Ƙasashen duniya sun kaɗu da kisan Falasɗinawa fiye da 100

Ƙasashen duniya na ci gaba da sukar Isra’ila bayan mutuwar Falasɗinawa fiye da ɗari, waɗanda tsananin yunwa ta sa su yin cunkosa kan motocin dakon kayan agaji a birnin Gaza.

Isra’il ta amince cewa sojojin ta sun buɗe wuta a kan mutanen, amma ta ce mafiya yawan mutawar ta faru ne saboda tirmitsitsin da aka samu.

Shugaba Macron na Faransa ya ce da gangan sojojin Isra’ila suka kai hari a kan fararen hula, ya kuma yi Allah-wadai da lamarin.

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya ma ya bayyana kaɗuwar sa kan lamarin, yana mai cewa dole a gudanar da bincike mai zaman kansa don zaƙulo waɗanda ke da hannu.

Shi ma shugaban sahshin tsare-tsaren ƙungiyar Tarayyar Turai, ya ce ba za a kawar da kai daga wannan kisan gillar ba.

Sai dai kuma, duk da cewa shugaba Biden ya ce lamarin zai kawo koma-baya ga ƙoƙarin cimma tsagaita wuta, rahotnni sun ce Amurka ta hana a fitar da sanarwar da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya tsara fitarwa kan kisan Falasɗinawan.

Hukumomin Falaɗinawa sun ce da gangan dakarun Isra’ila suka buɗe wuta kan mutanen, yayin da Isra’ilan ke cewa sojojin sun yi harbi ne kan mutanen da ke da barazanar tsaro ne gare su.