Yadda yawaitar sace allunan kabari ya jefa al'ummar Tanzaniya cikin zullumi

- Marubuci, Alfred Lasteck
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Morogoro
- Lokacin karatu: Minti 5
An bi kabari bayan kabari a wannan makabarta da ke birnin Morogoro a gabashin Tanzania, tare da sacewa da kuma lalata su.
A wasu, akwai wurin da aka saka allunan waɗanda su ma aka cire su, a wasu kuwa ɓarayi sun jingine allunan tare da fatan sayar da su ga ƴan gwangwan, sannan sun kasa cire wasu kuma.
Sama da kaburbura 250 aka lalata a wani ɓangare na makabartar kwaryar birnin Kola.
An fi aikata wannan ta'asa ne da daddare lokacin da babu jami'an tsaro, kuma babu ma'aikatan makabarta.
Lamarin ya tayar wa iyalai hankali da kuma lalata makabartar, abin da ya janyo fushi da ɓacin rai.
Sama da shekara 20, Pudensiana Chumbi ta kasance tana zuwa makabartar aƙalla sau ɗaya cikin wata guda domin ziyarar kabarin ƴarta da kuma mahaifiyarta - sai dai abin mamaki ta samu an lalata kaburburan a cikin shekaru kaɗan da suka wuce.
Kabarin da aka fara lalatawa shi ne na mahaifiyarta wadda ta rasu a shekara ta 2000.
Watanni kaɗan bayan iyalan sun samu damar mayar da allon da aka sace kan kabarin a 2021, sai kuma aka sace na ƴarta. Kabarin yana kusa - ɗiyarta ta rasu a 1997 tana da shekara 15.
Kafin Chumbi ta yanke shawarar gyara kabarin ƴarta, abin mamaki sai aka sace sabon allon da ta saka a kabarin mahaifiyarta.
Bayan shiga ruɗani kan abin da za ta yi na gaba, ta ji cewa saka allon ƙarfe ba shi ne zaɓi ba wajen maye gurbin na ƴarta da aka sace.
"Wannan kabarin ɗiyata ce - ɗiyata ta huɗu," ta faɗa tare da nuna kabarin.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sace allunan daga kan kaburbura ya fara damun al'ummomi a wannan ɓangare na Tanzania, abin da ake tsammani na faruwa saboda ƙaruwar buƙatar ƙarafa.
"An tsinewa mutanen da ke wannan ta'asa saboda kowaye na fushi kan abin da ke faruwa," kamar yadda Ms Chumbi ta faɗa wa BBC.
"Yanzu akwai wasu matasa da ke buƙatar a biya su don su tsare kaburbura da daddare, musamman waɗanda ke da alamomi na tayil."
Ana sayar da tayil ma ga mutane domin amfani da shi wajen ƙawata gidajensu.
Augustine Remmy, ɗan uwan Chumbi, ya ce abin tashin hankali ne a faɗin al'ummar.
"Wannan abin ya yi muni... idan aka mayara da waɗannan wurare da suka cancanci mutunci zuwa wannan yanayi, abin damuwa ne matuka," ya faɗa wa BBC.
Ƙaruwar sace-sacen na nuna irin zaƙuwar da wasu ke da ita na son su yi kuɗi ko ta wani hanya, har ta kai su ga lalata wurare masu tsarki.
Ɓata-garin na samun tsakanin shilling 700 zuwa 870 na kuɗin Tanzaniya kan wani kilo ɗaya.
Ba kuɗi ne masu yawa ba sai dai za su iya sayen filet ɗaya na abinci ko kuma sayen kolban giya.
"Masu sana'ar gwangwan na sayen ƙarafan ba tare da yin tambayoyi ba," a cewar ɗaya daga cikin mutanen da ya faɗa wa BBC cewa ya sace alluna a wata makabarta don sayar da su ga ƴan gwangwan.
Bayan ya amince ya yi magana amma tare da buƙatar ɓoye asalinsa, ya kwatanta yadda ɓarayin ke fara zuwa wajen masu aikin walda waɗanda ke yayyanka ƙarafan kafin kai su wajen ƴan gwangwan.

Masu sana'ar gwangwan na da zaɓin sayen kayan sata cikin sauki ko kuma bin doka.
Izire Ramadhani, wani mai sana'ar a tsakiyar birnin Morogoro, ya tuna yadda a 2023 shi tare da wasu, suka kama wani yana ƙoƙarin sayar da allon sata - inda suka kai kararsa wajen hukumomi.
"A can baya, suna kawo mana alluna. Amma mun kai ƙarar ɗayansu zuwa wajen ƴan sanda, inda daga baya aka yake masa hukuncin ɗaurin shekara uku da rabi a gidan yari," Mista Ramadhani ya faɗa wa BBC.
Ya ce hakan ya janyo raguwar satar allunan a makabartu, duk da cewa an samu ƙaruwar satar a baya-bayan nan.
Mista Ramadhani ya hakikance cewa ba ya sayan kayan sata.
"Idan aka kawo allo a nan, mutum da ya kawo mana zai kasance cikin matsala saboda za mu kai shi wajen ƴan sanda."
Ɓarayi sun fara far wa wasu allunan kaburbura kamar tayil da sauransu, waɗanda za a sayar cikin sauki ga masu saye.
Dr Ndimile Kilatu, jami'in lafiya a Morogoro, ya ce hukumomin birnin sun shirya inganta tsaron makabartu ta hanyar ƙara tsawon katanga da kuma samar da masu gadi, sai dai ya yi gargaɗin cewa hakan na "buƙatar kuɗi da kuma lokaci.
"Ba abu ne da za mu yi yau ko gobe ba."
Ya kuma ce za su wayar da kan masu sana'ar gwangwan kan kayan da bai kamata su saya ba, kamar wanda ake saka wa a kaburbura da kuma kan hanyoyin jiragen ƙasa.

Gwamnatin Tanzaniya ta sha alwashin sa ido a ɓangaren masana'antar masu ƙarafa.
Mataimakin firaiminista Dotto Biteko ya nanata buƙatar sana'o'i masu lasisi da su bi doka da oda.
"Abin da ake buƙata shi ne saka doka da kuma wayar da al'umma kan lamarin. Za mu ci gaba da wayar da kan mutanen mu saboda mu kare kayayyakin mu," in ji Biteko.
Shugabannin addini su ma na yin kira ga al'ummominsu da su yi ƙoƙari wajen hana waɗannan mutane aikata wannan ta'asa.
Fasto Steven Msigara daga majami'ar Jesus Assembles of God a Morogoro, ya yi kiran haɗin kai wajen wayar da matasa muhimmancin mutunta wurare masu tsarki.
"Idan muka haɗa-kai za mu mayar da mutunci, mun san wasu matasa suna aikata munanan ayyuka amma za mu iya dawo da su hanya madaidaiciya," in ji shi.
Ga waɗanda aka lalata kaburburan ƴan uwansu, akwai alamun ɓacin-rai da kuma fushi a wajensu.
Chumbi na son a kashe ƙarin kuɗi a ɓangaren tsaron makabartu da kuma aikin kula da wuraren saboda ganin cewa ƴan uwan mutane ne ke kwance a wurin.
Yanzu da take ƙoƙarin maye gurbin allon mahaifiyarta karo na biyu - da kuma na ƴarta - tana tunanin amfani da allo na laƙa.











