Ɗan bindiga ya harbe mutane da dama a Denmark

Asalin hoton, EPA
'Yan sanda a Denmark sun ce an kashe mutane da dama yayin da wasu suka jikkata a harbe-harbe da aka yi a wani rukunin kantuna da ke Copenhagen babban birnin kasar.
Ba a san manufar dan bindigar ba wanda 'yan sanda suka ce dan asalin kasar ne.
Da yake sanar da mutuwar mutanen, babban sufeton 'yan sanda Soeren Thomassen ya ce an kama wani matashi ɗan Denmark mai shekara 22 bisa zarginsa da hannu a harin.
Mista Thomassen ya ce ba a san dalilin da ya sa aka kai harin ba amma akwai yiwuwar na "ta'addanci ne".
Wadanda suka shaida lamarin sun yi magana kan hargitsin da aka shiga lokacin da aka ji karar harben-harben bindiga a rukunin kantuna na Fields Mall da ke gabashin birnin.
Wata mai suna Emilie Jeppesen ta faɗa wa jaridar Jyllands-Posten: " Ba mu san abain da ke faruwa ba, kawai sai mu ga wuri ya haustine."
Shi ma wani da abin ya faru a gabansa, Mahdi Al-Wazni, ya faɗa wa TV 2 cewa maharin na ɗauke ne da "bindigar farauta".
Da yake magana a taron manema labarai, Mista Thomassen ya ce ya yi wuri a faɗi adadin waɗanda aka kashe ko aka jikkata a harin. Sai dai ya faɗa wa 'yan jarida cewa babu alamun akwai wasu maharan daban.
Fields ce cibiyar kasuwanci mafi girma a Denmark, inda take da shaguna 140 da kuma wuraren cin abinci.











