Motocin da ƴan majalisar dokokin jihar Kebbi suka saya wa Tinubu sun bar baya da ƙura

Asalin hoton, others
Ƙungiyoyin farar hula tare da wasu ƴan hammaya sun soki matakin da ƴan majalisar dokokin jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya suka ɗauka na saya wa ƙungiyar yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar da shugaba Bola Ahmed Tinubu motoci har guda 25 da aka ƙiyasta kuɗin kowace zai kai naira miliyan shida.
Ƙungiyoyin dai sun ce ƴan majalisar sun yi amfani ne da kuɗin talakawa wajen sayen motocin da suka ce ba su da wani tasiri ga al'ummar jihar.
Sun bayyana matakin a matsayin wani babban almabazaranci da dukiyar talakawa musamman a wannan lokaci da jihar ke fama da koma bayan tattalin arziki da matsalolin tsaro.
Gammayar ta yi Alla-wadai da gudumuwar motoci da kowane ɗan majalisar dokokin jihar ya ya bayar da guda ɗaya har guda 25 ras domin yaƙin neman zaɓen da ko kaɗa gangarsa ba'a yi ba.
Kwamared Ibrahim Ngaske shugaban wata ƙungiyar farar hula a jihar ta Kebbi ya yi iƙirarin cewa waɗannan kuɗaɗe ba daga cikin aljihun ƴan majalisar dokokin jihar aka fitar da su ba:
''Halin da ake ciki yanzu na matsalar talauci a mafi yawan mazaɓu na waɗannan mutane, za ka iske akwai matsalar tsaro, mutane suna nan a sansanin waɗanda suka rasa muhalansu, akwai buƙatu na musamman da ya kamata a ce waɗannan ƴan majalisun sun biya mu su.''
''Aƙalla wannan motar an sayeta miliyan 6 ko 7, aƙalla miliyan 2 zai iya ba wani gari wanda ke fama da matsalar ruwa rijiyar burtsatse'', in ji shi.
A ɗayan ɓangaren ƴan majalisar dokokin jihar Kebbi sun ce bai kamata a soki matakinsu ba . Hon Mohammed Garba Bena mai wakiltar Donko-Wasagu ya ce sun yi haka ne domin su taimakawa jami'yyar APC ta samu nasara a zaɓe mai zuwa:
''Ita wannan ƙungiyar tana goyon bayan gwamnan jihar da shugaba Tinubu su sake zarcewa. Ƙungiyar ta na aiki ne don taimakawa jam'iyyar APC ta kai gacci a zaɓen 2027.''
Ya kuma ce wannan mataki shi ne mafi alheri ga jihar baki ɗaya.
''In da ba a aiki sai a ce to nan ya kamata a mai da hankali, akwai ayyuka da dama da aka yi, misali a mazaɓata an gyara asibitin Bena da masallatai da dama'', in ji shi
Sai dai Hon Mohammed ya ƙi ya yi bayani a kan yadda suka tara kuɗin.
Ita ma gwamnatin jihar Kebbin ta ce ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wajan samar wa alummar jihar da ababen more rayuwa tare da inganta tsaro.














