Man City ta sha da ƙyar a hannun Arsenal a Etihad a Premier

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta tashi 2-2 da Arsenal a wasan mako na biyar a Premier League da suka kara a Etihad ranar Lahadi.
Erling Haaland ne ya fara cin ƙwallo a minti na tara kuma na 100 a Man City a wasa na 105 jimilla, kuma na 10 da ya ci a kakar nan.
Arsenal ta farke ta hannun Riccardo Calafiori, wanda ya zama na 20 da ya ci wa Gunners ƙwallo a wasansa na farko da ya yi mata.
Haka kuma Gunners ta kara na biyu ne ta hannun Gabriel Magalhães daga nan aka bai wa Liandro Trossard jan kati.
Bukayo Saka ne ya bai wa Gabriel ƙwallon da ya ci na biyu, kenan ya bayar da ƙwallaye a kowanne wasa biyar da fara kakar bana ana zurawa a raga.
Mai wannan bajintar a Arsenal shi ne Thierry Henry a kakar 2004/05.
Haka aka yi ta wasan har ta kai ga karin lokacin, inda City ta farke ta hannun John Stone da hakan ya sa suka raba maki a wasan na hamayya.
Kafin su kara ranar Lahadi sun fuskanci juna sau 211 a dukkan fafatawa, inda Gunners ta yi nasara 99 da canjaras 47 aka doke ta wasa 65.
Da wannan sakamakon City ta koma matakin farko a kan teburin Premier League da maki 13, bayan karawa biyar.
Ita kuwa Gunners mai maki 11 tana ta huɗun teburi, bayan da Liverpool ce ta biyu mai maki 12 iri ɗaya da na Aston Villa ta ukun teburi.
Ranar Laraba 25 ga watan Satumba, Arsenal za ta kara da Bolton a English League Cup a Emirates daga nan Gunners ta kara wasa a gida da Leicester City a Premier League ranar Asabar 28 ga watan Satumba.
City za ta karɓi bakuncin Watford a English League Cup ranar Talata 24 ga watan Satumba a Etihad daga nan ta je gidan Newcastle ranar Asabar 28 ga watan Satumba a Premier League.
Sakamakon wasannin da suka buga a 2023/24:
Premier League ranar Lahadi 31 ga watan Maris 2024
- Man City 0 - 0 Arsenal
Premier League ranar Lahadi 8 ga watan Oktoba 2023
- Arsenal 1 - 0 Man City
Community Shield ranar Lahadi 6 ga watan Agusta 2023
- Arsenal 1 - 1 Man City











