Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Japan ce kasar da yara suka fi kashe kansu a 2024
Japan ta zamo kasa ta farko da aka fi samun yaran da suka mutu sakamakon kashe kansu a shekarar ta 2024, wato adadi mafi yawa da aka samu tun shekarar 1980.
Ma'aikatar lafiya da ta walwalar jama'a ta kira lamarin a matsain abin tsoro da tashin hankali.
Sannan kuma ta ce akwai bukatar a gudanar bincike mai zurfi don gano abubuwan da ke haddasa yar ana kashe kansu.
Wata kididdiga daga hukumar 'yan sandan kasar ta nuna cewa kusan mutum 530 ne suka kashe kansu a 2024 inda 527 kuma suka kasance yara yawanci kuma dalibai a makarantun sakandire.
Adadin ya haura wanda aka samu a 2022 inda yara 514 suka kashe kansu.
Wannan adadi dai a cewar hukumar shi ne mafi muni a cikin shekaru 45 da suka wuce.
Yawancin yaran da suka kashe kan nasu na da wata matsala ko damuwa data shafi harkokin makaranta, yayin da wasu kuma suka kashe kansu akan dalilan da suka shafi damuwa ta kafafan sada zumunta.
A bangare guda kuma wata kididiiga daga gwamnatin kasar ta nuna cewa an samu an samu raguwar mutanen da suke kashe kansu a Japan tun daga shekarar 1978, sai a 2024 ne adadin ya yi sama sosai.