duniya, kafin ya fuskanci koma baya saboda Mark Zuckerberg – a 2014 shafin ya dishashe.

Shin waɗannan abubuwa ne da ya kamata ake lura da su a wannan lokaci? Ba kowanne masanin ke da tabbacin hakan ba.

Tson dandalin sada zumunta na MySpace

Asalin hoton, Getty Images

Sharhi daga Joe Tidy, wakili kan kusten na'ura

Tunanin babu mamaki a kawo karshen rayuwar kafofin sada zumunta ya kasance abin jan hankali.

Abin da ya kamata ake la'akari da shi, shi ne rayuwar wasu kafofin sada zumunta da a yanzu ba a jin duriyarsu.

Bebo, MySpace da Vine sun yi zamaninsu sun wuce.

Sai dai fasahar zamani a tsawon shekaru, na da ban mamaki da al'ajabi.

Facebook shi ne babban misalin wannan batu.

Kamfanin ya yi kokarin inganta makomarsa ta hanyar saye Instagram da WhatsApp domin ya cigaba da ganiyarsa.

Tuwita kuma na sake bijiro da wasu dabaru domin tabbatar da cewa masu amfani da shafin ba su sauya sheka ba.

Amma shin mutane za su iya barin Tuwita? Akwai shaku dai.

Wadannan shafukan suna da kwarewa kamar masu amfani da ita, kuma shekaru biyar baya ana iya ganin abubuwan da ya wakana da tsare-tsaren da suke bijirowa da shi domin ganin sun riƙe mutane.

Duk da cewa ba kuma za a dauke kai daga 'yar zamani ba wato TikTok da yanzu haka ke ɗaga hankulan abokan hamayya, har ta kai ga ana kirkirar sabbin salo irinsu Club House da BeReal.

Gogayya

Duk da cewa wannan na iya zama kalubale ga Facebook da Twitter na sake dawo wa da karfinsu ko ya iya kawo karshensu, wasuna ganin fitattun shafuka irin wannan dama dole su rinka karo na kalubale irin wannan.

"Misali guda mai karfi shi ne wadannan shafuka na fuskantar karin gogayya,” a cewar Renaud Foucard.

"Idan muka za a yi adalci dole kasuwar ta bai wa sabbin kamfanonin damar ba je tasu fasahar domin mutane su kasance suna da zabi."