Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda dubban yara suka yi ɓatan-dabo a Syria lokacin mulkin Assad
- Marubuci, Reda Elmawy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
- Aiko rahoto daga, Damascus
- Lokacin karatu: Minti 4
Wata ɗaya bayan hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad, wata tambaya da ɗumbin iyalai ke yi ita ce: ina yaran da suka ɓata suka shiga?
Yaƙin basasa - wanda aka shafe sama da shekara 10 ana tafkawa - ya bar mummunan tasiri ba kawai na kashe-kashe ba, har da shafar rayuwar dubban yara da suka ɓace, wasunsu tare da iyaye da 'yan'uwansu.
Ƙiyasi ya nuna cewa an ɓatar da yara 2,000 zuwa 5,000 da ƙarfin tsiya tun bayan fara yaƙin a 2011, kuma har yanzu ba a san inda suka shiga ba. Wasu iyayen na ganin hamɓarar da gwamnatin Assad abu ne da zai taimaka musu sake ganin yaran nasu.
'Na aika wa Assad wasiƙa da ta sa suka kama ni'
Hadi Mohammad Fraa mai shekara 45, ma'aikacin buga litattafai ne a wani lardin binrin Damascus, kuma ya ba da labarin lokaci na ƙarshe da ya ga iyalansa.
Ya ce shi da matarsa mai cikin wata tara sun tsara za ta koma gidan innarta da zama a Damascus babban birnin ƙasar domin ta haihu saboda gidansu na yankin da aka yi wa ƙawanya a lokacin.
Ta fita tare da 'ya'yanta uku a watan Agustan 2013 - Mohammed mai shekara takwas, da Islam (mai bakwai), da Youssef (mai uku) - bisa rakiyar wani mamba a ƙungiyar tsaro mai goyon bayan gwamnati. Hadi na shirin haɗewa da su daga baya.
Daga baya aka kira Hadi daga wani wurin duba ababen hawa cewa iyalansa sun isa lafiya ƙalau. Ofisan da ya kira shi ya faɗa masa cewa kiran kawai tsari ne na tsaro.
Tun daga nan, Hadi bai sake ganin iyalansa ba. Ya ce ya bi duk hanyoyin da ya kamata tsawon shekara 11 amma ba labari.
"Na je ma'aikatar shari'a, da ma'aikatar walwalar jama'a, har da wajen gwamnan Damascus. Na je wajen jami'an tsaro na unguwa, da masu bincike, da masu fatiro, har da na ƙasa baki ɗaya," in ji shi.
Saboda tsabar matsuwa da ya yi, har sai da ya rubuta wa siƙa zuwa ga shugaban ƙasa na lokacin Bashar al-Assad, da matarsa Asma.
Sai dai wannan matakin ya harzuƙa jami'an tsaro, abin da ya sa aka kama Hadi aka tsare shi shekara uku. "Na faɗa musu abin da nake nema kawai shi ne matata da 'ya'yana, amma suka zarge ni da haddasa fitina saboda na yi ƙorafi kan jami'an tsaro kuma na rubuta wa shugaban ƙasa wasiƙa."
Gidajen marayu da ɓoye-ɓoye
Lokacin mulkin Assad, akan kai 'ya'yan fursunoni ajiya a gidajen marayu kuma a ɓoye sunayensu.
A cewar Maha Diab, wata shugabar gidan marayu a Syria, hukumomi na tabbatar da cewa ba a ji wani abu game da yaran ba. "An haramta mana yin magana game da irin waɗannan yaran," in ji ta.
Duk da haramcin, Maha da abokan aikinta ka yi ƙoƙarin gano haƙiƙanin inda yaran suka fito. "Wani zubin masu wayo daga cikinsu kan gyara sunayen da aka ba su kuma su bayar da labarin iyayensu," a cewarta.
Tun bayan faɗuwar gwamnatin, gidajen marayun sun mayar da gomman yara ga iyalansu, amma dai ƙalilan ne kawai na dubban yaran da ake nema.
Shaidu na cewa har a cikin kurkuku akan kira yara da sunayen boge ta yadda ba za a iya gane su ba idan sauran fursunoni na neman su.
Ita ma likitar haƙori Rania al-Abbasi, tana cikin wannan zulumin. An tsare ta tare da 'ya'yanta shida a 2013. Shekara 10 bayan haka, har yanzu 'yan'uwanta ba su san inda suke ba.
Ƙarancin bayanan na jawo fargaba a rayuwar mutane nan gaba. "Me zai faru idan wani ya auri 'yar'uwarsa bisa kuskure?" kamar yadda Ahlaam Yassin, 'surikar Rania, ta tambaya.
'Mun yi fargabar tambaya saboda ana ganin mu 'yanta'adda ne'
Yayin da wasu kamar Hadi suka nemi jin batu game da iyalan nasu, wasu da yawa ba su iya yin hakan ba saboda suna zaune a wuraren da 'yan'adawa ke iko da su.
Daga cikinsu akwai Ysser Suleiman, wani tsohon ɗan gwagwarmaya a Zamalka da ke gabashin Ghouta - garin da ke gabas da Damascus wanda ya sha ƙwanya tun daga 2013 zuwa 2018.
Yasser ya bayyana halin da ɗan ɗan'uwansa Abdulhadi Muwafaq Suleiman ya shiga, wanda ya ɓace a watan Agustan 2013.
Bayan an kashe mahaifinsa da ɗan'uwansa yayin wani hari a Zamalka, Abdulhadi ya yanke shawarar barin garin da aka yi wa zobe domin komawa wajen mahaifiyarsa a Damascus. Sai dai kuma bai ƙarasa ba kuma har yanzu ba a san inda ya maƙale ba.
Kasancewa kusa da 'yan'adawa ya sa da wuya iyalai irin na Yasser su kusanci gwamnati da wata tambaya.
"Suna yi mana kallon 'yanta'adda," in ji shi, yana mai bayyana fargabar da ta sa mutane da yawa suka haƙura da neman bayanai game da iyalansu.
Batun yaran da suka ɓata a Syria yana koma wuyan ma'aikatar walwalar al'umma, wanda ta kwatanta da babban ƙalubale.
Ibrahim Bakour, sabon mataimakin minista na walwalar al'umma ya tabbatar cewa ma'aikatar ta kafa wani kwamati da zai nema kuma ya tantance hujjoji.
A cewarsa: "Aikinmu shi ne tattara hujjoji da kuma gabatar da su ga duniya baki ɗaya," in ji Bakour.