Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda karancin maganin kashe radadi ke jefa mutane cikin mawuyacin hali a Gaza
Likitoci a fadin Gaza sun kwatanta irin mawuyacin hali da mutane suke ciki, musamman ma wadanda ba a samu damar yi mu su maganin kashe radadi ba yayin da ake fama da karancin magunguna.
"Saboda karancin maganin kashe radadi muna barin marasa lafiya su yi ta ihu na tsawon sa'o'i," kamar yadda wani likita ya shaida wa BBC.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta kwatanta yanayin tabarbarewar bangaren lafiya a Gaza da cewa ba zai misaltu ba.
Ta ce asibitoci 23 a Gaza sun daina aiki kwata-kwata ya zuwa ranar Lahadi - 12 kuma na aiki na takaitaccen lokaci.
WHO ta ce hare-hare ta sama da kuma rashin kai kayan agaji ya janyo tabarbarewar al'amura a Gaza.
Dakarun tsaron Isra'ila sun ce Hamas ta amfani da asibitoci da kuma cibiyoyin lafiya a fakaice wajen shirya kai hare-hare.
A wata sanarwa ga BBC, IDF ta ce ba ta kai hare-hare kan asibitoci ba, sai dai ta shiga cikin wasu yankuna...domin tarwatsa wuraren Hamas da kama mayakan kungiyar, yayin da take aiki da taka tsan-tsan.
Sojojin sun ce suna bari a kai agaji zuwa cikin Gaza, ciki har da magunguna.
Kungiyoyin ba da agaji, ciki har da WHO, sun ce an sha takaita kai agaji cikin Gaza.
Asibitoci sun cika makil
Yawancin asibitoci a Gaza sun cika makil kuma babu isassun kayan aiki, in ji ma'aikatan lafiya. Akwai rahotanni da ke cewa wasu asibitoci a kudancin Gaza na kwantar da marasa lafiya fiye da daya a kan gado daya.
An kafa asibitoci hudu masu gadaje 305 a wasu sansanoni a Gaza, a cewar WHO.
A ranar Lahadi, WHO ta ce asibitin Nasser da aka kafa a kudancin Gaza, shi ne baya-bayan nan da ya daina aiki, bayan wani samame da sojojin Isra'ila suka kai kansa.
Sojojin sun ce sun gano makamai a asibitin a ranar Lahadi da dare, da kuma magunguna dauke da sunaye da kuma hotunan wadanda aka yi garkuwa da su, kuma sun kama daruruwan 'yan ta'adda da ke boye a can.
"Hamas ta ci gaba da sanya 'yan Gaza marasa galihu cikin babbar barazana ta hanyar amfani da asibitoci wajen tsara yadda za su kai hare-hare," kamar yadda suka fada wa BBC tun da farko.
Jami'an lafiya a asibitoci da ke kusa sun ce kula da marasa lafi ya sanya su shiga cikin mawuyacin hali.
Yousef al-Akkad, darekta a wani asibitin Turawa da ke kudancin birnin Khan Younis na Gaza, ya kwatanta halin da ake ciki a can a matsayin mafi muni da ba a gani ba tun fara yakin.
"Al'amarin ya yi tsanani kafin yanzu, don haka me kake tunani bayan karbar karin daruruwan mutanen da aka daidaita wadanda kuma ke mafaka a yanzu?
Ya ce asibitin ba shi da isassun gadaje ga marasa lafiya da ke bukatar kulawa, don haka likitoci na shimfida kyallaye a kasa ba tare da saka komai ba don ganin sun yi mutane magani.
Wasu likitoci a fadin Zirin Gaza su ma sun ce yanayin ya yi muni. "Idan aka samu wani da matsalar bugun zuciya, muna kwantar da su a kasa da kuma fara yi musu magani,'' in ji Dr Marwan al-Hams, darektan Asibitin Shahidi Mohammed Yusuf al-Najjar.
Wani kwamitin siyasa na Hamas ya nada darektocin asibiti a Gaza. Wasu likitocin na nan kafin Hamas ta karbi iko da Zirin Gaza.
Magunguna da kai agaji
Likitcoi sun ce suna cikin mawuyacin hali sakamakon karancin kayayyaki da kuma magunguna. "Mun kasa samun na'urar taimakawa wajen yin numfashi," kamar yadda wani likita ya shaida wa BBC.
"Ba mu da magungunan kashe radadi, kayakin dakin bayar da agajin gaggawa da sauran su,'' in ji Dr al-Akkad. "Akwai mutane da yawa wadanda suka kone... ba mu da maganin kashe radadi da za mu iya ba su.''
Wani likita ya tabbatar da cewa ana ci gaba da aiki ba tare da magunguna kashe radadi ba.
A baya-bayan nan, wata tawagar Hukumar Lafiya ta Duniya ta samu wata yarinya 'yar shekara bakwai a asibitin Turawa na Gaza da ke fama da tsananin ciwo sakamakon konewa da ta yi a jikinta, sai dai ta kasa samun maganin kashe radadi saboda karancinsa.
Mukaddashin darektan asibitin Al-Awda, Dr Mohamed Salha, ya ce ana kai mutanen da suka ji ciwo a kan dawakai da kuma jakuna don yi musu magani.
''Abin da ya fi taayar da hankali shi ne ganin yadda raunukan mutane ke rubewa, saboda kasa yi musu aiki tsawon makonni biyu ko uku,'' in ji likitan.
Ya ce likitoci a can sun yi aikin tiyata da amfani da toshi saboda karancin wutar lantarki.
'An raba likitoci da iyalansu'
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce akwai kusan likitoci 20,000 da ke aiki a Gaza, sai dai yawancinsu ba sa aiki "saboda suna cikin mawuyacin hali na neman tsira da kuma kula da iyalansu.''
Dr al-Akkad ya ce alkaluman jami'an lafiya da kuma 'yan sa kai a asibitinsa sun karu, saboda mutane da aka daidaita daga wasu yankuna na zuwa neman taimako. Sai dai ya ce da wuya su kula da kowane mara lafiya saboda yawansu da kuma irin raunukan da suka ji.
Ya ce mutane sun zo asibitin sakamakon fuskantar tashin bama-bamai.
"Za ka mutum daya ya zo da raunukan kwakwalwa, karyewar kwankwaso, karyewar yatsa, wasu lokutan kuma har da rasa ido... babu irin raunin da ba za ka gani ba a asibitinmu.''
Ya ce mutum daya na bukatar likitoci biyar ko fiye domin kula da shi saboda irin raunukan da ya ji.
An raba wasu likitoci da suka ci gaba da aiki da iyalansu.
"Iyalina sun yi nisa da ni sama da watanni uku kuma ina son ganinsu,'' in ji Dr Salha a arewacin Gaza, wadda iyalansa ke zaman mafaka a kudanci.
"Abu mai kyau dai shi ne ina nan domin taimakon yara, mata da kuma tsofaffi wadanda ake kula da su da kuma ceto rayuwarsu.''
'Babu dakin kwantar da mutanen da raunukansu ya tsananta'
Likitoci sun fada wa BBC cewa mutane a Gaza wadanda suka gamu da munanan raunuka sun shiga cikin mawuyacin hali.
"Maganar gaskiya ba mu da wasu gadaje na kwantar da su,'' a cewar Dr al-Akkad.
"Duk mutanen da ake duba su sau hudu a mako daya, a yanzu sau daya a ke duba su a mako. Idan wannan mutumi yana yi sau sa'o'i 16 a mako daya, yanzu sa'a daya ce kacal.''
Wasu mata na haihuwa a sansanonin da aka kafa ba tare da samun kulawa ba, yayin da asibitocin da ke karbar haihuwa suka ce ba su da isassun wurare.
"A wani sashi za ka ga mutum ya mutu, sannan a daya kuma za ka ga an haifi jariri. Ana haihuwar yara sannan babu nonon shayar da su. Asibitin na samar da roban nono guda ga kowane yaro,'' in ji Dr Salha.
Mutane na zuwa asibitoci da ciwuka da suka yadu cikin al'umma wadanda kuma ba su da muhalli mai kyau.
"Akwai ciwuka kuma mun kasa magancesu,'' in ji Abu Khalil, mai shekara 54, wanda aka daidaita a Rafah da ke kudancin Gaza.
"Muna fita tun asuba do shiga layuka, watakila ma za ka ga samu mutum 100 a gabanka. Za ka iya komawa gida hannu rabbana.''