Yadda aka sa wa yara 175 cutar HIV a Birtaniya

Michael as a young child

Asalin hoton, Family photo

Sama da kananan yara 150 masu fama da cutar borin jini ne aka saka wa cutar HIV a tsakanin shekarun 1980s, kamar yadda wani kundi da BBC ya gani daga Kundin Tattarai Bayanai na kasa ya fada.

Wasu daga cikin iyalan da lamarin ya shafa suna bayyana hujjoji ne a gaban kwamitin binciken lamarin, wanda ake gani a matsayin bala'in mafi muni a tarihin Hukumar Lafiyar ta Kasar.

Kusan shekara 36 kenan da suka gabata-karshen watan Oktoban 1986- amma Linda ba za ta taba manta ranar da aka bayyana mata cewa danta ya kamu da cutar HIV ba.

Kiranta aka yi zuwa dakin duba marasa lafiya a Asibitin Yara na Birmingham tare da danta Michael mai shekara 16.

Tun yana karaminsa, aka gano yana fama da cutar borin jini.

A tunanin Linda, za a mata batun mayar da danta zuwa babban asibitin Sarauniya Elizabeth ne da ke cikin birni.

"Abu ne da muka saba, wanda hakan ya sa na bar mijina (mai rikon Michael) a mota a waje," inji ta.

"Kwatsam sai likitan ya ce min Michael ya kamu da cutar HIV, abin mamaki shi ne yadda yake maganar kamar yana labari a kan yanayin sararin samaniya. Nan da nan cikina ya duri ruwa.

"Muka fito muka shiga mota, na fada wa mijina, sai dukanmu muka yi gum har zuwa gida babu mai magana. Wannan ne yanayin da muka shiga na damuwa."

Kamuwa da cutar

A lokacin ana tsaka da annobar Aids- watanni kadan kafin a fara shirin gwamnati na wayar da kan mutane a kan cutar a tashoshin talabijin.

Sannan kuma a lokacin ana tsananin kyarar masu dauke da cutar.

A shekarar 1985, iyaye da sama sun cire yaransu daga makarantun firamare a Hampshire, bayan wani yaro mai shekara 9 - wanda shi ma yana fama da matsalar borin jini- ya kamu da cutar ta Aids, kamar yadda ake kiran HIV a lokacin.

Michael ba ya so a fada wa abokansa da 'yan uwansa halin da yake ciki.

"Haka ya cigaba da rayuwarsa. Bai fada wa abokansa komai ba domin yana so ya cigaba da rayuwarsa kamar kowa."

Linda sitting at a table

A tsakanin 1970 zuwa 1991, mutum 1,250 masu fama da matsalolin jini sun kamu da cutar HIV bayan sun yi amfani da maganin Factor VIII, wanda sabon magani ne da ke sauya sinadarin da ke sa wa jini ya yi guda-guda a jikin dan Adam.

Ciki har da kananan yara da suke karbar magani a wajen likitocin Hukumar Lafiya a asibitoci da makarantu ko kuma asibitocin masu fama da cutar borin jini.

Haka kuma ana zargin dubbai sun kamu da cutar hepatitis C, wadda za ta iya shafar kodarsu da kuma kansa, ko dai ta hanyar amfani da maganin ko kuma wajen karin jini.

Kusan rabin wadanda suka kamu da cutar sun mutu ne a sanadiyar cututtuka masu alaka da HIV kafin a gano maganin rage radadi da yake saukar da cutar sosai.

Masu amfani da magani

A lokacin, Ingila ba ta da isasshen jini a ajiye, wanda hakan ya sa aka yi jigilar Factor VIII din daga Amurka.

Kowanne hadin, an hada shi ne jinanen da dubban mutane suka bayar. Wanda hakan ke nufin, idan daya na dauke da cutar, sauran ma za su iya samu.

Kamfanonin magungunan Amurka ne suka rika biyan mutane kudi domin su ba da jini-ciki har da fursunoni da masu ta'ammuli da kwayoyi da za su iya kasancewa da cututtuka.

Linda tana tuna kasancewarta wadda aka fara bayyana wa batun na Aids din a Asibitin Yara na Birmingham a 1984, sannan aka gargade ta da ta lura da wasu alamomi.

Amma ta ce ba a yi musu cikakken bayanin hadarin lamarin ba-wani lokacin ma wata nas fada mata ta yi ta daina damuwa saboda a cewarta, "Michael yana nan lafiyarsa kalau."

Duk a wannan lokacin, danta Michael yana cigaba da karbar maganin da aka kawo daga Amurka.

An kulle tsohon asibitin Sarauniya Elizabeth na Birmingham a shekarar 2010, aka canja masa waje.

Queen Elizabeth hospital, Birmingham

Daga bisani sai Michael ya fara rashin lafiya-daga zufa zuwa zazzabi mai zafi da tari.

Amma duk da haka ya cigaba da rayuwarsa kamar kowa-Yana tafiye-tafiye, da jin wakokin da kuma goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta West Bromwich Albion

"Watarana akwai wani wasa mai zafi a Wembley, amma kuma ba ya jin dadin jikinsa," inji Linda.

"Sai muka shirya shi, sannan ya hadu da abokansa. Shi dai burinsa in har zai iya karasa filin, to zai je."

Daga bisani da ya fara girma, garkuwar jikinsa suka fara rage karfi, sai Michael ya fara rama da saurin gajiya da mantuwa.

Michael as a young man

Asalin hoton, family photo

An fara kai shi Asibitin Heartlands ne da ke Birmingham, inda Linda wadda ta ajiye aikinta na kuku ta kasance tana jinyar danta Michael har zuwa karshen rayuwarsa.

"Ya ce min 'Mama, ba za ki taba zama kaka ba,' sai in ce masa, 'kar ka damu da wannan.' Wannan ne abun da na fi tunawa yana fada," inji Linda.

Daga baya Michael ya kamu da cutar bakon dauro da tari- wadanda duk ya samu a sanadiyar kamuwa da cutar HIV din.

Ya rasu ne a 26 ga Mayun 1995, mako daya kafin zagayowar ranar haihuwarsa da zai cika shekara 26.

Taro na musamman 

Kusan bayan shekara 30, Linda ta bayyana domin bayar da hujjoji a gaban kwamitin da ya dade yana bincike a kan lamarin.

Za ta bayyana ne tare da iyayen sauran yaran, a wani taro na musamman domin jin ta bakin iyalan wadanda suka kamu da cutar a tsakanin 1970s zuwa 1980s.

"Na ga lallai akwai bukatar in bayyana komai ne domin in taimaka wajen binciken lamarin," inji ta.

"Dukanmu muna so mu san yadda aka yi lamarin ya auku, kuma aka bari ya cigaba da faruwa."

Linda ta bukaci a sakaya sunan mahaifinta.