Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waɗanne ƴan wasa ne suka fi zura kwallo a tarihin gasar cin kofin Afirka?
- Marubuci, Ousmane Badiane
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist BBC Afrique
- Lokacin karatu: Minti 8
Tun fara gasar cin kofin Afirka a shekarar 1957, an ga yadda zaƙaƙuran ƴan wasan gaba suka zura kwallaye da kuma haskakawa - abin da ya ɗaga darajar gasar a faɗin nahiyar.
Shahararrun ƴan wasa irinsu Samuel Eto'o zuwa Laurent Pokou, Rashidi Yekini, Sadio Mané da Hossam Hassan da kuma Kalusha Bwalya, sun kasance masu cin kwallaye na gaske, inda ƙoƙarinsu ke bai wa ƙasashensu nasara da kuma barin tarihi a gasar.
Kwanaki kalilan kafin fara gasar cin kofin Afirka karo na 35 wanda za a yi a ƙasar Moroko daga 21 ga watan Disamban, 2025 zuwa 18 ga watan Janairun, 2026 - BBC ta duba ƴan kwallon da suka fi zura kwallaye da kuma haskawa a gasar.
1. Samuel Eto'o (Cameroon): Kwallo 18
Har yanzu Samuel Eto'o shi ne wanda ya fi kowane ɗan kwallo zura kwallaye a gasar ta cin kofin Afirka, inda yake da kwallo 18.
Ya lashe gasar sau biyu ( a shekara ta 2000, da 2002), kuma ya kasance yana ceton ƙasarsa ta Kamaru a duk lokacin da ta shiga tsaka mai wuya.
Tasirin da ya yi a gasar ba zai taɓa misaltuwa ba, kuma yana ɗaya daga cikin ƴan wasa mafi hazaƙa da aka gani a zangon karshe na gasar.
2. Laurent Pokou (Ivory Coast): Kwallo 14
Laurent Pokou ya riƙe kambun wanda ya fi zura kwallaye a gasar na tsawon lokaci da kwallo 14 wanda ya ci a shekarun 1970.
Kwallaye biyar da ci Habasha a 1970 da kuma guda takwas da ya ci a lokacin gasar, na cikin abubuwan tarihi da ba za a manta ba a gasar.
3. Rashidi Yekini (Nijeriya): Kwallo 13
Rashidi Yekini wanda ya kasance ɗan wasa mai ƙwazo ga tawagar Super Eagles, ya ci kwallaye 13 a gasar, abin da ya saka shi cikin jerin ƴan wasa masu zura kwallaye a Afirka.
Ya kasance ɗan wasa mafi hazaka da kuma wanda ya fi cin kwallaye a gasar da aka yi a 1994.
Ya ɗau tsawon lokaci yana taimakawa Najeriya ganin irin ƙwarewarsa haɗe da ƙarfi, nitsuwa da kuma ƙwazo na tsawon shekaru.
4. Hassan El-Shazly (Masar): Kwallo 12
Hassan El-Shazly yana ɗaya daga cikin ƴan wasan gaba na farko-farko a tarihin gasar AFCON.
Ya samu damar zura kwallaye 12 - kuma yana cikin ƴan wasa kalilan da suka ci kwallo uku rigis a gasar har sau biyu.
Iya cin kwallo da kuma tsayawa yanda ya kamata a cikin fili, na cikin abubuwan da suka sa Masar ta shahara sosai a kwallon kafa a shekarun 1960 da 1970.
5. Didier Drogba (Ivory Coast), Hossam Hassan (Masar), Patrick Mboma (Kamaru): Kwallaye 11
Akwai shahararrun ƴan kwallon Afirka guda uku da kowannensu ya zura kwallaye 11.
Didier Drogba ya zura kwallaye 11, inda ya taimakawa Ivory Coast zuwa wasan karshe har sau biyu (a 2006, 2012). Ya kasance babban jagora ga tawagar ƙasar, inda tasirinsa ya taimakawa gasar ba kaɗan ba.
Patrick Mboma shi ma ya zura kwallo 11, inda ya kasance ɗan wasan Kamaru mafi haɗari ga masu tsaron baya a shekarun 2000. Ya lashe kyautar gwarzon ɗan kwallon Afirka a shekara ta 2000 da kuma lashe gasar AFCON har sau biyu (a 2000, da 2002).
Hossam Hassan ya kasance ɗaya daga cikin zakakuran ƴan wasan gaba na Masar, inda ya zura kwallo 11 a gasar ta cin kofin Afirka. Ya lashe gasar sau uku a 1986, 1998 da kuma 2006.
Shi ne ɗan wasa ɗaya tilo da ya lashe gasar AFCON har sau uku a lokuta daban-daban.
6. Kalusha Bwalya (Zambiya), Francileudo Santos (Tunisiya), Joël Tiéhi (Ivory Coast) André Ayew (Ghana), Pierre Ndaye Mulamba (Zaire): Kwallaye 10
Kalusha Bwalya (Zambiya)
Kalusha Bwalya ya ci kwallo 10 a gasar cin kofin Afirka, abin da ya ɗora shi cikin sahun waɗanda suka fi cin kwallo a gasar. Ya taka rawar gani sosai a gasar da aka yi a 1996, inda ya zama wanda ya fi zura kwallaye da kwallo biyar kuma ya lashe kyautar ɗan wasa mafi ƙwazo.
Tsohon kyaftin ɗin na Zambiya, na cikin ƴan wasa kalilan da suka ci kwallo aƙalla ɗaya a gasa har shida.
Francileudo Santos (Tunisiya)
Francileudo Santos na cikin ƴan wasa masu muhimmanci a lokacin da Tunisiya ta lashe gasar a gida a 2004. Shi ne ɗan wasan da ya cin kwallo a gasar ta 2004 - ya ci kwallaye 10 a ɗaukacin gasar - ya samu damar yin haka ne a gasar 2004, 2006 da kuma 2008.
Joël Tiéhi (Ivory Coast)
Joël Tiéhi ya ci kwallo 10 a gasar AFCON, abin da ya mayar da ƙasar kan ganiyarta a shekarun 1990. Yana ɗaya daga cikin ƴan wasan gaba masu ƙwazo na ƙasar bayan zamanin Pokou.
André Ayew (Ghana)
André Ayew na cikin ƴan wasa kalilan da suka iya cin kwallo 10 a tarihin gasar cin kofin Afirka. Ya kasance jagoran ƙasar Ghana na tsawon shekara goma, ya kuma ci kwallo a gasa shida da aka yi daban-daban.
Pierre Ndaye Mulamba (Zaire/DR Congo)
Duk da cewa sau biyu ya buga gasar AFCON, Pierre Ndaye Mulamba ya kasance cikin ƴan wasan gaba masu hakaza a tarihin kwallon kafa a Afirka.
Ya ci kwallaye 10, kuma yana riƙe da kambun wanda ya fi zura kwallo a gasa ɗaya da kwallaye tara a 1974.
Baya ga waɗannan manyan ƴan wasan kwallon kafa a Afirka, akwai wasu yan wasa ma da suka ci kwallaye kaɗan amma suka kafa tarihi a gasar.
7. Abdoulaye Traoré (Ivory Coast), Vincent Aboubakar (Kamaru), Sadio Mané (Senegal), Manucho (Angola): Kwallaye 9
Abdoulaye Traoré "Ben Badi" (Ivory Coast)
Abdoulaye Traoré, wanda aka fi sani da Ben Badi, yana cikin ƴan wasan da suka shahara a shekarun 1980 da 1990. Ya ci kwallaye tara a tarihin gasar da kuma lashe gasar a 1992.
Vincent Aboubakar (Kamaru)
Vincent Aboubakar wanda ya kasance jagora a Kamaru, ya ci kwallaye tara a AFCON, ciki har da rawar da ya taka a gasar a 2022, inda ya zama wanda ya fi cin kwallaye.
Sadio Mané (Senegal)
Sadio Mané ya ci kwallaye tara a AFCON, kuma yana cikin ƴan wasan da suka taka rawa a lokacin da Senegal ta lashe gasar a 2022.
Manucho (Angola)
Manucho shi ne ya jagoranci Angola a shekarun 2000 tare da zura kwallaye tara a tarihin gasar. Ya taka muhimmiyar rawa a gasar ta AFCON.
8. Ahmed Hassan (Masar), Asamoah Gyan (Ghana), Wilberforce Mfum (Ghana), Pascal Feindouno (Guinea), Seydou Keita (Mali): Kwallaye 8
Ahmed Hassan (Egypt)
Ahmed Hassan, ya lashe gasar cin kofin Afirka sau huɗu, kuma ya kasance ɗan wasa mai hazaka ga ƙasar Masar. Ya ci kwallaye takwas a tarihin gasar.
Wilberforce Mfum (Ghana)
Wilberforce Mfum ɗan wasan gaba ne na ƙasar Ghana mafi ƙwazo a shekarun 1960. Ya zura kwalaye takwas a gasar Afcon da taka rawar gani lokacin da ƙasar ta lashe gasar a 1963 da 1965.
Pascal Feindouno (Guinea)
Pascal Feindouno ɗan wasan gaba na Guinea ne mafi hazaka. Kwallaye takwas ya ci a gasar da kuma taka rawar gani matuka.
Seydou Keita (Mali)
Seydou Keita, ɗan wasan tsakiya ne na ƙasar Mali wanda ya yi tasiri sosai a gasar.
Ya samu damar zura kwallaye takwas a tsawon lokacin da ya buga gasar.
Asamoah Gyan (Ghana)
Asamoah Gyan, ya kasance ɗan wasan Ghana da ya fi cin kwallo a gasar Afcon da kwallaye takwas.
Ya jagoranci tawagar Black Stars a lokuta da dama, ciki har da zuwa wasan karshe a 2015.
Shahararru bakwai
Yana da matukar wuya a kammala wannan muƙala ba tare da bayyana sunayen waɗannan zakaru ba a ɓangaren kwallon kafar Afirka waɗanda suka haɗa da Roger Milla (Kamaru), Frédéric Kanouté (Mali), Jay-Jay Okocha (Nijeriya) and Mohamed Salah (Masar) waɗanda dukkansu suka ci kwallaye bakwai-bakwai.
Roger Milla (Cameroon)
Ɗan wasan kwallon kafa ne a gaske a tarihin Afirka - ya ci kwallo bakwai a gasar lokacin jagorantar Kamaru. Ya kafa tarihi na gaske a ƙasarsa ta Kamaru wanda ba za a manta ba.
Frédéric Kanouté (Mali)
Frédéric Kanouté ya ci kwallo bakwai a gasar Afcon. Ɗan wasa ne da ya taka rawar gani wajen farfaɗo da Mali a shekarun 2000. Ya taimakawa ƙasar wajen mayar da ita kan ganiyarta a nahiyar.
Jay-Jay Okocha (Nigeria)
Jay-Jay Okocha wanda ya riƙe tsakiyar Najeriya a shekarun 1990 da farkon 2000, ya zura kwallaye bakwai. Ya taka muhimiyar rawa musamman wajen irin salon wasansa da kuma ƙwarewa - abin da ya sanya ya samu tagomashi a idon ƴan nahiyar.
Mohamed Salah (Masar)
Mohamed Salah wanda taɓa zuwa wasan karshe na Afcon har sau biyu, ya zura kwallaye bakwai. Ɗan wasa ne mai ƙwazo wanda ya shahara a faɗin duniya.
Salon wasarsa da kuma tasiri ya sanya shi jagora a ɓangaren masu buga kwallo a Masar da kuma duniya.