Maƙiya na neman shiga tsakanina da Tinubu - Gwamna Nasir Idris

Dr Nasir Idris Kauran Gwandu

Asalin hoton, Dr Nasir Idris Kauran Gwandu/facebook

Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnan jihar Kebbi Dokta Nasir Idris, ya zargi wadanda ya kira ''masu son bata tsakaninsa da Shugaba Bola Tinubu'' da kirkira labarin cewa zai bar jam'iyar APC.

Gwamnan dai na mayar da martani ne ga wani rahoto da ke wadari a shafukan sada zumunta, cewa shi da wasu gwamnonin APC hudu na shirin ficewa daga jam'iyyar, tare janye goyon bayansu ga Shugaba Tinubu.

A taron da ya kira na 'yan jam'iyyar APC a jihar Kebbi domin karyata labarin, Gwamnan ya ce ana zargin ya koma SDP kuma mutane ne da ba sa son zaman lafiya ke yada wannan jita-jita.

Ya ce shi bai ga dalilin barin APC ba, kawai maƙiyansa na siyasa ke son shiga tsakaninsu da Bola Tinubu ganin cewa akwai kusanci da alaƙa mai kyau tsakaninsu.

Gwamnan ya jaddada cewa yanzu ya soma goyon-bayan shugaban kasa da jam'iyyarsa don haka duk masu yaɗa wannan raɗe-raɗin za su yi su gama.

Mahalarta taron irinsu Hon Muhammad Usman, kakakin majalisar Kebbi ya ce su ba suyi mamakin raɗe-raɗin da aka rinka yaɗawa ba, saboda sun san dama maganganu ne marasa tushe.

"Mun ji dadi da gwamna ya fito ya yi wannan bayyani saboda zaman lafiya, duk da cewa munsan cewa midiya marasa lasisi ke yada wanna batu".

Ita ma jam'iyyar APC a Kebbi ta ce tayi mamaki wannan labari, kuma tana sane cewa duk surutai ne na karya domin suna da imanin cewa gwamna na tare da su haka ma da shugaban kasa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jita-jita da aka rinka yadawa kan Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu sun hada da wasu gwamnonin hudu da ake cewa za su fice daga APC zuwa SDP.

Fagen siyasar Najeriya dai na cigaba da daukan sabon salo a kullum musamman a wannan lokaci da ake samun karuwar 'yan hamayya da ke komawa APC.

Komawar gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori jam'iyyar APC a tsakiyar makon da ya gabata ya sa masana kimiyyar siyasa da wasu daga ɓangaren hamayya fara tuhumar shugaba Bola Tinubu da yunƙurin mayar da Najeriya kan tsarin jam'iyya ɗaya.

Bugu da ƙari, sauya sheƙar da tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban Najeriya na PDP, Dr Ifeanyi Okowa zuwa jam'iyyar mai mulki da kuma iƙrarin da gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya yi cewa zai bai wa Bola Tinubu goyon baya, sun ƙara sanya fargabar tattara masu hamayya a ƙarƙashin jam'iyya guda.

PDP ita ce babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, sai dai rikice-rikicen cikin gida ya yi mata dabaibayi, lamarin da ake ganin ya hana ta taka rawar da ta kamata a ɓangaren adawa.

Haka nan kasancewar ɗaya daga cikin manyan ƴaƴanta - Nyesom Wike - a cikin gwamnatin APC ta Bola Tinubu ya sanya wasu ke zargin ta da kasancewa tamkar "wani reshe na jam'iyyar APC".

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa , ya ce a yanzu babu wata hamayya da ta rage a fagen siyasar Najeriya.

A tattaunawarsa da BBC ya ce 'yan siyasar kasar su ne ke hamayya da kansu da cutar juna game da neman mukamai ba tare da sun anfana wa talakawa wani abu ba.

Bafarawa ya bayyana hakan ne ganin yadda wasu jiga-jigan jam'iyyun hamayya na kasar ke tururuwa suna komawa jam'iyya mai mulki ta APC a wannan tsakanin yayin da ya rage wajen shekara biyu a yi babban zabe na gaba, a 2027.

Tsohon gwamnan na Sokoto ya ce, yanda siyasar Najeriya take ciki a yanzu abin ya wuce saninsu.