Mece ce matsalar rashin bahaya kuma ta yaya za a magance ta?

Lokacin karatu: Minti 3

Rashin yin bahaya yadda ya kamata, matsala ce da ke damun mutane da dama. Matsalar ta fi shafar waɗanda suka kai shekara 30.

An fi samun matsalar a tsakanin mata, inda take shafarsu ninki biyu fiye da maza.

Wasu alamomin cutar na fara wa ne da ciwon ciki, amai da gudawa da kuma rashin bahaya.

Mece ce ainihin alamomin cutar? Kuma me yake janyo shi, ta yaya kuma za a magance matsalar?

Wata ƙwararriya kan ɓnagaren abinci mai gina jiki, Ayah Langar, ya ce matsalar ba ta babbar barazana ga lafiya duk da cewa tana wahalar da mutane.

Mece ce matsalar rashin bahaya?

Rashin yin bahaya, matsala ce da ke shafar ciki, duk da cewa cutar ba ta barazana sosai - amma tana da raɗaɗi matuka wanda har take iya ɗaukar tsawon watanni uku.

Tana shafar yadda bahaya ke fita, inda take fara wa da ciwon ciki da kuma amai da gudawa.

Ga Ayah Langar, ta ce akwai muhimmanci a gane cewa rashin bahaya ba babbar matsala ba ce: "Kawai ciki ne yake rage aiki yadda ya saba yi. Shi ya sa ake kiranta da matsalar hanji."

Alamomi da abin da ke janyo shi

Manyan alamomin matsalar guda uku su ne: ciwon ciki, rashin fitar bahaya (amai da gudawa ko wahala wajen fitar kashi) da ɗaurewar ciki.

Alamomin dai kan bambanta daga mutum zuwa mutum.

Cutar na fara wa ne ta hanyar fuskantar tsananin ciwon ciki, daga lokaci zuwa lokaci inda yake ƙaruwa a wasu lokuta - yana taɓarɓarewa lokutan da aiki ya yi wa mutum yawa da kuma shiga damuwa.

Ciwon ciki na janyo tsananin juyawar ciki.

Ɗaurewar ciki, rashin bahaya ko kuma amai da gudawa, damuwa da kuma gajiyar ƙwakwalwa na cikin wasu alamomin cutar. Tana kuma iya janyo rama.

Babu abu ɗaya da aka hakikance cewa shi ne yake janyo matsalar.

Kwararriya kan abinci mai gina jiki Ayah Langar ta ce: "Abubuwa da dama ne ke janyo cutar."

Ta yaya za a magance matsalar?

Yanayin warkaswa daga cutar ta sha bamban daga wannan mutum zuwa wancan, kuma tana da alamomi. Ana iya warkewa daga matsalar ce yawanci ta hanyar sauya salon rayuwa.

Yawanci likitoci na ba da shawarar shan magungunan da suka haɗa da antispasmodic, antidiarrheals (idan matsala ce ta amai da gudawa) da kuma laxatives (a wajen matsalar rashin fitar kashi).

Ayah Langar ta ce: "Daga lokacin da na kalli mutum, na duba harshensu, zan iya gano matsalar. Yanayin abincin da mutum zai ci na iya warkas da cutar," in ji ta.

Shawara kan yanayin salon rayuwa

Matsalar ta rashin bahaya dai na shafar cikin mutum da kuma hanji - inda har take kawo tsaiko wajen gudanar da ayyukan yau da kullum.

Magunguna na taimakawa wajen rage alamomin cutar, ganin cewa babu hanya ɗaya tilo ta magance matsalar rashin bahaya.

Matsalar na buƙatar slaon rayuwa mai inganic, wanda hakan zai sa mutum ya ƙaucewa fuskantar matsalar.

Abinci yana taka muhimmiyar rawa, a cewar Ayah Langar: "Ga wanda ke fama da rashin bahaya, yana da kyau a guji cin wasu na'ukan abinci kamar waɗanda aka soya da kuma kayan lemu mai suga. Kayan hatsi na da muhimmanci har ma da shinkafa - musamman ma na'uin basmati," in ji ta.

Ta ƙara da cewa wasu na'uin abinci na janyo wahala wajen fitar bahaya don haka a guje su. Ta ce yana da kyau a riƙa cin abinci mai saukin narkewa a ciki.