Yadda 'yan kasashen waje ke neman mafaka a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da 'yan gudun hijira da 'yan ci-rani da kuma mutanen da aka raba da muhallansu ta Najeriya NCFRMI, ta ce yanzu haka akwai mutanen da suka rugo zuwa Najeriya daga kasashe kusan arba'in da uku da suka hada da Kamaru da Jamhuriyyar Dimokuradiyar Kwango da Siriya da sauran su domin neman mafaka.
Hukumar ta ce mutanen sun zo Najeriya don samun mafaka ne sakamakon rikice-rike da ake fama da su a kasashen nasu.
Jami'in hukumar mai kula da shiyyar arewa ta tsakiyar Najeriya, Basheer Yusuf, ya shaida wa BBC cewa 'yan gudun hijira da neman mafakar da suka zo daga wasu kasashen zuwa Najeriya sun kai 138, 154.
Ya ce, "Akwai ire-iren wadannan mutanen masu neman mafaka da suka kai 32, 748 da suka gudo daga wasu kasashe da ke jira a ba su damar samun mafaka a Najeriya.
A Najeriya kanta a cewar hukumar ta NCFRMI, akwai mutum fiye da miliyan uku da rabi da aka raba da muhallansu.
Jami'in hukumar ya ce kashi 92 cikin 100 na wannan adadin mutanen da suka rasa muhallansu a Najeriya sun fito ne daga arewa maso gabas.
Ya ce," Akwai kuma mutanen da suka fito daga arewa maso yamma wanda suma suka rasa muhallansu inda adadinsu ya kai 718, 126, daga tsakiyar Najeriya kuma akwai 604, 640.
Ya ce kuma wadannnan mutanen sun rasa muhallansu sakamakon rikce rikicen da ake fama da su a yankunansu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wasu daga cikin mutanen da rikicin ya raba da muhallan nasu sun sami matsuguni a gida Najeriya, yayin da wasu kuwa suka tsallaka zuwa makwabtan kasashe ne, a cewar jami'in hukumar.
Ya ce," Kamar yadda alkaluma suka nuna mutanen da suka tserewa rikicin Boko Haram suka koma kasar Kamaru sun kai 126, 189, sai kuma wadanda suka koma Chadi daga Najeriya sun kai 21, 429 sai kuma wadanda suka je Nijar sun kai dubu 263, da 86."
Basheer Yusuf, ya ce, hukumar tasu ta yi kokari wajen dawo da dama daga cikin 'yan gudun hijiran da ke kasar Kamaru zuwa gida, kuma ana kokarin dawo da wasu gida daga kasashen Chadi da Nijar.
A cewar Hukumar kula da ƴan gudun Hijira ta Majalisar dinkin duniya UNHCR, zuwa watan Yunin 2024, akwai ƴan gudun hijira miliyan 43.7 a faɗin duniya.
Kuma kashi 65 cikin 100 na zuwa ne daga ƙasashe huɗu: Syria da Venezuela da Ukraine da kuma Afghanistan.
Kashi 71 na ƴan gudun hijira na zama ne a ƙasashe masu tasowa da masu matsakaitan tattalin arziƙi. Iran da Turkiyya da Colombia da Uganda sune ƙasashen da suka fi tsugunar da ƴan gudun hijira.
Kusan kashi 70 na ƴan gudun hijira na samun matsuguni ne a ƙasashen da ke maƙwaftaka da su.











