An kama mata a Kano bisa zargin satar yara don karɓar fansar miliyoyi

Kano Kidnapping

Asalin hoton, Abdullahi Haruna Kiyawa/Facebook

'Yan sanda sun ce sun kama wasu mata biyu, bisa zargin shirya maƙarƙashiyar sace ƙananan yara a Kano, ciki har da mahaifiyar ɗaya, don neman miliyoyin kuɗi a matsayin fansa.

Matan biyu na cikin gomman mutanen da rundunar 'yan sandan Kano ta ce ta kama a baya-bayan nan.

Tana dai zargin su ne da aikata miyagun laifuka iri daban-daban a Kano, kamar satar mutane don neman kuɗin fansa da aikata fashi da yin garkuwa da mutane da kuma dillancin ƙwaya.

Rundunar 'yan sandan ta ce ta kama matar wadda bazawara ce 'yar shekara 25, da zargin sace Hafsat Kabiru, 'yar da ta haifa da tsohon mijinta, inda ta nemi ya biya kuɗin fansa naira miliyan uku.

Sanarwar da Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Alhamis, ta ce wani Kabiru Shehu Sharaɗa a tsakiyar birnin Kano ya kai rahoto ga 'yan sanda a ranar Litinin 8 ga watan Mayu, cewa tsohuwar matarsa ta sanar da shi 'yarsu ta ɓata.

Kuma, wasu mutane sun kira mahaifiyar yarinyar ta wayar salula, inda suka nemi sai an biya naira miliyan uku kafin a saki 'yar tasu, cewar sanarwar.

Mai magana da yawun 'yan sandan na Kano, ya ce bayan gudanar da bincike ne aka kuɓutar da yarinyar a ƙaramar hukumar Madobi, tare da kama da mahaifiyar.

Ya kuma yi iƙirarin cewa mahaifiyar yarinyar, ta amsa da bakinta cewa ita ce ta ɗauke 'yar tata, kuma ta kai ta maɓoya, sannan ta nemi tsohon mijinta ya biya kuɗin fansa.

Sanarwar Abdullahi Haruna Kiyawa ta ce 'yan sanda suna ci gaba da bincike.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ɗaya matar, mai shekara 45, ana zargin tana cikin gungun mutum huɗu da suka sace wani yaro a birnin Kano, tare da neman kuɗin fansa fiye da naira miliyan biyar.

Sanarwa Abdullahi Haruna Kiyawa ta zargi matar wadda gwaggon yaron ce, da shirya maƙarƙashiyar sace Almustapha Bashir a farkon watan jiya.

Ta kuma ce tun da farko, mutanen da suka saci yaron, ɗan shekara shida ranar 4 ga watan Afrilu sun nemi mahaifinsa da ke unguwar Ƙofar Ruwa a tsakiyar birnin Kano, ya biya naira miliyan ashirin kafin su sake shi.

Daga bisani in ji sanarwar Abdullahi Kiyawa, mahaifin da masu garkuwar suka daidaita a kan naira miliyan biyar da dubu ɗari da hamsin.

"Bayan gudanar da bincike, an kuɓutar da yaron ba tare da wani rauni ba, sannan an kama babbar wadda ake zargi da shiryawa, da kuma tsara yadda za a sace Almustapha" sanarwar ta ce.

Haka kuma 'yan sanda sun kama duk waɗanda ake zargi da hannu a satar yaron, waɗanda matasa ne 'yan tsakanin shekara 24 zuwa 27 daga unguwar Sheka.

Sanarwar Abdullahi Kiyawa ta ce za a kai mutanen gaban kotu da zarar sun kammala bincike.

Matashin da ake zargi ya sace matashiya

Haka zalika, sanarwar 'yan sandan ta ce jami'anta sun kama wani matashi ɗan shekara 19 bisa zargin sace wata matashiya 'yar shekara 14 a unguwar Wailari cikin ƙaramar hukumar Kumbotso.

Ta ce mahaifin yarinyar ne ya kai rahoton sace 'yar tasa ranar Juma'a 5 ga watan Mayun 2023, wadda aka kasa gano inda ta shiga bayan an yi duk wani ƙoƙari.

Sai dai binciken da aka gudanar ya kai ga 'yan sanda suka kama wanda ake zargi a unguwar Kenimi cikin Kumbotso.

Hukumomin tsaron sun dai yi zargin cewa matashin ya yaudari matashiyar, tare da ɓoye ta tsawon kwana biyu.

Kano Kidnapping

Asalin hoton, Abdullahi Haruna Kiyawa/Facebook

Bayanan hoto, Sabon kwamishinan 'yan sanda Mohammed Usaini Gumel ya yi alƙawarin kawo zaman lafiya Kano, mai fama da akasari fashin waya a baya-bayan nan

'Yan sanda kuma sun ce sun kama wasu da ake zargin masu satar mutane ne, waɗanda suka yi wa gidan wani Nasiru Yahaya, mazaunin ƙauyen Yarimawa cikin ƙaramar hukumar Tofa, tsinke.

Sun ce masu garkuwar sun yi yunƙurin harbin ɗan maigidan Gaddafi Nasiru, a lokacin da ya so kuɓucewa, bayan sun kama shi tare da mahaifinsa ranar 16 ga watan Maris.

Sai dai sun kuskure shi, inda suka harbi ɗaya daga cikin abokan tafiyarsu mai suna Umar Abdullahi wanda aka fi sani da suna Ɗanbaba, cewar 'yan sanda.

Kuma nan take ya riga mu gidan gaskiya.

Sanarwar 'yan sanda ta ce Nasiru Yahaya ya kuɓuce daga bisani.

Haka zalika, an harbi mutanen ƙauyen biyu a ƙafafuwa, lokacin da masu garkuwar suke ƙoƙarin awon gaba da ɗan.

Sai dai bayan gudanar da bincike, in ji 'yan sanda, jami'ansu sun kama mutum uku dukkansu 'yan tsakanin shekara 25 zuwa 40 mutanen ƙauyukan Janguza da Langyal da kuma Gargai.